Gwamnonin Arewa Sun Kafa Asusun Tsaro, Za a Rika Zubin N1bn a Wata

Gwamnonin Arewa Sun Kafa Asusun Tsaro, Za a Rika Zubin N1bn a Wata

  • Gwamnonin Arewa sun cimma matsaya a kan batutuwa daban-daban da suka danganci tsaron yankin tare da nema wa kansu mafita
  • A wani muhimmin taron gwamnoni, sarakunan gargajiya da masu ruwa da tsakin suka gudanar a yankin ,amince da samar da asusun tsaro
  • Gwamnonin sun sake nanata goyon bayansu ga ‘yan sandan jihohi domin karfafa tsaro da kawo karshen kashe-kashe da aka yi a yankin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnonin da ke karkashin kungiyar gwamnonin Arewa (NSGF) sun sanar da kafa wani sabon Asusun tsaron yanki da zummar kawo karshensu.

Za a yi amfani da asusun wajen yaki da ta’addanci, ‘yan bindiga da garkuwa da mutane da suka addabi Arewa, musamman a 'yan kwanakin nan.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa sun yi magana da murya 1 kan matsalar rashin tsaro

Gwamnonin Arewa sun amince da kafa asusun tsaro
Gwamnonin Arewa a yayin taron masu ruwa da tsaki a Kaduna Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta wallafa cewa a karkashin sabon tsarin, jihohin Arewa 19 da kananan hukumominsu za su rika bayar da gudummawar N1bn a kowane wata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnonin Arewa sun yi asusun tsaro

Dazu Punch ta wallafa cewa za a rika cire kudin kai tsaye daga tushe domin tabbatar da cewa kowa ya biya ba tare da tsaiko ba.

Wannan muhimmin mataki ya fito ne daga wata ganawa ta musamman da ta kunshi gwamnoni da Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa (NTRC) wacce aka gudanar a Kaduna a ranar Litinin.

Za a rika amfani da asusun tsaro domin magance tsaro
Gwamnoni da sarakunan Arewa a taronsu na Kaduna Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

A cikin sanarwar da aka fitar bayan taron, wacce shugaban NSGF kuma gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya, ya rattaba wa hannu, an bayyana cewa wannan mataki ya zama dole domin fuskantar matsalar tsaro.

Sanarwar ta ce:

“Domin tunkarar matsalolin tsaro yadda ya kamata, an amince da kafa asusun tsaro a Arewa da kowace jiha da kowane Karamar Hukuma za su rika bayar da N1bn a kowane wata, karkashin wata doka da za a tsara.”

Kara karanta wannan

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi magana kan barazanar 'yan bindiga a Kano

Gwamnonin Arewa sun dakatar da hakar ma'adanai

Gwamnonin sun yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya umarci Ministan Ma’adinai, Dele Alake, da ya gaggauta dakatar da dukkannin ayyukan hakar ma’adinai a Arewa na tsawon watanni shida.

Sun ce hakan zai bai wa gwamnati damar gudanar da cikakken bincike da tantance sahihancin lasisin masu hakar ma’adinai da ake alakantawa da cewa akwai na bogi a cikinsu.

Gwamnonin sun yaba wa Shugaba Tinubu kan kokarin da ya yi wajen kubutar da wasu daliban da aka sace a baya-bayan nan, tare da jinjinawa jarumtar jami’an tsaro da ke fuskantar barazanar ta’addanci a fadin kasar.

Haka kuma, sun sake nanata cikakken goyon bayansu ga kafa ‘yan sanda na jihohi, tare da kira ga ‘yan majalisar dokoki na tarayya da na jihohi a Arewa da su gaggauta gyaran kundin tsarin mulki.

Gwamnan Taraba ya gana da Tinubu

A baya, mun wallafa cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya karɓi bakuncin gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, a fadar gwamnati da ke Aso Rock, Abuja yayin da ake batun sauya shekarsa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kogi ta sha alwashi bayan 'yan bindiga sun tattaro fasto da masu ibada a coci

Ganawar ta kasance ta musamman, kwana biyu bayan Gwamna Kefas ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC, amma an jingine batun bikin sauya shekarsa saboda tsaro.

A wani hoton da aka wallafa daga ofishin Gwamna Kefas, an ga shi tare da Shugaban Kasa Tinubu suna musayar bayanai a fadar shugaban kasa, alamar sabuwar dangantakar siyasa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng