Dubun Masu Garkuwa da Mutane Ta Cika: An Cafke Hatsabiban 'Yan Bindiga a Zamfara
- Jami'an Scorpion Squad sun kama rikakkun masu garkuwa da mutane biyu a Zamfara, tare da kwato motoci da bindigogi
- Rahotanni sun tabbatar da cewa wadanda ake zargin sun sha shiga hannun hukuma, saboda yawan sace mutane da suke yi
- An ji yadda wadannan 'yan ta'adda suka taba sace wani mutumi a Abuja, suka kwashe rabin miliyan daga asusun bankinsa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Zamfara - Rundunar 'yan sanda ta musamman, watau Scorpion Squad ta yi nasarar cafke wasu hatsabiban masu garkuwa da mutane a jihar Zamfara.
Jami'an 'yan sandan sun cafke miyagun ne a ranar 25 ga Nuwamba 2025, bayan samun sahihan bayanan sirri da aka gudanar ta hanyar amfani da fasahar bincike ta zamani.

Source: Twitter
Mai sharhi kan al'amuran tsaro a Arewacin Najeriya da kuma Tafkin Chadi, Zagazola Makama ne ya rahoto nasarar 'yan sandan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An cafke masu garkuwa da mutane a Zamfara
Rahoto ya nuna cewa masu garkuwar da aka kama su ne Dalhatu Bashiru, wanda aka fi sani da Yellow, mai shekaru 38, da Chidiebere Nwadigo Emmanuel, mai shekara 34.
An ce dukkan mutanen biyun tsofaffin fursunoni ne, kuma suna cikin jerin wadanda ake nema kan ayyukan garkuwa da mutane da sace motocin alfarma a jihohi daban-daban.
A yayin samamen, jami’an Scorpion Squad sun kwato mota kirar Toyota Corolla mai lambar JUX 578 AA, farar Toyota Corolla JUX 890 AA, da Toyota Camry Pencil Light mai lambar APR 459 AE.
Yadda miyagun suka sace wani mutum a Abuja
Bincike ya gano cewa an taba kama waɗannan ake zargi a Nuwambar 2023 bisa irin wannan laifi, kuma an gurfanar da su a kotu. Sai dai bayan samun beli, sun koma gidan jiya.
Bisa bayanan da suka fito daga jami’an tsaro, wadanda ake zargin sun tabbatar da cewa sun yi garkuwa da wani Segun Akinwumi O a ranar 18 ga Janairu 2024 a kusa da otel din Rita Lori da ke Garki, Abuja.
Sun ce sun shiga gidansa ne suka yi awon gaba da shi zuwa hanyar Kano, inda suka tsaya a Kaduna suka karɓi katin ATM ɗinsa sannan suka cire ₦500,000 daga asusunsa.
Sai dai bayanai sun nuna cewa karyarsu ta kare ne bayan an cafke su a wani gidan sayar da fetur da ke Kaduna yayin da jami’an tsaro suka yi musu dirar mikiya, in ji rahoton News Express.

Source: Original
An gano bindigogi daga hannun 'yan ta'addan
A wancan lokacin, mutane uku daga cikin su sun tsere, amma an kama Chidiebere, Dalhatu (Yellow), daga bisani aka sake ganin suna fashi, har aka sake kama su yanzu.
A yanzu da aka kama su, jami’an tsaro sun gano bindigogi uku kirar Beretta, wadanda ake zargin suna amfani da su wajen garkuwa da mutane.
Hukumomin tsaro sun tabbatar da cewa wadanda ake zargin sun amsa cewa sun taba sace motoci sama da 20 irin SUV a Abuja cikin shekaru biyun da suka gabata.
A halin yanzu suna ci gaba da bincike da kokarin kamo sauran abokan aikinsu da suka tsere.
An cafke jagoran 'yan bindiga a Zamfara
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ’yan sanda sun kama jagoran ’yan bindiga Muhammadu Kan Kani (Akki), daga ƙaramar hukumar Bungudu, Zamfara.
An samu nasarar cafke hatsabibin dan bindigar ne a hanyar Kano zuwa Yankara (da ke jihar Katsina) bayan samun sahihan bayanan sirri.
Muhammadu Kan Kani (Akki) ya amsa cewa yana jagorantar ’yan bindigan da ke addabar garuruwan Tsafe, Yandoto da Yanwaren Daji a Zamfara.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


