Mutane 6 Sun Mutu a Hatsarin Mota yayin Dawowa daga Jana'iza a Ranar Juma'a
- An tabbatar da cewa hatsarin mota ya kashe mutane shida bayan karo tsakanin motar diban kasa da wata Bus
- Majiyoyi sun tabbatar da mutuwar mutanen wadanda aka ce sun rasa ransu ne yayin da suke dawo wa daga jana'iza
- FRSC ta tabbatar da cewa hatsarin ya faru sakamakon sakaci da gaggawar direba, inda mutane 32 suka tsira da raunuka
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Awka, Anambra - Rahotanni sun tabbatar da cewa mutane shida sun mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya hada tifa da bas.
Mutane shidan sun rasa ransu a kusa da Enugu-Agidi, kan titin Awka–Onitsha a Anambra da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.

Source: Original
Hatsarin mota ya lakume rayuka
Punch ta ce hatsarin ya faru daren Juma’a 28 ga watan Nuwambar 2025 saboda gaggawa da saurin direbobin tifar mai launin rawaya da baki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fasinjojin da suka mutu suna dawowa gida ne daga jana’izar da aka gudanar a jihar Ebonyi, inda suka shiga hanya domin komawa wuraren su.
Kwamandar FRSC ta Anambra, Bridget Asekhauno, ta tabbatar da faruwar hatsarin cikin sanarwa, tana mai cewa rashin kulawar direba ne babban dalilin.
Ta bayyana cewa mutane 32 ne suka shiga hatsarin, ciki har da maza tara da mata 23, tare da mutuwar mutum shida nan take.
Ta ce mata biyar ne suka jikkata yayin mutane 21 suka tsira ba tare da rauni ba, kuma an garzaya da su asibitin Amaku na Awka.

Source: Facebook
Yadda hatsarin mota ya faru
Shaidu daga cikin bas sun ce direba yana gaggawar wucewa da sauri, yana kokarin samun dama, kafin ya afka cikin tipar da ke tahowa gaba.
Ta ce:
“An kai dukkan waɗanda suka jikkata Asibiti Amaku, Awka, inda ma’aikatan lafiya suka tabbatar da mutuwar su. An cire cinkoson da ya rufe hanya, kuma zirga-zirga ta koma yadda ta saba.

Kara karanta wannan
Ngige: An ji halin da ministan Buhari ke ciki bayan 'yan bindiga sun bude wa motarsa wuta
“Wani shaida, wanda shi ne fasinja a cikin motar, ya ce sun taso daga jihar Ebonyi zuwa Onitsha bayan halartar jana’izar da Kungiyar Mata ta Katolika ta shirya.
“Shaidan ya bayyana cewa direban yana tuki ba bisa ƙa’ida ba, yana yawan wuce motoci."
FRSC ta bayyana hatsarin a matsayin gargadi mai tsanani kan illar sakaci da saurin tuki, tana mika ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a hatsarin mota.
Hukumar ta jaddada kudirinta na ci gaba da wayar da kai, tabbatar da bin dokoki, da taimaka wa wadanda suka tsira a irin wadannan lamurra, cewar Vanguard.
Tirela ta markade mutane, an rasa rayuka
A baya, mun ba ku rahoto cewa an rasa rayuka da dama da wata tirela dauke da buhunan siminti ta sauka daga kan titi, ta fada kan mutane a jihar Ondo.
Rahoto ya nuna lamarin ya faru ne a kusa da Jami’ar Adekunle Ajasin da ke Akungba Akoko, a karamar hukumar Akoko ta Yamma.
Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) ta tabbatar da mutuwar mutum takwas a hatsarin, ta kuma gargadi direbobi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
