Rufa Rufa Ta Kare: Za a Fadi Sunayen Masu Daukar Nauyin Ta'addanci a Najeriya

Rufa Rufa Ta Kare: Za a Fadi Sunayen Masu Daukar Nauyin Ta'addanci a Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta ce ba da jimawa ba za ta fitar da sunayen mutanen da ke daukar nauyin ta’addanci a Najeriya
  • Mai ba shugaban kasa shawara, Daniel Bwala ya ce ana ɗaukar matakai masu tsauri kan batun tsaro a fadin kasar
  • Ya bayyana cewa haɗin guiwar ƙasashen duniya na da muhimmanci, domin matsalar ta’addanci babba ce sosai

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja, Najeriya – Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa nan ba da jimawa ba za ta fito fili ta bayyana sunayen mutanen da ake zargin suna daukar nauyin ta’addanci a sassan Najeriya.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnati ke kara ƙaimi wajen murkushe kungiyoyin da ke barazana ga zaman lafiyar ƙasa.

Daniel Bwala tare da Bola Tinubu
Daniel Bwala yayin gana wa da Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Hadimin shugaban kasa, Daniel Bwala ne ya bayyana haka a wata hira da aka yi da shi a shirin talabijin na TVC a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Barazanar 'yan bindiga: Gwamnatin jihar Kano ta yi magana kan 'yan acaba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a fadi sunan masu taimakon ta’addanci

Daniel Bwala ya ce gwamnatin tarayya tana tafe da matakan da ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen bayyana mutanen da ke taimakawa, goyon baya ko daukar nauyin kungiyoyin ta’addanci a Najeriya.

Ya ce:

“Gwamnati na ɗaukar matakai kai tsaye. A kwanaki masu zuwa, ’yan Najeriya za su san su waye ’yan ta’addan da kuma wadanda ke ba su kuɗi.”

Bwala ya nuna cewa gwamnatocin baya sun sha fama da kalubalen gano hanyoyin kudi da ke shiga hannun kungiyoyin ta’addanci.

Sai dai a wannan karon, Bwala ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta dauki sabon salo da aka gina kan bayanan sirri.

Ya ce irin wadannan bayanan za su ba gwamnati damar gano sahihan cibiyoyi da mutanen da suka zamo ginshiƙai wajen tallafawa ’yan ta’adda a ƙasar.

Ta’addanci matsala ce ta duniya — Bwala

Punch ta rahoto Daniel Bwala ya bayyana cewa matsalar ta’addanci ta wuce matsalar ƙasa ɗaya a duniya, domin a cewarsa:

Kara karanta wannan

Fitaccen mawakin Najeriya ya rasa shafukan sada zumunta bayan waka game da Trump

“Tun bayan abubuwan da suka faru na 9/11, ta’addanci ya zama babban batu na tsaron duniya. Kowace ƙasa da ’yan ta’adda ke aiki a cikinta tana zama damuwa ga sauran ƙasashe.”

Ya kara da cewa saboda haka dole ne ƙasashen duniya su ci gaba da hada kai da Najeriya wajen kawo karshen kungiyoyin 'yan ta'adda.

Hafsun tsaron Najeriya
Hafsun tsaron Najeriya, Janar Oluyede a wani taro. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Twitter

A cewarsa, manyan ƙasashe sun fahimci cewa barazanar 'yan ta'adda, idan ta bar wani wuri ba tare da kulawa ba, tana iya yaduwa cikin sauri zuwa sauran wurare.

Bwala ya bayyana cewa matsalar ta’addanci da a da ake ganin tana tashe a Gabas ta Tsakiya yanzu ta ƙaura zuwa yammacin Afirka, musamman yankin Sahel.

Magana kan barazanar tsaro a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Kano ta magantu kan yadda ake yada cewa jihar na fama da rashin tsaro sosai.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi gargadi game da masu yada labaru marasa tushe game da tsaron jihar.

A wata sanarwa da gwamnatin Kano ta fitar, Abba Kabir ya ce jami'an tsaro na sanya ido a kan dukkan sassan jihar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng