Gwamna Oyebanji Ya Canza Shawara, Ya Dawo da Mafi Yawan Kwamishinonin da Ya Kora

Gwamna Oyebanji Ya Canza Shawara, Ya Dawo da Mafi Yawan Kwamishinonin da Ya Kora

  • Gwamnan Biodun Iyebanji ya tura sunayen mutanen da zai nada a matsayin kwamishinoni ga Majalisar dokokin jihar Ekiti
  • Gwamnatin Ekiti ta ce yawancin wadanda gwamnan ya nada suna cikin tsofaffin kwamishinonin da ya kora daga aiki a kwanakin baya
  • Ta ce an dawo da kwamiahinonin ne domin gudun barakar da iya bullowa tsakanin 'ya'yan APC a zaben gwamnan da za a yi a 2026

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ekiti, Nigeria - Gwamnan Jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, a ranar Litinin ya aika da jerin sunayen wadanda ya nada kwamishinoni zuwa Majalisar Dokokin Jihar domin tantancewa.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba Gwamna Oyebanji shawara kan harkokin yaɗa labarai, Yinka Oyebode, ya fitar a Ado Ekiti, ranar Litinin.

Gwamna Oyebanji.
Gwamna Biodun Oyebanji a fadar gwamnatin jihar Ekiti Hoto: Biodun Oyebanji
Source: Facebook

Gwamna Oyebanji ya rusa majalisar zartarwa

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa sun yi magana da murya 1 kan matsalar rashin tsaro

Premium Times ta rahoto cewa tun a ranar 10 ga Agusta, Gwamna Oyebanji ya rusa majalisar zartarwarsa, ya kori gaba daya kwamishinoni da hadimansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai ya bar wasu kwamishinoni guda biyar da ake ganin ayyukansu na da matuƙar muhimmanci ga tafiyar da gwamnati, waɗanda suka haɗa da Ma’aikatar Ilimi, Lafiya, Noma, Kasuwanci da Zuba Jari, da Ma’aikatar shari'a.

Rusa majalisar zartarwar ta zo ne wakonni kaɗan kafin zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar APC da aka gudanar a jihar Ekiti.

A cewar sanarwar da kakakin gwamnan ya fitar jiya Litinin, sababbin kwamishinonin da aka miƙa yanzu yawancinsu suna cikin wadanda aka kora kwanakin baya.

Me yasa gwamna ya dawo da kwamishinonin?

Oyebanji ya dawo da tsofaffin kwamishinonin ne bayan shawara da shugabannin APC da manyan jiga-jigan jam’iyyar a Ekiti, waɗanda suka matsa lamba ga gwamnan da ya ci gaba da aiki da tawagar da ta wuce.

Sanarwar ta ce:

“Mun amince da dawo da tsofaffin kwamishinonin ne domin jam’iyyar ta shiga zaɓen gwamnan Jihar Ekiti na 20 ga Yuni, 2026 a matsayin gida ɗaya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya sa labule da babban hafsan tsaron Najeriya da ya kora daga aiki

"Ana ganin cewa maye gurbin kwamishinoni da sababbi a cikin watanni bakwai kacal kafin zaɓe, na iya kawo tarnaki.”
Gwamnan Ekiti.
Gwamna Biodun Oyebanji na jihar Ekiti Hoto: Biodun Oyebanji
Source: Twitter

Ta kara da tunatar da cewa shugabannin jam’iyya, shugabannin al’ummomi da sauran muhimman ’yan siyasa ne suka yanke wadanda gwamna ya nada a matsayin kwamishinoni tun a 2023, in ji Leadership.

“Gwamna Oyebanji ya sha fada tun farkon mulkinsa cewa jam’iyya da shugabannin jama'a za su taka muhimmiyar rawa wajen zaɓen waɗanda za su riƙe muƙamai."

Gwamnan Ekiti zai ba malamai rance

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Biodun Oyebanji ya amince da bayar da rancen N596.6m ga malamai da ma’aikatan makarantun sakandare a jihar Ekiti.

Babban sakataren hukumar kula da malamai ta jihar Ekiti, Michael Boluwade ne ya sanar da hakan a sanarwar da ya fitar ranar Talata a Ado Ekiti.

A cewar Michael Boluwade, ba da rancen kudin na daga cikin kokarin Gwamna Oyebanji na inganta walwalar malaman sakandare da firamare na gwamnati.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262