Ribadu Ya Fadi Manyan Kasashen da ke Taimakon Najeriya a Yaki da Ta'addanci
- Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya ce ƙasashen duniya na haɗa kai da Najeriya wajen ceto ɗaliban da aka sace
- Ya ziyarci makarantar St Mary da ke Papairi, inda aka sace malamai da ɗalibai 265, ya kuma miƙa saƙon shugaba Bola Ahmed Tinubu
- Malam Nuhu Ribadu ya ce gwamnatin tarayya ta ɗauki alhakin lamarin tare da alƙawarin ƙara tsaurara matakan tsaro a yankin da ceto daliban
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Neja – Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana samun goyon baya daga ƙasashen Amurka da wasu ƙasashen Turai wajen yaƙi 'yan ta’adda da ceto ɗaliban da aka sace daga makarantar St Mary Catholic School da ke Papairi.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ne ya bayyana haka yayin ziyararsa a yankin da aka sace dalibai a Neja.

Source: Facebook
Punch ta rahoto cewa ya yi magana ne a ranar Litinin bayan sace malamai da ɗalibai 265 a yankin Agwara, Ribadu ya shaida musu cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana tare da su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nuhu Ribadu ya fadi kasashe masu taimakon Najeriya
Ribadu ya ce ana daukar kwararan matakai don ganin an kubutar da ɗaliban cikin koshin lafiya, tare da tabbatar wa iyaye cewa ƙasashen duniya na taimakawa Najeriya wajen murkushe abin da ya kira “mugunta da ta daɗe tana addabar ƙasar.”
Ya bayyana cewa:
“Ina tabbatar muku cewa muna tare da ku. Mutane da dama daga sassan duniya na zuwa domin taimakawa, ciki har da Amurka. Muna godiya musamman ga ƙasashen Turai kamar Faransa, Birtaniya da wasu da dama.
"Duniya gaba ɗaya na haɗuwa don kawo ƙarshen ta'addanci da ya addabi Najeriya.”
Gwamnatin tarayya ta ɗauki alhakin sace dalibai
Ribadu ya ƙara da cewa gwamnatin shugaban ƙasa ta jajirce wajen kare rayuka da dukiyoyi, sannan umarnin ziyarar ya fito kai tsaye daga Tinubu bayan ya dakatar da tafiyar da ya kamata ya yi saboda tashin hankali da lamarin ya janyo.

Source: Facebook
A cewar Ribadu, gwamnati na cikin damuwa bayan jin halin da iyaye ke ciki, inda ya ce:
“Mun ji a jikimmu. Mun ji kamar kamar yadda kuka ji. Wannan lokaci ne mai matuƙar wahala gare mu, amma mun ɗaukar alhakin lamarin domin nauyinmu ne mu kare ku.”
Business Day ta rahoto ya ce gwamnati za ta ƙara tsaro a yankin tare da nuna cewa abin da ya faru zai zama babban darasi da zai taimaka wajen tsara sababbin matakan tsaro a faɗin ƙasar.
Ribadu ya ce:
“Ina da tabbacin cewa mugayen mutane ba za su taɓa ƙarewa ba, amma abin da suka yi yanzu shi ne abin da zai sauya Najeriya zuwa alheri.”
Za a fadi masu taimakon 'yan ta'addan Najeriya
A wani labarin, mun kawo muku cewa mai magana da yawun shugaban kasa, Daniel Bwala ya bayyana cewa an kusa a bayyana sunayen masu taimakon 'yan ta'adda.

Kara karanta wannan
Nuhu Ribadu ya gana da wakilan CAN da iyayen daliban Neja, an ji abin da suka tattauna
Bwala ya bayyana haka ne yayin wata hira da aka yi da shi, inda ya ce shugaba Bola Tinubu ya dukufa wajen ganin ya magance rashin tsaro.
A bayanin da ya yi, Bwala ya ce rashin tsaro lamari ne da ya shafi duniya baki daya, saboda haka kasashe ba za su zuba ido ta'addanci ya yadu ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

