Tsohon Hafsan Tsaro, Janar Irabor Ya Fadi Yan Siyasa Masu Rura Wutar Matsalar Tsaro

Tsohon Hafsan Tsaro, Janar Irabor Ya Fadi Yan Siyasa Masu Rura Wutar Matsalar Tsaro

  • Tsohon Hafsan Tsaro na kasa, Janar Lucky Irabor (mai ritaya) ya ce matsalar tsaron kasar nan ta wuce a jingina ta kan abu daya
  • Irabor ya bayyana cewa wasu 'yan siyasa na amfani da sha'anin tsaro wajen nuna gazawar gwamnati da cimma burinsa na neman mulki
  • Ya ce duk wani nau'in ta'addanci da ake aikatawa a Najeriya yana da manufa amma ba zai yiwuwa a dunkule shi wuri daya ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Tsohon babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Lucky Irabor (mai ritaya) ya fallasa 'yan siyasar da yake zargi da rura wutar matsalar tsaro a kasar nan.

Janar Irbor ya ce wasu daga cikin ’yan siyasa na amfani da rashin tsaro a matsayin makamin neman mulki, har ma suna rura wutar rikice-rikice domin kawai su cimma muradunsu.

Kara karanta wannan

Rufa rufa ta kare: Za a fadi sunayen masu daukar nauyin ta'addanci a Najeriya

Janar Lucky Irabor.
Tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor (mai ritaya) Hoto: Nigerian Army
Source: Twitter

Ya kuma yi gargadin cewa matsalolin tsaro a Najeriya suna da sarkakiya kuma sun zarce a jingina su wuri guda kamar masu zargin kisan kiristoci kadai, in ji Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Irabor ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da Channels Television a ranar Litinin, inda ya yi cikakken bayani kan nau’o’in laifuffuka da ake aikatwa wanda da ke tada zaune tsaye a Najeriya.

Furucinsa na zuwa ne bayan kwanaki kadan da hadimin shugaban kasa, Daniel Bwala, ya ce gwamnatin tarayya na shirin bayyana sunayen wadanda ke daukar nauyin ta’addanci.

Abin da Irabor ya ce kan matsalar tsaro

Yayin da yake bayanin rikita-rikitar matsalar tsaro, Irabor ya yi gargadin cewa bai kamata ana dunkule matsalolin wuri guda a jingia ga tushe daya ba.

Ya ce Najeriya na fama da nau’o’in barazanar tsaro daban-daban, na tsattsauran ra'ayi, na ta'addanci, na siyasa, da na tattalin arziki, kuma duka suna faruwa lokaci guda.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace mai martaba sarki a jihar Kwara

Ya ce:

“Ba za ka canza wa mutane ra’ayoyinsu haka kurum ba, amma gaskiyar magana ita ce matsalolin tsaron nan sun sha bamban sosai.”
"Muna da ’yan ta’adda masu tsaurin ra’ayi, yan ta'adda da ke kai hari kan Kiristoci, yan ta'adda da ke kai farmaki domin korar al’ummomi su mamaye yankuna, da masu aikata laifukan tattalin arziki.

Matsalar tsaron Najeriya siyasa ce?

Da yake tsokaci kan masu ganin matsalar tsaro siyasa, Irabor ya ce duk da cewa akwai siyasa a lamarin tsaron Najeriya hakan ba ya nufin gaba daya haka abun yake ba.

“Wadanda ke cewa matsalar tsaro siyasa ce, su ma suna yi wa al’amura takaitaccen kallon da bai dace ba,” in ji shi.

Sai dai ya amince cewa wasu ’yan siyasa na amfani da rashin tsaro domin samun rinjaye ko nuna gazawar gwamnati mai ci.

"Amma wannan ba ya na nufin babu ’yan siyasa da ke amfani da matsalar tsaro domin su nuna wa jama'a cewa idan suka samu dama za su yi abin da ya fi haka.

Kara karanta wannan

Fitaccen jarumin fim a Najeriya ya bayyana ana tsaka da jita jitar ya mutu

“Wasu kuma na iya daukar nauyin tayar da tarzoma domin su zargi gwamnati da gazawa,” in ji shi.
Sojoji.
Hoton babban hafsan tsaro, Janar Oluyede tare da sojoji Hoto: @NigerianArmy
Source: Facebook

Tinubu ya gana da tsohon hafsan tsaro

A wani labarin, kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu ya karbi bakuncin tsohon babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Chirstopher Musa (mai ritaya) a fadar shugaban kasa.

Wannan ganawa na zuwa ne a daidai lokacin da al'amuran tsaro ke kara tabarbarewa a Najeriya musamman a jihohin Kwara, Neja da Kebbi.

Wannan shi ne karo na farko da tsohon hafsun ya gana da Shugaba Tinubu a fili tun bayan saukarsa daga mukamin babban hafsan tsaron Najeriya a ranar 24 ga Oktoba, 2025.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262