Matafiya Sun Shiga Tsaka Mai Wuya yayin da 'Yan Sanda Sun Fafata da 'Yan Bindiga

Matafiya Sun Shiga Tsaka Mai Wuya yayin da 'Yan Sanda Sun Fafata da 'Yan Bindiga

  • 'Yan bindiga dauke da makamai sun tare hanyar da matafiya ke yawan bi a jihar Kogi da ke yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya
  • Harin da 'yan bindigan suka kai ya jawo matafiya da dama sun makale yayin da aka yi musayar wuta tsakaninsu da jami'an 'yan sanda
  • Artabun da aka yi tsakanin jami'an tsaron da 'yan bindiga ya jawo matafiya da dama sun gudu domin tsira da rayukansu

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kogi - Artabu tsakanin 'yan bindiga da jami'an 'yan sanda ya jawo daruruwan fasinjoji sun makale a kan hanyan Oshokoshoko–Obajana da ke jihar Kogi.

Fasinjojin sun makale ne sakamakon artabu mai zafi da ya barke tsakanin jami’an tsaro da ’yan bindiga a kan hanyar.

'Yan bindiga sun kai hari a jihar Sokoto
Jami'an 'yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa mutane da dama sun ajiye motocinsu sun gudu cikin daji yayin da musayar wuta ta dauki tsawon sa’o’i.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun aiko sako mai tada hankali, garuruwa sama da 10 na cikin hadari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun tare hanya a jihar Kogi

An samu tashin hankali ne bayan ’yan bindiga sun kaddamar da wani sabon hari a kan wannan hanya da ta zama sananniya wajen kai farmaki cikin 'yan kwanakin nan.

A wani faifan bidiyo da aka wallafa, an ga fasinjoji da dama tsaye a gefen hanya, wasu daga cikinsu cikin firgici.

Wani matafiyi da ya dauki bidiyon cikin tsananin tsoro ya bayyana halin da suke ciki, inda ya roki a kawo musu daukin gaggawa.

'Yan bindiga: Fasinjoji sun nemi dauki

Cikin rawar murya, wanda ya dauki bidiyon ya ci gaba da kiran neman agaji yana cewa:

"Najeriya, don Allah ku zo ku cece mu. Mun shiga matsala. Kowa ya tsaya, babu wanda ke motsi. Masu garkuwa sun mamaye hanya. Don Allah, muna nan yanzu haka.”

Hanyar Oshokoshoko–Obajana ta sha fama da hare-haren kwantan bauna a 'yan kwanakin nan, lamarin da ke kara tsorata mazauna yankin da ma masu wucewa kan hanyar a kullum.

Kara karanta wannan

Ba dadi: 'Yan bindiga sun sake ta'addanci a wasu kauyukan Kano

'Yan bindiga na kai hare-hare a Kogi

Jihar Kogi na daga cikin jihohin da suke fuskantar matsananciyar matsalar tsaro a Najeriya.

'Yan bindiga sun fafata da 'yan sanda a Kogi
Taswirar jihar Kogi, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

A ranar Lahadi, ’yan bindiga sun kutsa cikin wani coci a Ejiba, karamar hukumar Yagba ta Yamma, inda suka sace Fasto, matarsa da wasu mambobin cocin lokacin da ake tsaka da gudanar da ibada.

A makon da ya gabata, Gwamna Ahmed Ododo ya bayyana cewa wasu manyan kwamandojin ’yan bindiga sun koma buya a jihar, sai dai ya yi alkawarin cewa jami’an tsaro za su kai musu farmaki a maboyarsu.

'Yan bindiga sun sace mutane a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun sake kai hare-haren ta'addanci a wasu kauyukan jihar Kano.

'Yan bindigan sun tasa keyar akalla mutane 25 wadanda ba su ji ba, ba su gani ba a hare-haren da suka kai a wasu kauyukan karamar hukumar Shanono.

Hakazalika, 'yan bindigan sun raunata wasu mutane daban a hare-haren da suka kai cikin dare lokacin da mutane suke kwance cikin gidajensu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng