Ba Dadi: 'Yan Bindiga Sun Sake Ta'addanci a Wasu Kauyukan Kano
- An sake shiga jimami a jihar Kano bayan 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-haren ta'addanci a wasu kauyuka a karshen makon jiya
- Tsagerun 'yan bindigan sun farmaki kauyukan guda biyu na karamar hukumar Shanono a ranar Lahadi da daddare lokacin da mutane ke cikin gidajensu
- A yayin hare-haren, 'yan bindigan sun yi awon gaba da mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba tare da jikkata wasu bayin Allah
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-hare a wasu kauyukan jihar Kano.
Tsagerun 'yan bindigan sun kai hare-haren ne a kauyukan Unguwar Tsamiya da ke Faruruwa da Dabawa, duk a cikin karamar hukumar Shanono.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa akalla mutane 25 'yan bindigan suka yi awon gaba da su, yayin da suka raunata wasu mutum biyu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Harin ya faru ne da daren ranar Lahadi, kasa da awa 24 bayan makamancin harin da aka kai kauyen Yankamaye a karamar hukumar Tsanyawa, wani yanki da ke bakin iyaka da jihar Katsina, inda aka sace mutane uku.
Yadda 'yan bindiga suka kai hari a Kano
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun shiga kauyukan ne da daddare, inda suka rika harbi a iska tare da tayar da hankalin jama’a.
Daga bisani 'yan bindigan sun yi garkuwa da mutane da dama tare da jikkata wasu mutum biyu a yayin harin.
Mai magana da yawun shugaban karamar hukumar Shanono, Ammar Wakili, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami’ai na ci gaba da tantance cikakkun bayanai, Tashar TVC News ta kawo labarin.
“Harin ya faru, amma muna kokarin tabbatar da dukkan bayanai kafin mu fitar da sanarwa a hukumance."
- Ammar Wakili
Waɗannan hare-haren da ke ta maimaituwa sun ƙara tayar da hankalin mazauna yankunan kan iyaka tsakanin Kano da Katsina, wanda suka dade suna fama da hare-haren ’yan bindiga.
Mutane da dama sun nuna damuwarsu kan yadda tashe-tashen hankulan ke kara shigowa Kano, duk da tabbacin gwamnati na cewa an inganta matakan tsaro.
Me 'yan sanda suka ce kan lamarin?
Legit Hausa ta tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa domin samun karin bayani kan lamarin.
Sai dai, kakakin 'yan sandan bai dauki kiran wayar da aka yi masa ba, sannan bai dawo da amsar sakon da aka tura masa ba.

Source: Original
Karanta wasu labaran kan 'yan bindiga
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi magana kan barazanar 'yan bindiga a Kano
- Ana tsaka da zarge zarge, yan bindiga sun kutsa coci, sun sace Fasto da matarsa
- Ana wata ga wata: 'Yan bindiga sun tare hanya, sun sace matafiya a jihar Kogi
'Yan bindiga sun sace amarya
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kawo cikas a wurin wani bikin aure a jihar Sokoto.
Miyagun 'yan bindigan sun yi awon gaba da amarya da kawayenta a farmakin da suka kai cikin wani kauye da ke karamar hukumar Wurno.
Hakazalika, 'yan bindigan sun yi awon gaba da mutanen da suka je gidan biki yayin da ake shirye-shiryen gudanar da daurin aure.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


