Shaidar da Malaman Musulunci a Najeriya Suka Yi wa Marigayi Sheikh Dahiru Bauchi
A ranar Alhamis 27 ga watan Nuwambar 2025 aka sanar da rasuwar shehin malami kuma jagoran darikar Tijjaniya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi bayan ya dade yana jinya.
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Bauchi - Al'ummar Najeriya da dama da sauran yan kasashen ketare sun shiga wani irin yanayi bayan rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Marigayin ya rasu ne a ranar Alhamis 27 ga watan Nuwambar 2025 a garin Bauchi bayan fama da jinya na tsawon lokaci.

Source: Facebook
Malaman da suka yi ta'aziyyar Dahiru Bauchi
Jaridar Leadership ta ce an dage jana'izar marigayin a ranar da ya rasu zuwa Juma'a 28 ga watan Nuwambar 2025 domin ba mutane damar halarta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Sharif Ibrahim Saleh ne ya jagoranci sallar marigayin a ranar Juma'a kamar yadda Dahiru Bauchi ya ba da wasiyya.
Manyan malamai da dama sun yi ta'aziyyar rasuwar malamin cikin har da na bangaren Izalah duk da bambancin akida da ke tsakaninsu.
Legit Hausa ta yi duba kan malaman da suka yi ta'aziyyar rasuwar Dahiru Bauchi da abin da suka ce kan rashin da aka yi.
1. Sheikh Abdullahi Bala Lau
Sheikh Abdullahi Bala Lau ya tura sakon ta'aziyyarsa a madadin kungiyar Izalah ganin cewa shi ne shugabanta a Najeriya.
Malam Bala Lau ya bayyana yadda suka yi mu'amala da marigayi Sheikh Dahiru Bauchi kafin rasuwarsa.
Da ya ke magana a kan rayuwar marigayin, Sheikh Bala Lau ya tuno lokacin da su ke haduwa suna barkwani ba tare da cin mutunci ba.
Ya ce:
“Yana da barkwanci, dakuma zolaya. Duk lokacin da aka hadu zai ce ‘kai dan Izala,’ mu ce ‘kai dan Darika.’ Duk irin wadannan kalomomi ba tare da an ci zarafin kowa ba.”

Source: Facebook
2. Sheikh Muhammad Kabir Gombe
Har ila yau, Malam Kabiru Gombe ya yi magana bayan samun labarin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi a makon jiya.
Kabiru Gombe ya tura sakon ta'aziyya na musamman ga iyalan marigayin inda ya yi addu'a ga marigayin domin samun rahama a gobe kiyama.
"Ina miƙa ta'aziyya ga ƴan uwa da iyalan Shehu Ɗahiru Bauchi da al-ummar jihar Bauchi dama ƙasa baki ɗaya, bisa rasuwar Shehu Ɗahiru Usman Bauchi.
"Allah ka gafarta masa kura-kuransa, ka baiwa iyalansa dangana."
- Sheikh Kabiru Gombe

Source: Facebook
3. Sheikh Sani Yahaya Jingir
Shugaban Izalah reshen Jos, Sheikh Sani Yahaya Jingir shi ma ya yi ta'aziyyar rasuwar marigayi Dahiru Bauchi.
A cikin wani bidiyo da Abadurrahman Ibrahim Tela ya wallafa a Facebook, Jingir ya ce yana yiwa iyalan marigayin ta'aziyya kan wannan babban rashi.
Ya ce:
"Ina gabawarwa Malam Ibrahim Dahiru Bauchi ta'aziyya bisa rasuwar mahaifinsa, ka isar da hakurwartarwan nan ta ta'aziyya ga matansa na aure da yan uwanka yayu da kanne daga Muhammadu Sani dan Alhaji Yahaya Jingir."

Source: Facebook
4. Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan
Shugaban hukumar aljazai ta NAHCON, Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan ya bayyana jimaminsa kan rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi.
Ya ce marigayin jagora ne da ya taimaka wajen gyaran tsarin Hajji a Najeriya, kuma ya na taimaka wa alhazai da ilimin addini.

Kara karanta wannan
Allahu Akhbar: An yi jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi, an birne gawarsa a masallaci
Pakistan ya ce shawarwarin shehin sun taimaka wajen kula da alhazai cikin natsuwa, ya mika ta'aziyya ga iyalai da mabiyansa.
5. Farfesa Isa Ali Pantami
Tsohon Ministan Sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami, ya nuna jimami kan rasuwar babban malamin.
Pantami ya mika sakon ta'aziyya ga dattijon da ya kira babansa inda ya yi masa addu'ar Ubangiji ya gafarta masa da yafe masa kura-kuransa.
Ya wallafa a shafin Facebook cewa:
"Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Raaji'un! Muna mika ta'aziyyar rasuwar babanmu, Shaykh Dahiru Usman Bauchi... Muna rokon Allah ya yafe masa kura-kurensa, ya sanya Aljannah ce makoma gare shi. Allah ya ba da ladan hakuri."

Source: Facebook
6. Sheikh Ibrahim Zakzaky
Jagoran kungiyar Islamic Movement of Nigeria da ake kira Shi'a, Sheikh Ibrahim Zakzaky, ya bi sahun masu mika sakon ta'aziyyarsu kan rasuwar malamin darikar Tijjaniyya.
Sheikh Zakzaky ya bayyana rasuwar Dahiru Bauchi a matsayin babban rashi ga al'ummar Musulmi, ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin, almajiransa da dimbin mabiyansa.
Hakazalika, Sheikh Zakzaky ya roki Allah Madaukakin Sarki ya gafarta masa, ya yi masa rahama, kuma ya ba shi matsayi mai girma a gidan Aljannah.

Source: Twitter
7. Dr Ibrahim Jalo Jalingo
Shugaban malaman Izala, Dr Ibrahim Jalo Jalingo, ya yi ta’aziyya ga iyalan Sheikh Dahiru Usman Bauchi bisa rasuwar malamin.
A cikin rubutunsa, Jalo Jalingo ya gabatar da sakon ta’aziyya ga iyalan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda Allah ya yi masa rasuwa.
Dr Jalo ya ce:
"Muna gabatar da ta'aziyyarmu ga iyalan Sheikh Ɗahiru Uthman Bauchi wanda Allah ya yi masa rasuwa a safiyar Alhamis, Allah ya yafe masa kura-kuransa."
Tinubu ya yi ta'aziyyar rasuwar Dahiru Bauchi
An ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayi Sheikh Dahiru Bauchi bayan sanar da rasuwarsa.
Tinubu ya bayyana rasuwar Dahiru Bauchi a matsayin babban rashi ga kasa baki daya ba ga iyalansa ko mabiyansa kadai ba.
Ya kuma tuno yadda marigayin ya ba shi goyon baya da addu’o’i a lokacin shirin babban zaben shekarar 2023.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


