Sarkin Musulmi Ya Gayawa Gwamnonin Arewa Gaskiya yayin Taro a Kaduna
- Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III, ya halarci taron gwamnonin Arewa da sarakunan gargajiya
- Sarkin Musulmin ya bukaci gwamnonin da su kasance masu sauraron mutanen da ke sukar gwamnatocinsu
- Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya kuma bada tabbacin cewa sarakunan gargajiya za su ci gaba da aiki tare da gwamnonin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar sarakunan gargajiya ta Arewa, Mai Alfarma Sultan Sa’ad Abubakar III, ya bada shawara ga gwamnonin Arewa.
Sarkin Musulmi ya yi kira ga gwamnonin jihohin Arewa 19 da su rika sauraron masu sukar gwamnati sosai tare da amfani da sukar da ake yi cikin fa’ida domin inganta mulki a yankin.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce Sarkin Musulmi ya bayyana yayin da yake jawabi a ranar Litinin a taron hadin-gwiwar gwamnonin Arewa da sarakunan gargajiya da aka gudanar a Kaduna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarkin Musulmi ya kare shugabanni
Sarkin Musulmin ya jaddada cewa babu wani shugaba da ya nemi amanar jama’a sannan bayan hawa mulki ya juya musu baya da gangan.
Ya nuna damuwa kan yadda ake zargin gwamnonin da rashin yin komai, duk da kalubalen da suke fuskanta.
"Ba na jin dadi idan na ji ana cewa gwamna ba ya son yin komai ko shugaban kasa ba ya son yin komai. Babu wani gwamna ko shugaban kasa da zai nemi kuri’un jama’a sannan da zarar ya hau kujerar mulki ya juya wa al’umma baya.”
- Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III
Wace shawara ya ba gwamnoni?
Ya shawarci gwamnonin da su saurari masu suka, su saurari abin da ake cewa, su saurari masu nazari, sannan su yi gyara idan akwai bukatar hakan.
Sarkin Musulmin ya bayyana cewa suka mai ma’ana na iya zama abu mai wajen yanke sahihan matakai.
Ya gargade su cewa yin watsi da suka na iya jinkirta kokarin magance matsalolin yankin, musamman na tsaro, talauci da halin matsin tattalin arziki.
Yayin da yake nuna kwarin guiwa a kan gwamnonin, Sarkin Musulmin ya tunatar da su muhimmancin hadin kai da kara kaimi wajen aiki tare.
Sarkin Musulmi ya yabi gwamnoni
Ya yaba musu kan irin kokarin da suke yi, yana mai cewa jinkirin wasu tarurruka da suka wuce ya samo asali ne daga ayyukan gwamnati masu yawa da suke fuskanta.

Source: Facebook
A cewarsa, aiki tukuru da hadin kai ne kadai za su iya tabbatar da tsaron Arewa da kwanciyar hankali a Najeriya baki ɗaya.
Sarkin Musulmin ya kuma bukaci karin hadin kai da musayar shawarwari tsakanin gwamnonin Arewa da sarakunan gargajiya na kowane yanki, tare da shirya tsare-tsaren tarurruka na yau da kullum domin daidaita matsayar Arewa kan al’amuran da suka shafe ta.
Ya sake tabbatar da cewa sarakunan gargajiya za su ci gaba da mara wa gwamnonin baya wajen ganin an inganta rayuwar al’umma.
Sarkin Musulmi ya gana da Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III, ya sa labule da Mai girma Bola Ahmed Tinubu.
Mai girma Bola Tinubu da Sarkin Musulmi sun gana tare da tattaunawa kan muhimman barutuwa a ofishin mai girma shugaban kasa da ke Aso Rock Villa.
Ganawar na daga cikin tattaunawa da neman shawarwari da Shugaba Tinubu ke yi da shugabannin addini da na gargajiya a Najeriya kan barazanar da Amurka ta yi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


