Tuna Baya: Sanusi II Ya Fadi Yadda Dahiru Bauchi Ya ba Shi Darika, Ya ba Tijjaniya Shawara
- Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya jaddada muhimmancin hadin kan ’yan Tijjaniya, yana cewa ba za su bar masu adawa da su, su yi nasara ba
- Ya bayyana cewa ya fara karbar darika a hannun Shehu Dahiru Usman Bauchi wanda shi ne ya fara ba shi wuridin tarbiyya
- Sanusi II ya ce Shehu Dahiru Bauchi shi ne shehinsa har abada, yana kuma kira ga mabiyan Tijjaniya su kiyaye tarbiyya da kawar da rikici
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi magana game da hadin kan yan Tijjaniya a Najeriya da akidarsu.
Sanusi II ya yi karin haske game da yadda ya fara karbar darika a hannunsa inda ya ce yana mutunta Sheikh Dahiru Usman Bauchi a rayuwarsa.

Source: Facebook
Hakan na cikin wani tsohon bidiyo tun a 2022 da shafin Muhammad Sanusi II Study Snippets ya wallafa a X a jiya Asabar 29 ga watan Nuwambar 2025.
Shawarar Sanusi II ga 'yan Tijjaniya a Najeriya
Sarkin a wancan lokaci ya ce bai kamata su bari wasu a gefe musamman wadanda ke yakarsu su yi musu dariya.
Ya ce:
"Ka da mu yarda, wadanda suke wajenmu, wadanda suke yakarmu, wadanda suke son hura wuta a cikinmu su yi mana dariya.
"Fada tsakaninmu ba zai haifar da alheri ba, Sheikh Abdullahi Yabo ya fada muku na karbi darika a hannun Maulana Khalifah Sarki Muhammadu Sanusi.
"Amma akwai abin da watakila bai sani ba, shi ne wuridin tarbiya Shehi Dahiru Usman Bauchi ne ya bani wannan wuridi."

Source: Twitter
Sanusi II ya fadi wanda ya ba shi darika
Sarki Muhammadu Sanusi II ya Dahiru Bauchi shehinsa ne kuma akwai alaka mai karfi tsakaninsu har abada wacce ba zai manta ba.

Kara karanta wannan
Allahu Akhbar: An yi jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi, an birne gawarsa a masallaci
Ya ce yadda yake ganin Khalifan gidan Shehu Tijjani haka yake yi wa Sharif Sale da duk sauran shehunansu baki daya.
"Shehu Dahiru Bauchi shehi na ne, kuma wannan alaka tana nan har abada, yadda nake ganin Khalifan gidan Shehu Tijjani haka nake Sharif Sale da sauran shekunanmu baki daya."
- Sarki Sanusi II
Sarkin ya shawarce su da su yi kokari kamar yadda aka sansu da shi na kyakkyawar tarbiyya idan abubuwa sun taso, a kawar da kai za su wuce.
Ya ce zuwan Shehu kasar da haduwarsa da Sarki Alhaji tun 1937, a lokacin da ya zo, idan aka yi duba yanzu a nan gurin mutane daidai ne aka haife su.
Tuna baya: Dahiru Bauchi ya yiwa Sanusi addu'a
An ji cewa an tono tsohon bidiyon Sheikh Dahiru Bauchi yana jan hankalin al’ummar Kano da su guji tayar da hankula da gargadin cewa fitina za ta jawo hasara.
A bidiyon, marigayin ya bayyana cewa tashin hankali na iya jawo barna saboda masu kuɗi da iko za su iya ba da umarnin harbin mutane.
Sheikh Dahiru Bauchi ya shawarci mutane su bar komai ga ikon Allah, yana rokon Ubangiji ya kare jama’a tare da yi wa Sarki Sanusi II fatan alheri.
Asali: Legit.ng

