Ana Wata ga Wata: 'Yan Bindiga Sun Tare Hanya, Sun Sace Matafiya a Jihar Kogi
- Rundunar ‘yan sandan Kogi ta ce mutane biyu sun fada hannun ’yan bindiga a hanyar Isanlu zuwa Idofin da ke jihar
- An ce maharan sun tare fasinjoji uku a cikin mota, suka yi awon gaba da biyu, yayin da daya ya samu damar tserewa
- Rahoto ya nuna cewa wannan hari ya zo ne bayan sojojin sun ceci mutum biyar daga hannun 'yan bindiga a yankin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kogi - Rundunar ’yan sandan jihar Kogi ta tabbatar cewa ’yan bindiga sun tare hanyar da ke tsakanin Isanlu da Idofin inda suka yi garkuwa da mutane biyu.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP William Aya, ya tabbatar da lamarin a daren Asabar, inda ya ce matafiyaa uku ne aka farmaka.

Source: Twitter
'Yan bindiga sace matafiya a Kogi
SP William Aya ya ce mutum daya mai suna Raji Adesukanmi ne kawai ya kubuta, yayin da sauran biyun aka tafi da su cikin daji, in ji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda ’yan sanda suka bayyana, mutanen uku suna tafiya ne cikin motarsu lokacin da maharan suka tare su.
SP Aya bai bada cikakken bayani game da yadda aka yi harin ba, amma ya ce sace-sacen na gudana ne a yanki mai fama da hare-hare a baya-bayan nan.
A cewarsa, harin ya sake tayar da hankali a tsakanin mazauna Yagba ta Gabas da sauran yankuna da ke makwabtaka.
An tura jami'an tsaro don aikin ceto
Kakakin rundunar ya ce kwamishinan ’yan sanda na jihar ya tura tawaga ta musamman wacce ta kunshi dakarun kai daukin gaggawa, dakarun yaki da garkuwa da mutane da dakarun MOPOL domin shiga daji su kubutar da wadanda aka sace.
Sanarwar ta ce rundunar za ta tabbatar cewa ba a cutar da wadanda aka sace ba, yayin da kuma take ci gaba da sintiri mai karfi a yankin, in ji rahoton Shahara Reporters.

Kara karanta wannan
Ngige: An ji halin da ministan Buhari ke ciki bayan 'yan bindiga sun bude wa motarsa wuta
Mazauna yankin sun ce hare-hare irin wannan suna faruwa a kai a kai har zuwa kananan hukumomin da ke kusa da jihar Kwara da sauran yankunan Arewa ta Tsakiya.

Source: Original
Sojoji sun ceto mutane 5 kafin sabon hari
Kwanaki kadan kafin sabon harin, rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar cewa ta ceci mutum biyar a yankin Isanlu–Egbe bayan kai samame biyu.
Sojojin Brigedi ta 12 sun ce sun yi arangama da ’yan bindiga a wurare biyu da suka yi garkuwa da mutane daban-daban.
Bayan musayar wuta, ’yan bindigar sun gudu suka bar wadanda suka sace, wadanda aka cece su ba tare da wani ya ji rauni ba.
Sojojin sun bayyana cewa suna ci gaba da sintiri don hana maharan samun damar kai farmaki a nan gaba.
An kashe mutum 2 a harin 'yan bindiga a Kogi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kashe mutum biyu a harin da suka kai makarantar Kiri da ke karamar hukumar Kabba-Bunu, jihar Kogi.
Shugaban karamar hukumar Kabba-Bunu, Barista Zacheus Dare, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an dakile wannan hari.
Sai dai kuma, gwamnatin jihar Kogi ta karyata jita-jitar an yi garkuwa da ɗaliban makarantar, tare da barazanar kama masu yada karyar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

