Farfesa Mahmud Yakubu da Wasu 'Yan Arewa 14 da Tinubu Ya Nada Jakadun Najeriya

Farfesa Mahmud Yakubu da Wasu 'Yan Arewa 14 da Tinubu Ya Nada Jakadun Najeriya

  • Shugaba Bola Tinubu ya sanya sunayen mutane 15 daga Arewa cikin sababbin jakadun da ya tura majalisar dattawa
  • Sababbi jakadun daga Arewa sun fito daga jihohi daban-daban: Adamawa, Katsina, Borno, Kebbi, Jigawa, Plateau da Niger
  • Ana sa ran za a tura sababbin wadanda aka nada zuwa kasashen da Najeriya ke da kyakkyawar alakar da ke tsakaninsu

Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aika jerin sunayen mutanen da ya zaɓa don zama jakadun Najeriya zuwa ƙasashen waje.

Daga cikin sunaye mutane 35 da Tinubu ya aike wa majalisar, an gano cewa mutane 15 sun fito ne daga Arewacin Najeriya.

Farfesa Yakubu da wasu 'yan Najeriya 14 sun shiga jerin sababbin jakadun Najeriya
Farfesa Mahmdu Yakubu, tsohon shugaban INEC da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: @inecnigeria
Source: Facebook

Tinubu ya nada sababbin jakadun Najeriya

Wata sanarwa da aka wallafa a shafin gwamnatin tarayya na intanet ya nuna cewa, Tinubu ya aika wa majalisar sunayen ne a wasiku daban daban.

Ana sa ran za a tura sababbin wadanda aka nada zuwa kasashen da Najeriya ke da kyakkyawar alakar da ke tsakaninsu, kamar China, Indiya, Koriya ta Kudu, da Kanada.

Kara karanta wannan

PDP ta taso Tinubu a gaba kan nada jakadu, ta bayyana kuskuren da ya tafka

Sauran kasashen sun hada da Mexico, Hadaddiyar Daular Larabawa, Qatar, Afirka ta Kudu, Kenya, da kuma jakadun Majalisar Dinkin Duniya, UNESCO, da Tarayyar Afirka.

A makon da ya gabata ne dai shugaba Tinubu ya aika da sunayen jakadu uku domin tantancewa da tabbatar da su, kamar yadda muka ruwaito.

Wadanda aka nada sun hada da Ambasada Ayodele Oke (Oyo), Ambasada Amin Mohammed Dalhatu (Jigawa), da Kanar Lateef Kayode Are (mai ritaya daga Ogun).

'Yan Arewa 15 a jerin sababbin jakadun Najeriya

1. Ambassador Amin Mohammed Dalhatu — Jigawa

2. Yakubu Nyaku Danladi — Taraba

3. Miamuna Ibrahim Besto — Adamawa

4. Musa Musa Abubakar — Kebbi

5. Hamza Mohammed Salau — Niger

6. Ambassador Shehu Barde — Katsina

7. Ambassador Ahmed Mohammed Monguno — Borno

8. Ambassador Muhammad Saidu Dahiru — Kaduna

9. Ambassador Olatunji Ahmed Sulu Gambari — Kwara

10. Mahmud Yakubu — Bauchi

11. Tasiu Musa Maigari — Katsina

12. Yakubu N. Gambo — Plateau

13. Professor Nora Ladi Daduut — Plateau

14. Grace Bent — Adamawa

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban INEC ya samu mukami da Tinubu ya nada sababbin jakadun Najeriya 32

15. Ambassador Paul Oga Adikwu — Benue

Yadda aka rarraba matsayin sababbin jakadun Najeriya

Shugaba Bola Tinubu ya aika wa majalisar dattawa sunayen sababbin jakadun da zai nada.
Shugaba Bola Tinubu ya na gabatar da jawabi a zauren majalisar tarayya. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Jaridar Punch ta rahoto cewa, Tinubu ya bukaci majalisar da ta tantance tare da tabbatar da mutane 15 da aka nada a matsayin jakadun aiki da kuma mutane 17 a matsayin jakadun da ba na aiki ba.

Akwai mata hudu a cikin jerin jakadun aiki da kuma mata shida a cikin jerin jakadun da ba na aiki ba.

- Jakadun da ba na aiki ba

Daga cikin wadanda ba jakadan aiki ba akwai Barista Ogbonnaya Kalu daga Abia, Reno Omokri (Delta), Mahmud Yakubu, Erelu Angela Adebayo, Ifeanyi Ugwuanyi.

Sauran sun hada da Tasiu Musa Maigari, Yakubu N. Gambo, Farfesa Nora Ladi Daduut, Otunba Femi Pedro, Cif Femi Fani-Kayode, da Barista Nkechi Linda Ufochukwu

A cikin jerin sunayen akwai Fatima Florence Ajimobi, Lola Akande, Grace Bent, Victor Okezie Ikpeazu, Sanata Jimoh Ibrahim da kuma Ambasada Paul Oga Adikwu.

- Jakadun aiki

Kara karanta wannan

Tinubu ya nada shugaban NIA da ya shiga badakalar $43m lokacin Buhari a matsayin Jakada

Daga cikin wadanda aka zaba a matsayin jakadan aiki da kuma babban kwamishina mai suna: Enebechi Monica Okwuchukwu (Abia), Yakubu Nyaku Danladi (Taraba), Miamuna Ibrahim Besto (Adamawa), Musa Musa Abubakar (Kebbi), Syndoph Paebi Endoni (Bayelsa), Chima Geoffrey Lioma David (Ebonyi) da Mopelola Adeola-Ibrahim (Ogun).

Sauran wadanda aka nada sun hada da Abimbola Samuel Reuben (Ondo), Yvonne Ehinosen Odumah (Edo), Hamza Mohammed Salau (Niger), Ambasada Shehu Barde (Katsina), Ambasada Ahmed Mohammed Monguno (Borno), Ambasada Muhammad Saidu Dahiru (Kaduna), Ambasada Olatunji Ahmed Sulu Gambari (Kwara) da Ambasada Wahab Adekola Akande (Osun).

Farfesa Yakubu ya sauka daga shugaban INEC

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Farfesa Mahmood Yakubu ya sauka daga matsayin shugaban hukumar zabe ta kasa watau INEC.

Farfesa Yakubu ya mika ragamar shugabancin hukumar ga May Agbamuche, wacce za ta rike INEC kafin nadin sabon shugaba

Tun a shekarar 2015, marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nada Mahmood Yakubu a matsayin shugaban INEC na kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com