Mai Martaba Sarki da Aka Sace a Kwara Ya Gudo daga Hannun Masu Garkuwa da Mutane

Mai Martaba Sarki da Aka Sace a Kwara Ya Gudo daga Hannun Masu Garkuwa da Mutane

  • Sarkin Bayagan, Alhaji Kamilu Salami, da wasu mutane shida sun kubuta daga hannun ‘yan bindiga a dajin Kwara
  • ‘Yan bindigar dai sun nemi N150m a matsayin kudin fansar basaraken kafin 'yan sa kai su kai masu hari har sarkin ya tsere
  • Wata majiya daga masarautar Bayagan ta ce Sarki Kamilu da kansa ya kira su a waya ya sanar da su cewa ya kubuta

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kwara - Sarkin Bayagan da ke ƙaramar hukumar Ifelodun a jihar Kwara, Alhaji Kamilu Salami (Ojibara), ya tsere daga hannun ‘yan bindiga.

Mai martaba sarkin ya gudo daga hannun miyagun ne tare da wasu mutum shida da aka yi garkuwa da su a yankin Bayagan.

Sarkin kasar Bayagan da aka sace ya kubuta daga hannun 'yan bindiga a Kwara
Taswirar jihar Kwara, inda aka sace sarkin kasar Bayagan. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sarki ya gudo daga hannun 'yan bindiga

Majiyoyi daga masarautar Bayagan sun tabbatar da cewa sun samu kira daga Sarki Kamilu jim kadan bayan kubutarsa, in ji rahoton Channels TV.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi musayar wuta da 'yan ta'adda a Kano, an nemi wasu mutane an rasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce sarkin ya fadawa mutanensa cewa sun samu damar kubuta bayan artabun da jami’an 'yan sa kai suka yi da ‘yan bindigar a cikin dajin Eku Idaji, kusa da Igbaja.

Wata majiya ta ce:

“Jami’an 'yan sa kai sun mamaye dazuzzukan yankin, kuma suka kai hari cikin dajin da 'yan ta'addar da suka sake sarkin suke zama.
"An yi musayar wuta mai tsanani, wanda ya baiwa sarki da sauran mutane damar tserewa. Sun riga sun yi magana da mutanen gari domin tabbatarwa cewa sun tsira.”

‘Yan bindiga sun nemi N150m kudin fansa

Kafin ya samu damar tserewa, Legit Hausa ta rahoto cewa ‘yan bindigar sun yi wa al’umma Bayagan magana da safiyar Lahadi inda suka nemi N150m a matsayin kudin fansarsa.

Sarkin da kansa ya yi magana da mutanensa a lokacin da ‘yan bindigar suka kira wayar, inda aka ji yana roƙon jama'arsa su gaggauta taimaka masa saboda halin da yake ciki.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai hari a Kano, sun yi kisa da sace mutane

Wasu majiyoyi sun ce:

“Sarkin ya bayyana cewa sun dauke shi a kan babur suka yi tafiyar fiye da awanni biyar cikin daji kafin su isa wurin da suke waya da al’umma.
"Ya ce akwai wasu mutane daga wani gari da ke makwabtaka da su da aka yi garkuwa da su a lokacin, kuma an hada su a waje daya”
Har yanzu ba a ji ta bakin rundunar 'yan sanda kan kubutar basaraken ba.
Shugaban rundunar 'yan sanda na kasa, IGP Kayode Egbetokun. Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Sace sarki ya jefa al'umma cikin fargaba

Hankalin jama’a ya fara tashi ne bayan wasu manoma da ke wurin suka gaza ganinsa, sai dai suka ga babur dinsa a ajiye a cikin gonar.

Wannan ya sa aka shiga neman sa a tsakanin mazauna kauyen wata majiyar yankin ya bayyana cewa wani manomi daga wani kauye na makwabtaka ya shaida da idanunsa yadda aka yi garkuwa da Sarkin.

Yadda aka yi garkuwa da Sarki Kamilu

Tun da fari, mun ruwaito cewa, a ranar Asabar ne wata tawaga ta ‘yan bindiga dauke da AK-47 ta farmaki gonar Sarki Kamilu Salami inda suka yi awon gaba da shi.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace mai martaba sarki a jihar Kwara

Kasar Bayagan, inda sarkin ke mulki dai babban gari ne a karamar hukumar Ifelodun, jihar Kwara, kuma lamarin ya tayar da hankula sosai cikin al’umma.

Shaidu sun bayyana cewa sun ga lokacin da ’yan ta'adda dauke da bindigogi suna tilasta wa sarkin hawa babur a gonarsa da misalin karfe 9:0 na safiya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com