Bayan Komawa ADC, Atiku Ya Fara Zawarcin Mutanen da Za Su Yi Masa Mataimaki a 2027

Bayan Komawa ADC, Atiku Ya Fara Zawarcin Mutanen da Za Su Yi Masa Mataimaki a 2027

  • Ana ta shirye-shiryen fara buga gangar siyasa domin babban zaben shekarar 2027 da ake tunkara
  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya koma jam'iyyar ADC a wani mataki da ake gani na shirin tsayawa takara ne
  • Atiku ya fra duba mutanen da yake so su yi takara tare daga Kudancin Najeriya, ciki har da tsohon abokin takararsa a zaben 2019

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Bangaren tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a cikin jam’iyyar ADC ya fara shirin zaben 2027.

Bangaren na Atiku ya fara neman ɗan takarar mataimakin shugaban kasa daga Kudu domin takara a zaben shekarar 2027.

Atiku na neman mataimaki don takara a 2027
Peter Obi, Rotimi Amaechi da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar Hoto: @Peterobi, @ChibuikeAmaechi, @atiku
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce bangaren na Atiku ya karkata ne zuwa ga tsohon dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi.

Kara karanta wannan

Jonathan ya gana da Tinubu, ya fada masa abin da ya faru da shi a Guinea Bissau

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku na zawarcin Peter Obi da Amaechi

Wata majiya ta gayawa jaridar cewa idan Peter Obi ya ki amincewa ya tsaya tare da Atiku, to Atiku zai koma neman tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi.

Na kusa da Atiku, Dele Momodu, ya bukaci Peter Obi da ya hada kai da Atiku domin hambarar da Shugaba Bola Tinubu.

Momodu ya bayyana Atiku da Obi a matsayin zababbun mutane biyu mafi karfi da za su iya karɓe mulki daga APC.

Ya dora laifin rashin cimma matsaya tsakanin ɓangarorin biyu kan masu goyon bayan Peter Obi, yana gargadin cewa jinkiri na iya sa Obi ya rasa muhimmiyar dama ta siyasa.

Dele Momodu ya ce idan Peter Obi bai yanke shawara ba cikin gaggawa, Atiku zai iya zaɓar Amaechi a matsayin mataimakinsa.

“Mutane da yawa suna raina Amaechi. Amaechi shi kadai ne ya taimaka aka kawo Buhari mulki. Abin da Wike yake yi yanzu, ko da yake cikin rashin natsuwa, Amaechi ya yi shi cikin tsari lokacin da yake gwamna."

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Atiku ya hango jam'iyyar da za ta ceto 'yan Najeriya daga hannun APC

"Ya fi kowa kokari wajen kamfe na Buhari har ma fiye da Tinubu. Idan Peter Obi bai yanke shawara ba, to ina ganin Amaechi ne zai zama zabin karshe.”

- Dele Momodu

Peter Obi zai fito takara a 2027

Shugaban Obidient Movement na kasa, Yunusa Tanko, ya bayyana shirin Peter Obi na sake tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Mai magana da yawun na Peter Obi ya bukaci bangaren Atiku su fito ta fayyace abin da suke nema daga wajen tsohon gwamnan na jihar Anambra.

Ya yi nuni da cewa da wuya takara ta yiwu tare tsakanin Atiku da Peter Obi, inda ya bayyana cewa dan takara mai karfi ne daga Kudu zai iya kifar da Shugaba Tinubu a 2027.

Amaechi zai nemi tikitin ADC

A nasa bangaren, wani babban hadimin Amaechi ya bayyana cewa tsohon ministan yana neman tikitin shugaban kasa a jam'iyyar ADC.

Amaechi na shirin tsayawa takara a zaben 2027
Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi Hoto: @ChibuikeAmaechi
Source: Facebook

Sai dai ya ce akwai yiwuwar abubuwa su sauya kafin lokacin babban zabe, kuma lokacin batun mataimakin shugaban kasa bai yi ba tukunna.

“ADC na neman kuri’un Arewa. Don cimma haka, zai fi kyau jam’iyyar ta tsayar da dan takara daga Arewa."

Kara karanta wannan

Manyan hadakar adawa masu niyyar kifar da Tinubu sun shiga tattaunawar sirri

"Amma duk da haka, Amaechi na son tikitin shugaban kasa. Amma siyasa ce abubuwa na canzawa. Lokacin batun mataimaki bai yi ba tukuna. Mu jira.”

- Hadimin Amaechi

Atiku ya ba 'yan Najeriya shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bukaci 'yan Najeriya su mallaki katin zabe.

Atiku ya bayyana cewa katin zabe ne kawai zai ba su damar kawar da gwamnatin APC wadda ta jefa su cikin wahala.

Ya nuna cewa jam'iyyar ADC ce kadai zabin da 'yan Najeriya suke da shi domin ceto su daga kangin da APC ta saka su a ciki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng