'Yan Ta'adda Sun Koma Amfani da Tauroron 'Dan Adam wajen Sadarwa a tsakaninsu

'Yan Ta'adda Sun Koma Amfani da Tauroron 'Dan Adam wajen Sadarwa a tsakaninsu

  • Hukumar bincike da ci gaban sararin samaniya ta kasa (NASRDA) ta ce 'yan ta'adda suna amfani da kafar sadarwa ta zamani
  • Shugaban hukumar, Dr. Mathew Adepoju ya ce rufe layukan sadarwa na zamani ba zai kawo cikas wajen sadarwa mutanen ba
  • Ya bayyana cewa a yanzu, 'yan ta'adda suna amfani da taurarun 'dan adam wajen raba bayanai a tsakaninsu maimakon wayoyin hannu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Daraktan Hukumar Bincike da Cigaban Sararin Samaniya ta Kasa (NASRDA), Dr. Mathew Adepoju, ya ce 'yan ta'adda sun koma amfani da kafar zamani.

Ya yi gargaɗin cewa kungiyoyin ta’addanci a Najeriya sun sauya dabarar sadarwa, suna barin layukan salula zuwa tsarin sadarwa na tauraron dan adam.

Kara karanta wannan

Tinubu ya lissafa abubuwa 2 da ya dauka da muhimmanci domin jin dadin 'yan Najeriya

'Yan ta'adda sun karo karfin sadarwa
Shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Yayin wata hira da tashar Channels Television a ranar Juma’a, Adepoju ya bayyana damuwa game da wasu matakai da gwamnoni ke dauka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An soki matakin gwamnoni a kan tsaro

Daily Nigerian ta wallafa cewa Mathew Adepoju ya ce matakin da jihohi kan dauka na rufe layukan wayoyi yayin farmakin tsaro yanzu ba shi da tasiri.

A cewarsa, maharan sun fi dogaro da hanyoyi na zamani wajen raba sakonni a tsakaninsu a maimakon amfani da layukan waya da ake da su a kasar.

Mathew Adepoju ya ce:

“Ina matuƙar bakin ciki idan gwamnoni suka rufe layin wayoyin hannu saboda mafi yawan waɗannan miyagu ba su yin sadarwa ta hanyar layukanmu. Suna amfani ne da dandamalin tauraron dan adam. ‘Yan ta’adda suna amfani da tauraro wajen magana."
Yan ta'adda na amfani da tauraron 'dan adam wajen sadarwa
Wasu daga cikin 'yan ta'adda a wani zaman sulhu a Katsina Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

Ya kara da cewa akwai rashin fahimta a cikin al’umma game da abin da tauraron dan adam na Najeriya ke iya yi.

Kara karanta wannan

Gwamnan da ke fafutukar nemawa Nnamdi Kanu afuwa ya kai masa ziyara a kurkuku

Mathew Adepoju, ya ce an samar da tauraron 'dan adam a Najeriya ne domin ɗaukar hotuna, ba domin yin bidiyo kai tsaye ba.

Najeriya na shirin yakar 'yan ta'adda

Adepoju ya bayyana cewa tauraron da Najeriya ke da su yanzu—NigeriaSat-1, NigeriaSat-X da NigeriaSat-2—na bukatar akalla kwanaki uku kafin su dawo wurin da aka dauki wai bidiyo.

Wannan matsalar, in ji shi, na rage saurin martanin kasar kan barazanar tsaro da ke faruwa cikin gaggawa kamar yadda aka bukata.

Ya shaida cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da ƙaddamar da sababbin taurari hudu domin rage wannan lokacin zuwa tsakanin awanni huɗu zuwa shida, gwargwadon yadda za a tsara.

Hukumar tana kuma shirin ƙara wasu taurari huɗu ko biyar domin kara samun bayanai a kusan lokaci guda.

Mathew Adepoju, ya kuma bayyana cewa NASRDA ta kulla yarjejeniya da wasu hulda daga Amurka da ke da taurarin dan adam 300.

'Yan ta'adda sun fara gudu

A wani labarin, kun ji cewa an samu cikas a kokarin yaki da ta’addanci a yankin Tafkin Chadi bayan an fallasa bayanan sirri a kafafen sada zumunta game da ayyukan leken asirin Amurka.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun fara gudu bayan jin labarin zuwan jiragen sojan Amurka Najeriya

Rahotanni daga sahihan majiyoyi sun tabbatar da cewa wannan fitar bayanan sirri ta tilasta wa wasu mayakan ISWAP sauya matsugunansu domin kauce wa afkawar soji.

Duk da haka, har yanzu hukumomin Najeriya ko Amurka ba su fitar da wata sanarwa ba domin tabbatar da sahihancin labarin ko musanta shi yayin d ake ci gaba da yaki da ta'addanci a kasar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng