Yadda Buhari ya kwaci Buba Marwa daga hannun yan jagaliyan da kyar a Adamawa

Yadda Buhari ya kwaci Buba Marwa daga hannun yan jagaliyan da kyar a Adamawa

A ranar Alhamis, 7 ga watan Feburairu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci gangamin yakin neman zabensa daya gudana a garin Yolan jahar Adamawa, sai dai ba wanye lafiya ba yayin da yan jagaliya suka yi yunkurin lakada ma wani tsohon gwamna dan banzan duka.

Shi dai wannan tsohon gwamna ba wani bane illa tsohon gwamnan jahar Legas a zamanin mulkin Soja, Janar Buba Marwa, wanda dan asalin jahar Adamawa ne, kuma jigo a cikin jam’iyyar APC, amma basa ga maciji da gwamnan jahar, Bindow Jibrilla.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Kotu ta tsige wani Sanatan APC daga kujerarsa, ta bayyana halastaccen dan takara

Yadda Buhari ya kwaci Buba Marwa daga hannun yan jagaliyan da kyar a Adamawa

Buba Marwa
Source: UGC

Yan jagaliyan sun nemi lakada ma Marwa dukan tsiya ne bayan an bashi fili domin gabatar da jawabinsa a yayin yakin neman zaben Buharin, sai dai sun zargeshi da furta kalaman batanci game da Gwamna Bindow.

Wadannan kalaman batanci da matasan suka zargi Marwa da fada ma gwamnan yasa suka nemi su cicciboshi daga mumbarin jawabi tare da zane masa jiki, da ba don Allah Yasa Buhari ya umarci jami’an tsaronsa su ceci Marwan ba, da kyar suka waske dashi, suka fice dashi daga cikin filin taron gaba daya.

Dama dai Buba Marwa baya inuwa daya da gwamnan jahar Adamawa, inda ya hada kai da uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari, da kuma kaninta Mahmoud Halilu don ganin sun hana Bindow samun tikitin takarar gwamna a karo na biyu.

Ko a ranar Litinin data gabata, Marwa ya jagoranci tawagar wasu tsofaffin gwamnonin mulkin Soja zuwa fadar shugaban kasa, inda suka bayyana goyon bayansu ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019, a yanzu haka Marwa ne shugaban kwamitin shugaban kasa akan yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi.

A yayin da yake gabatar da nasa jawabi, shugaba Buhari ya daukan ma al'ummar jahar Adamawa alkawarin kammala duk ayyukan daya fara a jahar, musamman ma wadanda ya faro tun a zamanin gidauniyar PTF.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel