Gwamnatin Nasarawa Ta Ciri Tuta kan Batun 'Yan Sandan Jihohi
- Gwamnatin jihar Nasarawa ta bayyana shirinta na kafa 'yan sandan jiha domin bunkasa harkokin tsaro da kare rayukan al'umma
- Kwamishinan tsaro na jihar ya bayyana cewa gwamnatin Abdullahi Sule ta dauki matakai wajen tabbatar da zaman lafiya a Nasarawa
- CP Usman Baba (mai ritaya) ya bayyana cewa tun bayan hawan Gwamna Abdullahi Sule kan mulki a 2019 ya tallafawa hukumomin tsaro
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Nasarawa - Gwamnatin Abdullahi Sule ta bayyana cikakken shirinta na kafa ’yan sandan jiha a Nasarawa.
Gwamnatin Nasarawa ta ce za ta kafa 'yan sandan jihar ne idan kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba da dama.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa Kwamishinan tsaro da wasu harkoki na musamman na jihar, CP Usman Baba (mai ritaya), ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a Lafiya, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan
Tsohon hafsan tsaro, Janar Irabor ya fadi 'yan siyasa masu rura wutar matsalar tsaro
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Nasarawa ta fifita bangaren tsaro
A cewarsa, tun daga shekarar 2019 da gwamnatin Gwamna Abdullahi Sule ta hau mulki, an ba wa harkar tsaro fifiko ta hanyar tallafa wa hukumomin tsaro da motocin aiki, kayan aiki da sauran kayan aikin gudanarwa.
Kwamishinan ya jaddada cewa Gwamna Sule ya kuduri aniyar tabbatar da cewa jihar ta kasance mai aminci ga masu zuba jari da kuma zaman lafiya ga ’yan ƙasa.
Ya kuma bayyana matakan da gwamnati ta ɗauka domin kare makarantun gwamnati da na kudi, wuraren ibada da sauran wuraren da ake ganin suna da rauni.
Za a samar da 'yan sandan jiha
“Duk lokacin da aka samu matsalar tsaro a wani bangare na jihar, Gwamna kan shiga tattaunawa kai tsaye da shugabannin hukumomin tsaro, kuma ba ya hutawa sai an warware matsalar.”
“Saboda gwamnati na son ta tabbatar da tsaro da zaman lafiya domin jawo hankalin masu zuba jari, mun shirya tsaf don mu kafa rundunar ’yan sandan jiha idan doka ta ba mu dama."
- CP Usman Baba (mai ritaya)

Source: Facebook
Matakan da aka dauka kan tsaron makarantu
Kwamishinan ya ce an tura jami'an tsaro domin kula da makarantun da ake ganin suna cikin haɗari, da manyan wuraren ibada a babban birnin jihar da kuma a kananan hukumomi 13 na jihar.
Game da matsalar garkuwa da mutane, kwamishinan ya tabbatar da cewa gwamnati na aiki tare da hukumomin tsaro, ’yan sa-kai da masu kula da unguwanni don shawo kan lamarin.
Ya gargadi masu garkuwa da mutane cewa jihar za ta zama “wurin da ba su da tabbas,” kuma duk wanda aka kama zai fuskanci cikakken hukunci.
'Yan sanda sun fafata da 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan sanda sun yi artabu da wasu gungun 'yan bindiga a jihar Kogi da ke yankin Arewa ta Tsakiya.
Bangarorin biyu sun yi artabun ne bayan 'yan bindiga sun tare wata hanya da matafiya ke yawan bi da tsakar rana inda suka firgita fasinjoji.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kogi ta sha alwashi bayan 'yan bindiga sun tattaro fasto da masu ibada a coci
Fasinjoji da dama sun tsere zuwa cikin daji domin tsira da rayukansu yayin da artabu tsakanin jami'an 'yan sanda da 'yan bindigan ya dauki dogon lokaci.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
