'Yan Bindiga Sun Bude Wa Tawagar Gwamna Wuta a Titin Filin Jirgi? An Ji Abin da Ya Faru
- Gwamnatin jihar Abia ta fito ta yi karin haske kan jita-jitar da ake yadawa cewa 'yan ta'adda sun farmaki ayarin Gwamna Alex Otti
- Mai magana da yawun gwamnan, Ukoha Njoku ya bayyana cewa wannan jita-jita ba gaskiya ba ce domin ba a farmaki mai girma gwamna ba
- Ya ce tawagar jami'ai uku daga ofishin gwamnan ne suka fada tarkon 'yan bindiga amma kuma babu wanda ya rasa ransa a harin
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Abia, Nigeria - An fara yada wwata jita-jita da cewa 'yan bindiga sun farmaki ayarin gwamnan jihar Abia, Alex Otti a hanyarsa ta zuwa filin jirgin zama.
Jita-jitar ta yi ikirarin cewa Gwamna Otti ya fada tarkon 'yan bindiga, inda suka bude wa ayarin motocinsa wuta a titin zuwa filin jirgin Sam Mbakwe, Owerri a jihar Imo.

Source: Facebook
'Yan bindiga sun farmaki gwamnan Abia?
Vanguard ta ruwaito cewa mai magana da yawun gwamnan Abia, Alex Otti, Ukoha Njoku, ya bayyana cewa rahotannin da ake yadawa ba gaskiya ba ne.
A cikin sanarwar da ya fitar, Ukoha ya ce abin da ya faru shi ne wata tawagar da ke yin gaba wato "Advance team" ta ofishin gwamnan Abia, wacce ta kunshi jami'ai uku ne ta hadu da harin yan bindiga.
Ya ce tawagar ta gamu da yan bindigar ne a titin Umuowa zuwa shataletalen Ihitte, amma duk da haka babu wanda ya rasa rayuwarsa.
Abin da ya faru da jami'ai 3 daga Abia
Ya jaddada cewa ba jerin gwanon motocin gwamnan ba ne aka farmaka, kuma babu wanda ya rasa ransa a lamarin.
A rahoton Channels tv, kakakin gwamnan ya ce:
“A safiyar yau, 2 ga Disamba, wata tawaga mai mutane uku daga Ofishin Gwamnan Jihar Abia, Dr. Alex Chioma Otti, waɗanda aka tura aiki filin jirgin sama na Sam Mbakwe, Imo, sun gamu da harin ’yan bindiga da ba a san ko su waye ba."

Kara karanta wannan
Tsohon hafsan tsaro, Janar Irabor ya fadi 'yan siyasa masu rura wutar matsalar tsaro
“Lamarin ya faru ne tsakanin Umuowa da Ihitte Junction, jim kadan kafin su karasa kwanar zuwa filin jirgin sama na Sam Mbakwe da ke Jihar Imo.

Source: Twitter
A karshe, Ukoha ya bukaci daukacin jama'a da su yi wasti da rahoton da ake yadawa cewa 'yan bindiga sun farmaki Gwamna Otti, yana mai cewa ba gaskiya ba ne.
“Muna kira tare da tabbatar wa jama’a cewa harin bai shafi ayarin motocin Gwamna Alex Otti ba ba, kuma babu asarar rai a cikin wannan mummunan lamari.”
Gwamna Otti ya ziyarci Nnamdi Kanu
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Abia, Alex Otti ya kai ziyarar farko ga Nnamdi Kanu a gidan gyaran hali da ke Sakkwato bayan hukuncin da kotu ta yanke masa.
A wannan ziyara, Gwamna Otti ya tabbatar da cewa alkawarin da ya dauka na kokarin ganin an saki Nnamdi Kanu na nan daram kuma ba zai yi kasa a guiwa ba sai ya cika shi.
Wannan ziyara ta sa Alex Otti ya zama gwamna na farko da ya kai ziyara ga Kanu tun bayan da babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
