Gwamna Uba Sani Ya Gano Matsalolin da Ke Rura Wutar Rashin Tsaro a Arewa
- Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya nuna damuwa kan matsalar rashin tsaro da ta addabi yankin Arewa maso Yamma
- Uba Sani ya bayyana cewa fataucin miyagun kwayoyi na daga cikin abubuwan da ke kara ta'azzara matsalar rashin tsaro
- Gwamnan ya nuna cewa amfani da karfin bindiga kadai ba zai kawo karshen matsalar rashin tsaron da ake fama da ita
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ke addabar yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
Gwamna Uba Sani ya ce iyakokin kasar nan da ke a bude da yawaitar fataucin miyagun kwayoyi na daga cikin manyan abubuwan da ke hura wutar rashin tsaro a yankin.

Source: Facebook
Jaridar The Cable ta ce Gwamna Uba Sani ya bayyana haka ne a ranar Asabar yayin taron samar da tsaro da kwamitin wucin-gadi na majalisar dattawa kan harkokin tsaro ya shirya a Kaduna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadanne matsaloli Uba Sani ya ambato?
Gwamnan ya ce masu fataucin miyagun kwayoyi da masu safarar kayayyaki na tsallake iyaka cikin sauki sosai, sannan idan an matsa musu, suna guduwa zuwa kasashe makwabta.
Ya kara da cewa wadannan bata-garin suna shigo da makamai ta iyakokin, lamarin da ya haifar da yaduwar makamai kimanin adadin miliyoyi a yankin.
Uba Sani ya bayyana fataucin miyagun kwayoyi a matsayin manyan hanyoyin samar da kudaden da ’yan bindiga ke amfani da su.
Ya yi nuni da cewa shaye-shaye a tsakanin matasa na karfafa wa kungiyoyin ta’addanci guiwa, saboda ana amfani da miyagun kwayoyi don razana ko bautar su.
Gwamna Uba Sani ya ce dole ne a hada dabarun soja da aikin al’umma da kuma tsare-tsaren ci gaba na dogon lokaci idan za a murkushe matsalar.
Ya ce yankin Arewa maso Yamma na bukatar tsarin tsaro da ya dace da girman kalubalen da ake fuskanta.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta biya kudin fansa kafin ceto 'daliban Kebbi? Majalisa ta yi bayani
Uba Sani ya bada shawara kan rashin tsaro
Gwamnan ya yi kira da a samar da hedkwatar sojoji ta musamman a yankin Arewa maso Yamma, wadda za ta hada Division na 1 da Division na 8 a karkashin shugabanci guda.
Ya ce hakan zai hanzarta musayar bayanan sirri, karfafa hadin gwiwar aiki, tare da rushe hanyoyin manyan kungiyoyin ta’addanci da ke yawo jihohi daban-daban.
Gwamna Uba Sani ya kuma bada shawarar a fadada aikin rundunar Multinational Joint Task Force (MNJTF) zuwa kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar, yana mai cewa tsarin ya yi gagarumin tasiri a yankin Tafkin Chadi, Daily Post ta kawo rahoton.
“Wannan fadadawar za ta katse hanyar shigo da makamai, ta hana ’yan ta’adda wuraren fakewa a kasashe makwabta, tare da raunana hanyoyin da ke tallafa musu."
- Gwamna Uba Sani

Source: Facebook
Ya kara da cewa amfani da karfin bindiga kai tsaye ba zai magance matsalar ba, yana mai jaddada cewa hadin kan al’umma shi ne ginshikin da za a gina kowane tsarin tsaro mai dorewa a kai.
Gwamnan ya bada shawarar kafa kwamitocin tsaro na dindindin a matakan jihohi da kananan hukumomi.
Kwamitocin za su kunshi sarakunan gargajiya, shugabannin addini, kungiyoyin mata, kungiyoyin matasa, kungiyoyin farar hula, hukumomin tsaro domin tabbatar da cewa tsaro ya zama aikin kowa.
'Yan bindiga sun sace mutane a Kaduna
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun hallaka daya daga cikin fastocin cocin HEKAN a Kaduna.
An kuma sace mutane fiye da 20 a mummunan hari da ’yan bindiga suka kai a Farin Dutse, ƙaramar hukumar Kauru.
'Yan bindigan da ke ɗauke da makamai sun mamaye garin, inda suka rika harbi ba kakkautawa, lamarin da ya jefa mazauna cikin firgici.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

