Wakilan Trump a Najeriya Sun Gana da Hadimar Tinubu kan Rashin Tsaro

Wakilan Trump a Najeriya Sun Gana da Hadimar Tinubu kan Rashin Tsaro

  • Wani kwamitin Amurka ya nuna sha’awar fahimtar tushen rikice-rikicen da ke addabar Najeriya tare da tallafa wa ƙoƙarin samar da zaman lafiya
  • 'Yan kwamitin sun kai ziyarar ban girma ne ga mai ba shugaban ƙasa shawara kan lamuran al’umma a Arewa ta Tsakiya, Dr Abiodun Essiet
  • Bayan ganawar da suka yi, bangarorin biyu sun jaddada buƙatar ƙara haɗin gwiwa domin magance matsalolin tsaro da ke damun yankunan Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Tawagar ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ta bayyana ƙudirin ta na fahimtar manyan abubuwan da ke haifar da rikice-rikice a Najeriya da kuma tallafa wa duk wasu shirye-shiryen da za su rage tashin hankali da ƙarfafa zaman lafiya.

Wannan na zuwa ne bayan ziyarar ban girma da suka kai wa Mai ba shugaban ƙasa shawara kan hulɗar al’umma a Arewa ta Tsakiya, Dr Abiodun Essiet.

Kara karanta wannan

'Yan bangan Najeriya sun budewa sojojin kasar Nijar wuta, Hedikwatar tsaro ta yi bayani

Jami'an Amurka tare da hadimar Tinubu
Hadimar Tinubu, Dr Essiet da wasu jami'an Amurka. Hoto: NTA Network News
Source: Facebook

Tashar NTA ta wallafa a X cewa tawagar da Dianna Palequin ta jagoranta, ta haɗa da jami’in kare haƙƙin dan Adam na ofishin jakadancin, Dave Young.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattauna batutuwa da dama da suka shafi shirin shugaban ƙasa na haɓaka zaman lafiya, wanda ofishin Dr Essiet ke jagoranta musamman a yankunan Arewa ta Tsakiya da rikice-rikice suka daɗe suna kawo tsaiko ga ci gaban al’umma.

Tattaunawar Najeriya da Amurka kan tsaro

Bangarorin biyu sun jaddada muhimmancin ƙara haɗin kai tsakanin Najeriya da Amurka domin magance matsalolin tsaro da suka haɗa da rikice-rikicen al’umma, tashin hankali tsakanin makiyaya da manoma da kuma rikicin kabilanci da addini.

Palequin ta bayyana cewa:

“Tawagar Amurka na da muradin fahimtar abubuwan da ke haifar da rikice-rikice tare da tallafa wa ƙoƙarin da ake yi na samar da zaman lafiya da daidaito tsakanin al’umma.”

Ta ce Amurka na goyon bayan duk wani shiri da zai taimaka wajen rage fargaba, gina fahimtar juna da ƙarfafa haɗin kai tsakanin ƙabilun da ke rayuwa a yankin Arewa ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Ribadu ya fadi manyan kasashen da ke taimakon Najeriya a yaki da ta'addanci

Martanin Dr Essiet ga wakilan Trump

Da ta ke mayar da jawabi, Dr Essiet ta nuna godiyarta ga Amurka bisa ci gaba da mara wa Najeriya baya wajen samar da zaman lafiya, tana mai cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu na aiki tukuru wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.

Ta ce:

“Gwamnatin Shugaba Tinubu na yin duk mai yiwuwa domin ganin cewa ’yan Najeriya na rayuwa cikin tsaro da kwanciyar hankali.”

Dr Essiet ta kuma jaddada muhimmancin ci gaba da samun goyon bayan ƙasashen duniya wajen farfado da alakar al’umma da rage sabani, musamman a yankunan da rikice-rikice suka yi tasiri a tsawon shekaru.

Amurka da wasu kasashe na tallafawa Najeriya

A wani labarin, mun kawo muku cewa Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya ce Amurka na cikin kasashen da ke tallafawa Najeriya.

A bayanin da Ribadu ya yi, ya lissafa Faransa da Birtaniya cikin wadanda ke ba Najeriya gudumawa domin ganin ta shawo kan matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

Ekane: Jagoran 'yan adawa da Paul Biya a Kamaru ya rasu a kurkukun soja

Legit Hausa ta gano cewa Ribadu ya bayyana haka ne yayin ganawa da shugabannin addini a jihar Neja bayan sace dalibai da malamai a wata makaranta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng