Gwamnan da ke Fafutukar Nemawa Nnamdi Kanu Afuwa Ya Kai Masa Ziyara a Kurkuku

Gwamnan da ke Fafutukar Nemawa Nnamdi Kanu Afuwa Ya Kai Masa Ziyara a Kurkuku

  • Gwamnan Abia Alex Otti ya kai ziyarar farko ga Nnamdi Kanu a gidan gyaran hali da ke Sakkwato bayan hukuncin daurin rai da rai
  • Babbar kotun tarayya a Najeriya ta yanke wa Nnamdi Kanu, shugaban haramtacciyar kungiyar 'yan ta'addan IPOB hukuncin a watan Nuwamba
  • Kotu ta tabbatar da kama shi da laifuffukan ta'addanci da suka hada da kitsa hari ga ofishin UN a Abuja da kashe jami'an tsaro

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto – Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, ya ziyarci jagoran ƙungiyar 'yan awaren IPOB, Nnamdi Kanu, a gidan gyaran hali da ke jihar Sakkwato.

Hukumar gyaran hali ta Najeriya ta aika Kanu zuwa gidan gyaran halin ne bayan da kotu ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun koma amfani da tauroron 'dan adam wajen sadarwa a tsakaninsu

Gwamnan Abia ya ziyarci Nnamdi Kanu
Nnamdi Kanu, Gwamna Alex Otti da tawagarsa da suka sauka a Sakkwato Hoto: @MaziNnamdiKanu/Ferdinand Ekeoma
Source: Twitter

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa gwamnan ya ziyarci gidan gyaran halin a ranar Lahadi tare da wasu manyan jami’an gwamnati daga Jihar Sakkwato.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna ya ziyarci Nnamdi Kanu a Sakkwato

Daily Post ta wallafa cewa Mai shari’a James Omotosho ya umarci cewa a tsare Kanu ba tare da samun damar amfani da wayar salula ko na'urar sadarwa ba.

Jim kadan bayan kotu ta yanke hukunci, aka kwashe jagoran na IPOB daga Abuja zuwa jihar Sakkwato domin ya fara zaman da aka yanke masa.

Gwamnan Oti ya ce zai yi kokari a fito a Nnamdi Kanu
Shugaban 'yan awaren IPOB a yayin zaman kotu Hoto: Favour Michael Kanu
Source: Twitter

Kanu ya fito ne daga Afara-Ukwu a karamar hukumar Umuahia ta Arewa a jihar Abia a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

A wannan ziyara, Gwamna Otti ya tabbatar da cewa alkawarin da ya dauka na kokarin ganin an sake Nnamdi Kanu na nan daram.

Martanin lauya Nnamdi Kanu

Aloy Ejimakor, tsohon lauyan Nnamdi Kanu, ya jinjinawa Otti bisa wannan ziyara, inda ya bayyana fatan zai zamo alheri ga shugaban IPOB.

Kara karanta wannan

An fara cika umarnin Tinubu game da janye 'yan sanda daga tsaron manyan mutane

Ya ce:

“Ubangiji ya sanya wannan ziyarar taka ta zama mataki na farko da zai kawo ƙarshen wannan jarabawarda wuri."

Wannan ziyara ta sa Alex Otti ya zama gwamna na farko da ya kai ziyara ga Kanu tun bayan da aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai.

Kwanaki guda bayan hukuncin, Otti ya sanar da cewa zai fara aiwatar da manufofin neman a saki Kanu, matakin da ake ganin zai iya shafar siyasa da tsaro a Kudu maso Gabas cikin makonni masu zuwa.

'Yan majalisa sun mika bukata kan Nnamdi Kanu

A baya, mun wallafa cewa Kungiyar ’yan majalisar wakilai daga Kudu maso Gabas ta mika bukata ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan batun Nnamdi Kanu, jagoran kungiyar IPOB.

Sun yi kira da Shugaban kasa ya yi amfani da kundin tsarin mulki ya ba shi domin yi wa Kanu afuwa, suna mai jaddada cewa ko da yake suna mutunta hukuncin kotu, akwai bukatar sassauci.

Kara karanta wannan

Kanu da mutanen da suka wakilci kansu a kotu ba tare da lauya ba da yadda ta kaya

An yanke wa Kanu hukuncin daurin rai da rai ne makon da ya gabata bayan kotu ta same shi da laifi a kan tuhume-tuhumen ta’addanci da suka hada da kashe jami'an tsaro da sauran hare-hare.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng