Gwamnonin Arewa Sun Yi Magana da Murya 1 kan Matsalar Rashin Tsaro

Gwamnonin Arewa Sun Yi Magana da Murya 1 kan Matsalar Rashin Tsaro

  • Gwamnonin da ke mulki a Arewa sun gudanar da muhimmin taro tare da sarakuna kan matsalolin da suka addabi yankin
  • Bayan kammala taron, sun cimma matsaya kan hanyar da za a magance matsalar rashin tsaron da ake fama da ita
  • Hakazalika, sun yabawa Mai girma Bola Tinubu kan kokarin da ya yi wajen ganin an kubutar da daliban da 'yan bindiga suka sace

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Kungiyar gwamnonin jihohin Arewa (NSGF) ta bada shawara ga Shugaba Bola Tinubu kan matsalar rashin tsaro.

Kungiyar gwamnonin na Arewa ta bukaci Tinubu da ya umarci ministan ma’adanai ya dakatar da duk wani aikin hakar ma’adanai na tsawon watanni shida, domin gudanar da cikakken bincike da tantancewa.

Gwamnonin Arewa sun yi taro a Kaduna
Wasu gwamnonin Arewa yayin taron da suka yi a Kaduna Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ce hakan na kunshe ne a cikin takardar bayan taro da shugaban kungiyar kuma gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya karanta.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya sa labule da babban hafsan tsaron Najeriya da ya kora daga aiki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muhammadu Inuwa Yahaya, ya karanta takardar ne bayan kammala taron hadin guiwar Gwamnonin Arewa da majalisar sarakunan Gargajiya ta Arewa, wadda aka gudanar a Kaduna a ranar Litinin, 1 ga watan Disamban 2025.

Me gwamnoni Arewa suka ce kan rashin tsaro?

A cewar kungiyar, hakar ma’adanai ba bisa ka'ida ba ta zama babban abin da ke haifar da tabarbarewar tsaro a Arewacin Najeriya, jaridar The Punch ta kawo labarin.

“Kungiyar ta lura cewa hakar ma’adanai ba bisa ka'ida ba ya zama babban abin da ke janyo matsalar tsaro a Arewacin Najeriya."
"Don haka ta yanke shawarar kira ga shugaban kasa da ya umarci ministan ma’adanai ya dakatar da duk wani aikin hakar ma’adanai na tsawon watanni shida domin a gudanar da cikakken bincike."
"Duk takardun lasisin hakar ma’adanai kuma a sake tantance su cikin watanni shida tare da yin shawara da gwamnoni domin dakile miyagun ayyukan hakar ma’adinai ba bisa ka'ida ba”

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya gayawa gwamnonin Arewa gaskiya yayin taro a Kaduna

- Inuwa Yahaya

An kafa asusun tsaro a Arewa

Inuwa Yahaya ya bayyana cewa an kafa asusun tsaro domin yaki da matsalolin rashin tsaron da ake fama da su a yankin.

Kungiyar ta ce an amince cewa kowace jiha da kananan hukumomi za su riƙa bada Naira biliyan 1 duk wata, wanda za a rika cirewa bisa tsarin da za a tsara tare.

Gwamnonin Arewa sun yabawa sojoji kan rashin tsaro
Gwamna Inuwa Yahaya da sauran gwamnonin Arewa wajen taro a Kaduna Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Gwamnonin Arewa sun yabawa gwamnati

Kungiyar ta kuma yaba wa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa kokarinta wajen sakin wasu daga cikin yaran da aka sace.

Hakazalika, ta kuma jinjinawa jajircewar sojoji da sauran jami’an tsaro da ke yaki da ƙungiyoyin ta’addanci a fadin ƙasa.

A karshe, kungiyar ta tabbatar da cikakken goyon bayanta ga shirin kafa ’yan sandan jihohi, tare da kira ga ’yan majalisar tarayya da na jihohi daga Arewa da su dauki matakan ganin hakan ya tabbata.

Shawarar Sarkin Musulmi gwamnonin Arewa

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa sun hadu don samo mafita kan rashin tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III, ya bada shawara ga gwamnonin Arewa.

Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya bukaci gwamnonin yankin da su rika sauraron mutanen da ke sukar gwamnatocinsu.

Ya nuna cewa ba ya jin dadi idan ya ji ana cewa shugabanni sun yi watsi da mutanen da suka taimaka musu wajen samun mulki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng