Ana Wata ga Wata: Gwamna Ya Sanya Dokar Hana Fita Ta Awa 24 bayan Barkewar Rikici
- Gwamna Ademola Adeleke ya ayyana dokar hana fita ta awanni 24 a wani yanki na jihar Osun bayan barkewar rikici
- An tura sojoji, ‘yan sanda, DSS da NSCDC don gudanar da sintiri na awa 24 domin dawo da zama lafiya a garin Igbajo
- Gwamnan jihar Osun ya gargadi mazauna garin kan tayar da fitina, yana mai cewa gwamnati ba za ta sassauta ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Osun - Gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya ayyana dokar hana fita ta sa’o’i 24 a garin Igbajo, da ke ƙaramar hukumar Boluwaduro.
Gwamna Ademola Adeleke ya ayyana dokar ne bayan barkewar tashin hankali da aka samu a yankin a ƙarshen makon da ya gabata.

Source: Twitter
Osun: Gwamna ya sanya dokar hana fita
Ayyana dokar hana fitar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da da aka fitar daga ofishin kwamishinan Labarai na Osun, Oluomo Kolapo Alimi, aka wallafa a shafin gwamnati na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce gwamna ya ɗauki matakin ne bisa bayanan leken asiri daga ofishin mai ba gwamna shawara kan tsaro, Barr. Samuel Ojo.
A cewar gwamnatin jihar, tarzomar ta barke ne bayan rasuwar Prince Adegboyega Famodun a ranar Asabar da ta gabata bayan gajeriyar rashin lafiya.
Rahoton ya bayyana cewa mutuwar ta jawo rikicin cikin gida a garin, lamarin da ya rikide zuwa tarzoma tsakanin wasu kabilu mazauna yankin.
Sojoji, 'yan sanda, DSS za su sa ido
Domin dakile yaduwar rikicin, gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita nan take, wacce za ta ci gaba da aiki “har sai an tabbatar da cikakken zaman lafiya.”
Gwamnatin Adeleke ta tura sojoji, ‘yan sanda, DSS da jami’an NSCDC domin gudanar da sintiri na awa 24 a Igbajo.
A sanarwar da kwamishinan watsa labaran ya fitar, Oluomo Kolapo Alimi ya ce:
“Yayin da dokar hana fita za ta fara aiki daga yau Litinin, 1 ga Disamba, 2025, jami'an tsaro za su karɓi ragamar tsaron Igbajo tare da sanya ido na awa 24 har sai an dawo da zaman lafiya.”

Kara karanta wannan
Martanin Barau da gwamnatin Kano ta nemi a cafke shi saboda zargin ingiza rashin tsaro

Source: Twitter
Gwamna Adeleke ya yi tir da rikicin
Jaridar Premium Times ta rahoto Gwamnan Adeleke ya ce ba zai lamunci kowace iriyar rigima ko karya doka da za ta lalata zaman lafiyar jihar ba.
Adeleke ya bayyana takaicinsa kan barkewar tashin hankali a yankin, yana mai cewa:
“Gwamnati ba za ta nade hannu tana kallo ana karya doka a ko’ina cikin jihar ba, ballantana a Igbajo, gari mai tarihin zaman lafiya.”
Ya kuma yi gargadi ga mazauna garin da baki, cewa duk wanda aka kama da hannu a wani abu da zai ƙara tayar da hankali, zai fuskanci fushin doka.
Adeleke ya karyata batun komawa APC
A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnatin Osun ta sake fitowa fili ta yi magana kan jita-jitar cewa Gwamna Ademola Adeleke zai bar PDP.
Gwamnatin ta karyata rahoton da ke cewa Adeleke na tattaunawa da tsohon gwamna Rauf Aregbesola domin shiga jam’iyyar ADC.
Mai magana da yawun gwamnan, Malam Olawale Rasheed, ya bayyana labarin da ƙarya da yan adawa suka ƙirƙira domin biyan bukatar kansu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

