Matakai 5 da Trump Ya Dauka a kan Najeriya daga Dawowa Mulki Karo na 2 a 2025
A wannan rahoton, mun tattaro muku jerin wasu matakan da shugaban Amurka ya dauka game da Najeriya tun bayan rantsar da shi a watan Janairun 2025.
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A watan Janairun shekarar 2025 aka rantsar da shugaban Amurka karo ba biyu bayan nasara a zaben shugaban kasa.
Tun bayan dawowa mulki karo na biyu, Donald Trump ya dauki matakan siyasa da na tattalin arziki da suka shafi kasashe da dama.

Source: Getty Images
A wannan rahoton, mun kawo muku wasu daga cikin mataka da gwamnatin Amurka ta dauka game da Najeriya a 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Trump ya dakatar da tallafin USAID ga Najeriya
A watan Janairun 2025, gwamnatin shugaba Donald Trump ta dakatar da tallafin USAID zuwa Najeriya na kwana 90.
Sai dai VOA ta rahoto cewa jami’an Najeriya sun kaddamar da wani kwamiti domin samar da tsarin sauyi da dorewar shirye-shiryen lafiya da USAID ke daukar nauyi.
Kwamiti mai kunshe da jami’ai daga ma’aikatu daban-daban zai nemi sabbin hanyoyin samun tallafi domin ci gaba da muhimman shirye-shiryen kiwon lafiya.
Rahotanni sun ce Ministan lafiyar Najeriya ya ce kwamitin da ya kunshi jami’ai daga ma’aikatar kudi, lafiya da muhalli.

Source: Facebook
Kwamitin na da nufin tabbatar da cewa marasa lafiya da ke karbar magani kan cututtuka irin su kanjamau, tarin fuka, da zazzabin cizon sauro ba su fuskantar cikas.
2. Trump ya sa wa Najeriya harajin 15%
Najeriya ta fuskanci harajin shigo da kaya na kashi 15, ƙarƙashin umarnin shugaban kasar Amurka, Donald Trump a Agustan 2025.
Jaridar Punch ta tattaro cewa sanarwar ta fito ne a matsayin wani ɓangare na sauya tsarin harajin musayar kayayyaki da fadar White House ta bayyana.
A watan Afrilu, Trump ya kakaba haraji kan wasu abokan hulɗar kasuwanci, inda ya ɗaura harajin kashi 14 kan kayayyakin da Najeriya ke fitarwa zuwa Amurka.

Source: Twitter
Daga bisani an ɗage harajin na tsawon kwanaki 90 domin bai wa ƙasashen dama su tattauna yarjejeniyoyin kasuwanci na musamman, amma ya dawo da shi daga baya.
3. Amurka ta yarda da sayarwa Najeriya makami
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta amince da yiwuwar sayar wa Najeriya makamai da darajarsu ta kai Dala miliyan 346 a watan Agustan 2025.
Gwamnatin kasar Amurka ta amince da sayar da makaman ne domin taimaka wa Najeriya ƙara inganta tsaro.

Source: Facebook
Rahoton AP ya nuna cewa makaman da Najeriya ta nema sun haɗa da harsasai, bama-bamai da rokoki.
4. Trump ya jefa Najeriya a CPC
A ranar 31 ga Oktoba 2025, gwamnatin Amurka ta amince a hukumance tare da ɗaukar mataki kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya.
Rahoton Legit Hausa ya nuna cewa bisa zargin ne Trump ya sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ake bukatar ba su kulawa ta musamman (CPC).

Source: Facebook
Bayan daukar matakin, Donald Trump ya kuma yi kira ga ‘yan majalisar dokoki su gudanar da bincike kan zargin.
5. Amurka ta yarda ta yi aiki da Najeriya
Bayan ziyarar da wasu manyan jami'an Najeriya suka kai Amurka kan zargin kisan Kiristoci, kasashen biyu sun yarda su yi aiki tare domin yaki da ta'addanci.
Kasashen biyu sun kafa kwamiti da zai yi aiki tare domin fahimtar matsalolin da ake fama da su da yadda za a magance su.
A bangaren Najeriya, shugaba Bola Tinubu ya nada Mai ba shi shawara a kan harkokin tsaro ya jagoranci tawagar kasar.

Source: Twitter
Cikin tawagar Najeriya akwai ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar, hafsun tsaro, Janar Olufemi Oluyede, ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar da sauransu.
Labarin jiragen Amurka ya firgita 'yan ta'adda
A wani labarin, kun ji cewa an yada rade-radin cewa wasu jiragen yakin Amurka sun yi sintiri ta sama a Najeriya.

Kara karanta wannan
Majalisa ta tsoma baki da Jonathan ya makale a kasar da sojoji suka yi juyin mulki
An ce lamarin ya tayar da hankalin wasu 'yan ta'addan ISWAP da suka fake a wasu yankunan Borno kusa da Tafkin Chadi.
Masana harkokin tsaro sun bayyana cewa fitar da labarin bai dace ba saboda yana iya zama barazana da rayuwar sojoji.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


