An Kama Wasu 'Yan Kasashen Waje da Suka Shigo Najeriya Ta'addanci

An Kama Wasu 'Yan Kasashen Waje da Suka Shigo Najeriya Ta'addanci

  • An kama wasu ’yan kasar waje da ake zargi da hannu a ta’addanci a yankin Imande-Agbatse, kusa da iyakar Najeriya da Kamaru, bayan matasan yankin sun tare su
  • Wata majiya ta ce jami’an tsaro sun karɓe su daga hannun matasan kuma sun mika su ga sashen bincike na SCID domin tantancewa da zurfafa bincike a kan su
  • Rahotanni sun nuna lamarin na faruwa ne a lokacin da jihar Benue ke fama da matsaloli, tare da ci gaba da bincike domin gano inda matsalar take

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Benue – Jami’an tsaro a jihar Benue sun kama wasu mutum bakwai ’yan ƙasar Kamaru da ake zargin suna da hannu a ta’addanci da ke faruwa a kauyen Imande-Agbatse, wani yanki da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru.

Kara karanta wannan

Barazanar 'yan bindiga: Gwamnatin jihar Kano ta yi magana kan 'yan acaba

Rahoto ya ce lamarin ya auku ne da sanyin safiyar Litinin, inda matasan yankin suka fara tare mutanen kafin su mika su ga jami’an tsaro.

Taswirar jihar Benue a Najeriya
Taswirar jihar Benue da aka kama 'yan Kamaru. Hoto: Legit
Source: Original

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa dauki-ba-dadin ya faru ne a wani lokaci da hukumomi ke kara kokarin dakile laifuffukan da ake zargin suna faruwa a yankunan jihar Benue.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sunayen 'yan kasar waje da aka kama a Najeriya

Rahotanni sun gano cewa wadanda aka kama sune Titakung Cyril Gadinga, Nuvi Clifford Babila, Foyabo Godwin Nuvi T da kuma Doh Collins Dobgima.

Har ila yau sauran wadanda aka yi ram da su sun hada da: Basil Smith, Dama Kenneth Babila, da Dingana Emmanuel.

An ce matasan yankin ne suka kasance masu sa ido a kan motsin mutanen, kafin daga baya su tare mutane bakwai ɗin a hanyarsu ta shiga cikin dazuzzukan yankin.

Gwamna Alia na jihar Benue
Gwamnan jihar Benue yayin hira da manema labarai. Hoto: Benue State Government
Source: Facebook

Matasan sun zargi mutanen da kasancewa cikin gungun ’yan fashi da ke damun jama’a, musamman a yankin kan iyaka da ake yawan samun satar shanu, garkuwa da mutane da kai hare-hare ga kauyuka.

Kara karanta wannan

Fitaccen mawakin Najeriya ya rasa shafukan sada zumunta bayan waka game da Trump

Matakin da jami’an tsaro suka dauka

Daga bisani, an mika wadanda ake zargin zuwa sashen binciken manyan laifuffuka na rundunar ’yan sandan jihar (SCID), inda ake ci gaba da tantance su da gudanar da cikakken bincike domin gano hakikanin al’amarin.

Jami’an tsaro sun tabbatar da karɓar mutanen bakwai ɗin, inda suka ce an kai su sashen SCID domin gudanar da tantancewa da bincike mai zurfi.

Su ma jami’an tsaro sun bayyana cewa za a ci gaba da bibiyar bayanan da matasan suka bayar domin tantance sahihanci tare da gano ko mutanen na da alaka da kungiyoyin ta’addanci da ke aiki a iyakar Najeriya da Kamaru.

Sahara Reporters ta ce wata majiyar tsaro ta ce ana ci gaba da bincike domin gano ko akwai wasu cibiyoyin laifi da mutanen za su iya kasancewa suna da alaka da su.

'Dan adawar kasar Kamaru ya rasu a kurkuku

A wani labarin, mun kawo muku cewa fitaccen dan adawar Kamaru, Anicen Ekane ya rasu bayan tsare shi da gwamnatin Paul Biya ta yi.

Kara karanta wannan

Yadda 'Yan sanda suka saba alkawarin janye jami'ai daga gadin manya amma ba a cikawa

An kama Anicen Ekane ne a lokacin da ya fito ya nuna goyon baya ga dan adawa, Issa Tchiroma Bakary a zaben shugaban kasar da aka yi a Kamaru.

Jam'iyyarsa ta yi Allah wadai da lamarin tana mai zargin an hana shi damar ganin likita a asibitin farar hula a lokacin da jikinsa ya yi tsanani a kurkuku.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng