Zulum: Bana goyon bayan kafa 'yan sandan jihohi - za su ƙara dilmiya Najeriya cikin matsala

Zulum: Bana goyon bayan kafa 'yan sandan jihohi - za su ƙara dilmiya Najeriya cikin matsala

  • Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya ce baya goyon bayan kafa 'yan sandan jihohi a Nigeria
  • Farfesa Zulum ya ce kafa 'yan sandan jihar zai bawa wasu gwamnonin damar cin zarafin mutane da basu kauna
  • Zulum ya yi wannan jawabin ne a makarantar koyon dabaru da tsare-tsare, NIPSS, da ke Kuru a jihar Plateau

Plateau - Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno ya ce bayan goyon bayan kafa 'yan sandan jihohi a Nigeria, The Cable ta ruwaito.

Ana ta kiraye-kirayen cewa a bawa jihohi daman su kirkiri 'yan sandansu a wasu jihohin domin magance matsalar tsaro.

A watan Yuli, kudirin neman kafa yan sandan jihar ya wuce karatu na biyu a majalisar wakilai na tarayya.

Read also

Jagororin PDP sun fara yaki domin David Mark ko Makarfi ya karbi shugabancin Jam’iyya

Zulum: Bana goyon bayan kafa 'yan sandan jiha - za su ƙara dilmiya Najeriya cikin matsala
Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno. Hoto: The Cable
Source: Facebook

Onofiok Luke, dan majalisar tarayya daga jihar Akwa Ibom ne ya gabatar da kudirin a gaban majalisa a cewar rahoton na The Cable.

Amma Zulum ya ce bawa jihohi ikon kafa 'yan sandan su zai kara tabarbarewar matsalar tsaro a kasar.

Gwamnan Bornon ya bayyana hakan ne yayin da ya ke gabatar da mukallarsa a cibiyar koyan dabaru da tsare-tsare ta NIPSS da ke Kuru, Jihar Plateau.

Da ya ke bayani kan matsayarsa, gwamnan ya ce Nigeria ba ta kai matsayin da za a kafa 'yan sandan jihohi ba.

Ya ce wasu gwamnonin na iya amfani da su domin cin zarafin wasu mutanen ko kabilu.

A cewar Zulum:

"Maganar gaskiya, Ni Babagana Zulum, ba zan goyi bayan hakan ba, ba wai don bana son shi ba, amma saboda abubuwan da za su biyo baya.

Read also

Tsohon Sarki Sanusi ya soki tsarin biyan tallafin fetur, ya fallasa badakalar da ke cikin tsarin

"Nigeria ba ta kai matsayin kafa yan sandan jihohi ba, wasu gwamnonin za su iya amfani da su domin kawar da wasu kabilun daga jiharsu.
"Don haka ya kamata mu yi takatsantsan. Idan aka dauki rabin ikon da ke hannun sojoji aka bawa yan sanda da yan sandan jihohi, Nigeria za ta shiga matsala."

Abin da yasa Abacha har abada zai cigaba da zama jarumi a jihar mu, Gwamnan PDP na Kudu

A wani labarin daban, Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa, a ranar Litinin, 27 ga watan Satumba ya bayyana marigayi Janar Sani Abacha, tsohon shugaban kasa na mulkin soja a matsayin jarumi na jihar Bayelsa.

Diri ya ce tsohon shugaban kasar ya samu wannan darajar ne saboda nan take da alkalami, marigayin, shekaru 25 da suka gabata (1996) ya kirkiri jihar ta Bayelsa kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Gwamnan na jihar Bayelsa ya mika godiyarsa ga marigayin shugaban wanda ya amince a kirkiri jihar da ke da kananan hukumomi takwas a lokacin wanda ya ce ya gaza adadin da kundin tsarin mulki ya tanada, Daily Trust ta ruwaito.

Read also

Duk da tsoma bakin Diflomasiyya: 'Yan Ghana sun cigaba da muzguna wa 'yan kasuwan Najeriya

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel