An ‘Gano’ Wadanda Suka Yi Kokarin Hana Tinubu Zama Gwamnan Lagos a 1999
- Shugaban NDLEA, Buba Marwa ya yi magana game da Bola Tinubu da matsalolin da ya fuskanta kafin zama gwamnan Lagos
- Marwa ya bayyana cewa manyan sojoji sun yi ƙoƙarin hana Tinubu zama gwamnan jihar saboda gwagwarmayar da ya yi
- Ya ce duk da matsin lamba daga rundunar sojoji, ya gudanar da zabe sahihi wanda ya haifar da nasarar Tinubu a 1999
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban hukumar NDLEA, Buba Marwa, ya bayyana yadda ya yi kokarin gudanar da zabe sahihi a Lagos a 1999.
Marwa ya bayyana cewa wasu manyan hafsoshin soja sun yi yunkurin hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu zama gwamnan Jihar Lagos a 1999.

Source: Facebook
Yadda aka nemi hana Tinubu mulkin Lagos
Marwa ya yi wannan bayani ne a Abuja yayin taron gabatar da littafin marigayi Niyi Ayoola-Daniels mai suna Buni Boy, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Marwa, wanda ya jagoranci Jihar Lagos daga 1996 zuwa 1999, ya ce rundunar soja ta nemi hana ne Tinubu saboda ya taka a gwagwarmayar NADECO da ke kare dimokradiyya.
Ya ce mutanen Lagos sun nuna masa ƙauna da amincewa duk da cewa suna adawa da mulkin soja a lokacin, hakan ya sa ya dage wajen gudanar da zaben gwamna cikin gaskiya da rikon amana.
Ya bayyana cewa:
“Ko da shugaban kasa na wancan lokaci, Janar Abdulsalami Abubakar, bai tsoma baki ba, sai dai manyan hafsoshin soja sun matsa. Sun ce in hana Tinubu saboda yadda yake goyon bayan NADECO da adawa da mulkin soja.”

Source: UGC
Marwa ya fadi dalilin nasarar Tinubu a Lagos
Amma Marwa ya ce ya zabi bin gaskiya da sahihiyar dimokradiyya ta hanyar bari wanda ya fi karɓuwa a zaben watau Tinubu ya yi nasara.
Tsohon janar din ya ce shekarsa 30 a rundunar soja ta ƙarfafa imanin sa cewa Najeriya na iya kasancewa ƙasa ɗaya, domin soja na ƙoƙarin kawar da bambancin kabila ta hanyar auren juna da rayuwa tare.
Ya ce ko a kowane yanki, Ogoni, Bachama, Igbo ko Idoma yana jin kansa a matsayin ɗan gida, cewar rahoton Punch.
A ɓangaren tarihin gwagwarmayar Tinubu, an tuna yadda ya shiga jam’iyyar SDP a 1991, sannan ya zama sanata a 1992.
Bayan soke zaben June 12, Tinubu ya zama ɗaya daga cikin manyan jagororin NADECO da suka nemi dawo da dimokradiyya.
Ya gudu ƙasashen waje lokacin Sani Abacha, amma ya dawo 1998 bayan rasuwarsa, daga nan aka zaɓe shi gwamnan Lagos a 1999 ƙarƙashin jam’iyyar AD.
Tinubu ya sake nada Marwa shugaban NDLEA
An ji cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sabunta wa Mohammed Buba Marwa nadin shugabancin hukumar NDLEA na shekaru biyar masu zuwa.
Sabon wa’adin yana nufin Marwa zai ci gaba da jagorantar yaki da fataucin miyagun ƙwayoyi bayan gagarumin nasarar da aka samu tun 2021.
Bola Tinubu ya ce sake naɗin Marwa ya samo asali ne daga ƙoƙarinsa na dakile yaɗuwar miyagun ƙwayoyi da kare matasan ƙasar nan baki daya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

