Sheikh Dahiru Bauchi Ya Taka wa Masu Maulidi Burki a Wasiyyar da Ya Bari

Sheikh Dahiru Bauchi Ya Taka wa Masu Maulidi Burki a Wasiyyar da Ya Bari

  • Marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya rubuta a wasiyyarsa cewa bai yarda a rika gudanar da Maulidi domin tunawa da ranar haihuwarsa ba
  • Malamin ya bayyana cewa bai kai matsayin da za a yi masa Maulidi kamar yadda ake yi wa Manzon Rahama (SAW), Shehu Ahmadu Tijjani ko Ibrahim Inyass
  • Shehin ya ja kunnen mabiyansa da kada su hada sunansa da manya kamar irinsu Tijjani da Inyass, ya ce shi mabiyi ne kamar sauran ’yan Darikar Tijjaniyya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi – A cikin wata wasiyyarsa, marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya nuna rashin amincewarsa da duk wani shiri na ware ranar 2 ga Muharram domin yin Maulidi na musamman don tunawa da ranar haihuwarsa bayan barinsa duniya.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Sanusi II ya fadi yadda Dahiru Bauchi ya ba shi darika, ya ba Tijjaniya shawara

Shehin ya ce wannan lamari bai dace da shi ba, saboda bai kai matsayin gudanar da biki irin na manyan fitattun shugabannin addini da ake yi wa Maulidi ba.

Malamin Darika, Sheikh Dahiru Bauchi
Marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi. Hoto: Ibrahim Dahiru Usman Bauchi
Source: Facebook

Leadership ta wallafa cewa marigayin ya jaddada cewa yana daga cikin mabiya (Muqaddamai) da dama a tsarin darikar Tijjaniyya, kuma wannan matsayi shi kadai ya isa masa a matsayin abin alfahari a rayuwarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce kasancewarsa mataimaki da suruki ga Shehu Ibrahim Inyass babbar daraja ce da bai bukaci a kara masa wani abu da ya wuce hakan ba.

Sheikh Dahiru Bauchi ya hana a masa Maulidi

A cikin kalamansa da aka samu a cikin rubutacciyar wasiyyarsa da kuma wani bidiyo, Sheikh Dahiru Bauchi ya hana a yi masa Maulidi bayan ya rasu:

“Ban yarda cewa a yi taro a ranar 2 ga Muharram ba, ranar da aka haifi Shehu Dahiru domin yin Maulidi. Ban yarda ba. Kada a taba yi mini wannan bayan na rasu.”

Ya yi nuni da cewa wannan nau’in girmamawa ya dace ne kawai ga manyan shugabannin addini da suka zamo fitilu ga al’umma gaba daya kamar Shehu Ahmadu Tijjani da Shehu Ibrahim Inyass.

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani ya gano matsalolin da ke rura wutar rashin tsaro a Arewa

Marigayi Sheikh Dahiru Bauchi
Sheikh Dahiru Usman Bauchi a lokacn da ya ke raye. Hoto: Nazir Dahir Usman
Source: Twitter

Haka kuma, ya yi gargadi kan maganganun da wasu ke furtawa da ke kwatanta watanni da manyan shugabannin addini, inda ake cewa:

“Rabi’ul Awwal ya zo da Manzo (SAW), Safar ya kawo Shehu Tijjani, Rajab ya kawo Shehu Ibrahim, kuma Muharram ya kawo Shehu Dahiru.”

A nan sai ya ce:

“Kada wannan ya sake faruwa. Ban yarda da hakan ba, kuma bana so in sake jin irin wannan maganar.”

Matsayin Sheikh Dahiru Bauchi a Tijjaniyya

Shehin ya ce shi mutum ne daga cikin Muqaddamai, kuma kada a hada sunansa cikin manyan malamai da ake yi wa Maulidi na musamman.

Ya kara da cewa:

“Ni ba komai ba ne face Muqaddam. Idan za a yi wa kowane Muqaddam Maulidi, to kullum sai an yi Maulidi. Ban yarda da a saka sunana cikin wadanda ake yi wa irin wadannan bukukuwa ba.”

A cikin wasiyyarsa, ya jaddada cewa:

Kara karanta wannan

'Ni ne mafi girman Kirista a gwamnati': Akpabio ya fadi yadda ya taso a kaskance

“Ko bayan na mutu, kada wanda ya ce ranar 2 ga Muharram Maulidin Shehu Dahiru ce. Ban amince ba.”

Manyan da suka je jana'izar Dahiru Bauchi

A wani labarin, mun kawo muku cewa manyan Najeriya ciki har da mataimakin shugaban kasa sun halarci jana'izar Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Bayan Sanata Bala Mohammed mai masaukin baki, gwamnoni daga jihohin Gombe, Kano da Niger sun haarci sallar da aka yi wa marigayin a Bauchi.

Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar, Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu sun halarci sallar jana'izar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng