'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Manoman da Ke Dawowa daga Gona a Kaduna

'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Manoman da Ke Dawowa daga Gona a Kaduna

  • 'Yan bindiga dauke da makamai sun yi ta'asa a jihar Kaduna bayan sun ritsa da wasu manoma da ke dawowa daga gona
  • Tsagerun 'yan bindigan sun yi awon gaba da manoman wadanda suka fita neman na abinci a karamar hukumar Sanga
  • 'Dan majalisa mai wakiltar Jema'a/Sanga a majalisar wakilai, Daniel Amos, ya fito ya yi Allah wadai da harin 'yan bindigan

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - 'Yan bindiga dauke da makamai sun yi awon gaba da wa manoma 15 a jihar Kaduna.

'Yan bindigan sun sace mutanen ne yayin da suke dawowa daga gonakinsu a kauyen Ungwan Nungu da ke yankin gundumar Bokana ta karamar hukumar Sanga ta jihar Kaduna.

'Yan bindiga sun sace manoma a Kaduna
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani Hoto: @ubasanius
Source: Facebook

Dan majalisar tarayya mai wakiltar Jema’a/Sanga a majalisar wakilai, Daniel Amos, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a shafinsa na Facebook a ranar Talata, ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan

Matafiya sun shiga tsaka mai wuya yayin da 'yan sanda suka fafata da 'yan bindiga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin, wanda ya faru a ranar Asabar, 29 ga Nuwamba, 2025, ya tayar da hankula a yankin yayin da 'yan uwa ke jiran jin labarin inda aka kai mutanen.

'Dan majalisa ya koka kan harin 'yan bindiga

Daniel Amos ya bayyana harin a matsayin mugunta, rashin mani kuma abin takaici kwarai da gaske.

Hakazalika, dan majalisar ya ce harin ya sake nuna yadda tsaro ke tabarbarewa a kauyukan karkara.

“Mutanenmu sun cancanci rayuwa cikin kwanciyar hankali. Akwai zalunci da rashin adalci fiye da komai wajen kai hari ga mutane masu zaman lafiya da aikin yi.”

- Daniel Amos

'Dan majalisar ya roki jama’ar Ungwan Nungu da makwabtan kauyuka da su kwantar da hankali tare da kauce wa daukar matakan da ka iya ta’azzara lamarin.

Daniel Amos ya kuma bukaci su kasance masu lura tare da ba hukumomin tsaro hadin kai.

Hon. Amos ya bada shawara kan harin 'yan bindiga

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun aiko sako mai tada hankali, garuruwa sama da 10 na cikin hadari

Daniel Amos ya yi kira da a samar da ingantaccen tsarin aiki na hadin gwiwa don ganin an kubutar da wadanda aka sace.

“Ina kira ga hukumomin tsaro da su yi duk abin da ya dace wajen neman mutanen da aka yi garkuwa da su."
"A kara sa ido, a karfafa bincike da bayanan sirri, sannan a cafke wadanda suka aikata wannan ta’adi."

- Daniel Amos

Daniel Amos ya koka kan harin 'yan bindiga a Kaduna
Dan majalisa mai wakiltar Jema'a/Sanga, Daniel Amos Hoto: Hon. Daniel Amos
Source: Facebook

Ya bayyana goyon bayansa ga iyalan da abin ya rutsa da su, yana tabbatar masu da cewa an fara daukar matakai na ganin an kubutar da wadanda aka sace.

“Dukkanmu muna cikin bakin ciki tare da iyalan waɗanda lamarin ya shafa. Za mu ci gaba da matsawa har sai an dawo da su lafiya.”

- Daniel Amos

Daniel Amos ya jaddada cewa tsaron rayuka da jin dadin al’umma shi ne fifikonsa, tare da kiran mutane kada gwiwoyinsu su yi sanyi duk da tsananin kalubalen tsaro da suka addabi yankin.

'Yan bindiga sun sace mutane a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun ci gaba da kai hare-hare kan wasu kauyukan jihar Kano.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi awon gaba da amarya da sauran 'yan biki a Sokoto

Tsagerun 'yan bindigan sun yi awon gaba da akalla mutane 25 a wasu hare-hare da suka kai a karamar hukumar Shanono.

Hakazalika, 'yan bindigan sun raunata wasu mutane daban a hare-harem da suka kai cikin dare lokacin da jama'a ke cikin gidajensu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng