Ana Tsaka da Zarge Zarge, Yan Bindiga Sun Kutsa Coci, Sun Sace Fasto da Matarsa

Ana Tsaka da Zarge Zarge, Yan Bindiga Sun Kutsa Coci, Sun Sace Fasto da Matarsa

  • Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani sabon coci da aka gina na Cherubim da Seraphim inda al'umma suka shiga dimuwa
  • Lamarin ya faru ne a garin Ejiba da ke karamar hukumar Yagba ta Yamma, inda suka kutsa cocin tare da sace Fasto da kansa
  • Shaidu sun ce masu ibada sun gudu domin tsira yayin da maharan suka yi harbi tare da yin garkuwa da Fasto Orlando, matarsa da wasu mambobi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Yagba, Kogi - Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki a sabon da aka gina a jihar Kogi da ke Arewacin Najeriya.

An tabbatar da cewa na kai harin ne a Cocin Cherubim da Seraphim da aka kafa a garin Ejiba da ke Karamar Hukumar Yagba ta Yamma.

Kara karanta wannan

Natasha ta yi barazana ga Sanata kan sakon WhatsApp, ta sha alwashin tona asiri

Yan bindiga sun sake kai hari cikin coci a Kogi
Taswirar jihar Kogi da aka sace Fasto da matarsa. Hoto: Legit.
Source: Original

Lamarin ya faru ne a yau Lahadi 30 ga watan Nuwambar 2025 lokacin da mambobin cocin ke gudanar da hidimar ibada, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda yan bindiga suka addabi jihar Kogi

Ko a kwanakin baya, yan bindiga sun kai farmaki kan wasu manyan daraktoci da ke kan hanyarsu ta zuwa Abuja daga jihar Lagos.

Maharan sun sace daraktoci shida na ma’aikatar tsaron ƙasa yayin da suke tafiya daga Lagos zuwa Abuja domin jarabawa.

Ƙungiyar ASCSN ta tabbatar da sace mutanen tare da bayyana sunayen waɗanda abin ya shafa inda ta yi kiran a yi gaggawar ceto su.

Yan bindiga sun addabi jihar Kogi
Gwamna Usman Ododo na jihar Kogi. Hoto: Alhaji Ahmed Usman Ododo.
Source: Facebook

Yan bindiga sun saxce Fasto da matarsa

Rahotanni daga mazauna yankin sun bayyana cewa an shiga tashin hankali bayan da maharan dauke da bindigogi suka afka cocin ba tare da wani gargadi ba.

Mutanen da ke cocin sun rika gudu don tsira da rayukansu yayin da karar harbe-harbe ya cika unguwar, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Mutane 6 sun mutu a hatsarin mota yayin dawowa daga jana'iza a ranar Juma'a

Shaidu sun tabbatar cewa Faston cocin, wanda ake kira Orlando, ya shiga cikin wadanda aka yi garkuwa da su.

An kuma ce matarsa da wasu mambobi da dama sun shiga hannun maharan wanda har yanzu ba a san inda suke ba.

Halin da ake ciki bayan harin yan bindiga

Mazauna yankin sun bayyana harin a matsayin abin firgici, domin maharan sun iso ne kwatsam, suka tarwatsa zaman cocin, suka kuma bar jama’a cikin tsananin tayar da hankali.

Har yanzu ba a san adadin mutanen da aka sace ba, domin babu sahihin bayani daga hukumomi.

Yayin da ake ci gaba da jimami, gwamnatin jihar da kuma rundunar ‘yan sanda ba su fitar da wata sanarwa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Yan bindiga sun sace jama'a a Kogi

A baya, an ji cewa Rundunar ‘yan sanda a jihar Kogi ta ce mutane biyu sun fada hannun ’yan bindiga a hanyar Isanlu zuwa Idofin da ke jihar.

An ce maharan sun tare fasinjoji uku a cikin mota, suka yi awon gaba da biyu, yayin da daya ya samu damar tserewa.

Kara karanta wannan

'Dan majalisa ya karbi mutane da 'dan bindiga ya saki bayan sulhu a Katsina

Rahoto ya nuna cewa wannan hari ya zo ne bayan sojojin sun ceci mutum biyar daga hannun 'yan bindiga a yankin da ke fama da matsaloli.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.