Jonathan Ya Gana da Tinubu, Ya Fada Masa Abin da Ya Faru da Shi a Guinea Bissau
- Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya dawo Najeriya cikin koshin lafiya bayan rigimar siyasa da ta barke a Guinea-Bissau
- Jonathan ya gana da Tinubu a fadar shugaban kasa na Aso Rock Villa kan rikicin siyasar da ya barke a kasar bayan juyin mulki
- ECOWAS da AU sun yi tir da juyin mulkin, suka dakatar da Guinea-Bissau, tare da shirya tawagar sulhu domin dawo da tsarin mulki
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Jonathan, ya kai ziyara ta musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa.
Jonathan ya gana da Tinubu ne a ranar Asabar 29 ga watan Nuwambar 2025 domin yi masa bayani kan rikicin siyasar da ta barke a Guinea-Bissau.

Source: Twitter
Hakan na ciki wata sanarwa da hadimin shugaban kasa kan yada labarai, Bayo Onanuga ya wallafa a shafin X.

Kara karanta wannan
Guinea Bissau: Gwamnatin Tinubu ta faɗi halin da Jonathan ke ciki bayan ya maƙale
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda Jonathan ya makale a Guinea-Bissau
Ziyarar ta biyo bayan ceto Jonathan da aka yi daga kasar wadda sojoji suka karɓe iko kwanaki kadan da suka gabata.
Jonathan ya kasance a Guinea-Bissau ne a matsayin shugaban tawagar sa ido kan zabe, lokacin da wasu hafsoshin soja suka hambarar da gwamnati.
A ranar Laraba 26 ga watan Nuwambar 2025, sojojin kasar suka sanar da cewa “sun karɓi cikakken iko”, suka dakatar da tsarin zabe, tare da rufe iyakokin Guinea-Bissau, abin da ya tayar da hankulan ƙasashen yammacin Afrika.
Gwamnatin tarayya ta Najeriya ce ta tabbatar da ceto Jonathan, inda aka tashi jirgi na musamman tare da taimakon gwamnatin Ivory Coast domin dawo da tsohon shugaban gida lafiya.
Da yake magana da ’yan jarida bayan dawowarsa, Jonathan ya bayyana abin da ya faru a matsayin wani “shiryayyen juyin mulki”, yana nuni da cewa lamarin na iya kasancewa shirin tsohon shugaban kasar ne, ba yunkurin soja kai tsaye ba.

Kara karanta wannan
Majalisa ta tsoma baki da Jonathan ya makale a kasar da sojoji suka yi juyin mulki
Ganawar Jonathan da Tinubu a Abuja
Bayan ganawa da Tinubu a Abuja, Jonathan ya fadawa yan jaridu dalilin ziyarar ta shi zuwa fadar shugaban kasa.
Ya ce:
“An kammala zaben, sakamakon ya fito, dole a bayyana wanda ya ci zaben… shugabannin ECOWAS su tuntubi jagororin sojin don su saki dan adawa, sannan su bayyana sakamakon.”
A bangaren kasashen yammacin Afrika, ECOWAS ta dakatar da Guinea-Bissau daga dukkan muhimman harkokinta, tare da sanar da turo tawagar sulhu domin matsa kaimi kan mayar da tsarin mulki.
Haka zalika, kungiyar Tarayyar Afrika (AU) ta yi tir da juyin mulkin, tana cewa hakan ya sabawa tafarkin dimokuraɗiyya, tare da tabbatar da manufarta ta rashin yarda da duk wani karɓe ikon da bai bi doka ba.
Guinea-Bissau: Gwamnati ta magantu kan Jonathan
An ji cewa Gwamnatin tarayya ta yi magana bayan tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya makale a Guinea-Bissau.
Ma'aikatar harkokin waje a Najeriya ta ce Goodluck Jonathan ya bar Guinea-Bissau lafiya bayan rikicin shugabanci.
Jami’in ma’aikatar, Kimiebi Ebienfa, ya ce Jonathan ya tashi musamman tare da tawagarsa, ciki har da babban jami'in diflomasiyya, Ibn Chambas.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
