EFCC Ta Ƙwace Fasfon Malami, Ta Hana Ministan Buhari Fita Ƙasar Waje
- EFCC ta karɓe fasfo ɗin Abubakar Malami, tsohon ministan shari'a yayin da ake bincike kan badakalar $490m na kudin Sani Abacha
- An hana Malami fita zuwa kasashen waje na wata guda yayin da aka buƙaci ya rika kai kansa hedikwatar EFCC a kowace rana
- Tsohon ministan shari'ar dai ya fito ya musanta zargin cewa yana da hannu a wata badakala, inda ya ce gaskiya za ta yi halinta
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta karɓe fasfo ɗin tafiye-tafiye na tsohon babban lauyan Najeriya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, SAN.
An karɓe fasfo ɗin ne a wani mataki da EFCC ta ɗauka yayin ci gaba da bincike kan badakalar $490m na Abacha da aka dawo wa Najeriya ƙarƙashin yarjejeniyar MLAT.

Kara karanta wannan
Abubakar Malami ya yi bayani game da 'kudin Abacha ' da EFCC ke zargin ya yi wasosonsu

Source: Twitter
EFCC ta ƙwace fasfon Abubakar Malami
Wata sahihiyar majiya daga hukumar EFCC ce ta tabbatar da cewa an kwace fasfo din Malami a ranar Lahadi, kamar yadda jaridar Vanguard ya nuna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyar ta bayyana cewa an hana Malami barin Najeriya na tsawon wata guda, har sai hukuma ko kotu ta bayar da wani sabon umarni.
A cewar majiyar, ɗaya daga cikin sharuddan da aka ba tsohon ministan lokacin da aka gayyace shi ranar Asabar shi ne ya ringa zuwa hedikwatar EFCC kullum domin ci gaba da amsa tambayoyi.
Majiyar ta ce:
“Ba mu ce ya saci kuɗi ba, amma muna son ya bayyana inda $490m suka makale bayan an dawo da su.”
Majiyar ta ƙara da cewa akwai yawan takardu da ake bukatar ya duba da kuma shaidun da dole ne a tantance, shi ya sa aka karɓe fasfo ɗinsa domin tabbatar da cikakken bincike ba tare da tangarda ba.
$490m na MLAT: Me binciken EFCC ya kunsa?
Rahotanni sun nuna cewa hukumar na son Malami ya fayyace wasu bayanai game da kuɗin da aka dawo daga asusun da tsohon shugaban Najeriya, Marigayi Sani Abacha, ya tara — musamman $490m da aka dawo da su daga kasashen ketare ƙarƙashin MLAT.
Majiyar ta EFCC ta ce wannan shi ne babban abin da ya sa ake yi wa tsohon ministan shari'ar tambayoyi a yanzu.
Rahoton ya nuna hukumar EFFC ta ce ba za ta tsaya yin wani ce-ce-ku-ce ba a halin yanzu, tana mai cewa:
“Za mu fitar da cikakken sakamako bayan an kammala bincike yadda ya kamata.”

Source: Twitter
Martanin Malami: “Zarge-zarge ne kawai”
A shafinsa na X, Abubakar Malami ya bayyana cewa zarge-zargen da ake yadawa a kansa ba gaskiya ba ne, ya ce ya gode wa Allah da tattaunawarsa da EFCC ta kasance cikin natsuwa.
Ya rubuta cewa:
"Dangane da alkawarina na ci gaba da sanar da ’yan Najeriya game da gayyatar da EFCC ta yi mini, ina mika godiya ga Allah bisa ba ni ikon fitowa cikin aminci.
"Tattaunawar ta kasance mai kyau, kuma na samu fitowa, haka zalika an sake sanya wani sabon lokaci domin ci gaba da tattaunawa yayin da gaskiyar da ta shafi ƙagaggun zarge-zargen da aka yi a kai na ke ci gaba da bayyana."
Abubakar Malami bai yi karin haske kan karɓe masa fasfo ba, amma ya jaddada cewa gaskiya za ta bayyana a yayin ci gaba da binciken.
Malami zai shiga takarar gwamnan Kebbi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami, ya tabbatar da cewa zai shiga tseren gwamnan Jihar Kebbi a 2027.
Ya bayyana cewa kiraye kirayen da jama'a suka dade suna yi ne ya amsa yanzu, duk da cewa lokacin fara gangamin siyasa bai yi ba a halin yanzu.
Malami ya tabbatar da cewa ya yanke shawarar fitowa neman kujerar gwamnan jihar Zamfara a 2027, kuma babu abin da zai sanya ya ja da baya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

