Babban Fasto Ya Cire Tsoro, Ya Fadi Gaskiya game da 'Kisan Kiristoci' a Najeriya

Babban Fasto Ya Cire Tsoro, Ya Fadi Gaskiya game da 'Kisan Kiristoci' a Najeriya

  • Bishop Matthew Kukah ya ce maganganun da ake yadawa kan cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya ba su da tushe
  • Ya bayyana cewa masu maganganun ba su da cikakkun alkaluma na yawan coci ko Kiristocin da ake cewa an kashe su
  • Kukah ya jaddada cewa idan Kiristoci suna ganin ana zaluntar su, su kalli irin matsayin da suke da shi a Najeriya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Shugaban Darikar Katolika na Sokoto kuma jagoran Kwamitin Zaman Lafiya na Kasa, Bishop Matthew Kukah, ya karyata ikirarin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya.

Ya ce wadannan jita-jita sun fi kama da siyasa da rashin tantance bayanai fiye da gaskiyar abin da ke faruwa a kasar nan.

Bishop Mathew Kuka ya warware rudanin da aka samu game da zargin kisan Kiristoci a Najeriya.
Shugaban darikar Katolika na Sokoto, Bishop Mathew Kukah ya yi magana kan kisan Kiristoci a Najeriya. Hoto: @KukahBishop
Source: Twitter

Fasto ya karyata zargin kisan Kiristoci

Kara karanta wannan

"Mun san su": Sanata Maidoki ya ba gwamnati zabi 2 kan kawo karshen 'yan bindiga

A cewarsa, duk wata magana da ake yi a kasashen waje cewa Kiristoci na fuskantar matsanancin barazana a Najeriya ba ta da tushe, in ji rahoton Vanguard.

Bishop Kukah ya nuna mamaki kan rahotannin da ke cewa ana kona cocin Kiristoci 1,200 a Najeriya a duk shekara.

Ya tambaya ko wace kasa ake nufi, domin babu wata hukuma ko cibiyar addini da aka tambaya kafin wallafa irin wannan kididdiga.

Ya kara da cewa cocin Katolika ba ta da al’adar yin gulma ko yarda da bayanan da ba su da tushe, kuma wannan na nuna cewa ana yada labarai ne domin siyasa ko tada hankali.

Kisan kiyashi: Fasto Kukah ya warware rudani

Bishop Kukah ya yi karin bayani kan batun kisan kare dangi, yana mai cewa ba yawan wadanda aka kashe ake dogaro da shi ba wajen yanke hukunci.

Ya ce ana kallon manufar wanda ya aikata laifin: shin an yi shi ne da nufin kawar da wani rukuni gaba ɗaya?

Babban malamin ya ce rashin fahimtar wannan ka’ida na sa mutane su yi gaggawar kiran duk wani hari da zai faru a kasar a matsayin kisan kiyashi.

Kara karanta wannan

Trump: Masana tsaro sun fayyace gaskiya kan batun sojojin Amurka sun iso Arewa

Bishop Kukah ya ce masu yada cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi ba su da cikakkun alkaluma.
Fitaccen malamin addinin Kirista, Bishop Mathew Kukah ya yi wa Kiristoci tambaya. Hoto: @KukahBishop
Source: Facebook

Tambayar Bishop Kukah ga Kiristoci

Bishop Kukah ya kalubalanci wadanda ke cewa Kiristoci suna fuskantar danniya a Najeriya. Ya bayyana cewa mafi yawan ’yan Najeriya masu ilimi Kiristoci ne.

Babban malamin ya ce kashi 85% na tattalin arzikin Najeriya na hannun Kiristoci kuma wannan ya isa ya nuna cewa Kiristoci suna da matsayi da karfi a kasar.

Kukah ya dora wasu matsalolin da Kiristoci ke fuskanta a kan rashin hadin kai, inda ya ce sau da yawa suna bari a tsoratar da su ko a dannesu saboda basu tsaya tsayin daka tare ba.

Ya jaddada bukatar Kiristoci da sauran ’yan Najeriya su dinga yin zurfin tunani kafin su yi hasashe game da kowanne hari da ake kaiwa a kasar.

An kai karar Najeriya Majalisar Dinkin Duniya

A wani labari, mun ruwaito cewa, Jakadan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Michael Waltz, ya koka kan karuwar ta'addanci a Najeriya.

Kara karanta wannan

Trump: Malaman Musulunci da Kirista sun hada kai, sun shawarci mabiyansu

Michael Waltz ya gabatar da rahoto ga kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya kan abin da ya kira kisan gilla ga dubban Kiristoci a Najeriya.

Har ila yau, Waltz ya koka kan kona kauyuka da kuma harin da ake kai wa shugabannin coci a yankunan da rikice-rikice suka dabaibaye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com