An Tsinci Gawar Tsohuwar Babbar Alkali a Mummunan Yanayi a cikin Gidanta

An Tsinci Gawar Tsohuwar Babbar Alkali a Mummunan Yanayi a cikin Gidanta

  • Ana cikin firgici a Asaba bayan gano gawar tsohuwar Alkali, Ifeoma Okogwu cikin wani irin mummunan yanayi a cikin gidanta
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa an samu gawar matar ne a daure da hannayenta da kuma kafafu wanda ke nuna kisan gilla
  • ’Yan sanda sun kama wasu masu gadi yayin da ɗaya ya tsere, suna ci gaba da bincike don gano hakikanin abin da ya faru

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Asaba, Delta - Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Delta ta tabbatar da kisan gillar da aka yi wa tsohuwar alkalin jihar, Justice Ifeoma Okogwu.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an gano gawar marigayiywar a Asaba cikin yanayi mai tayar da hankali.

An tsinci gawar tsohuar alkali a Delta
Kakakin yan sanda a Delta, Bright Edafe. Hoto: Nigeria Police Force Delta State Command.
Source: Twitter

Rahoton The Guardian ya ce an tabbatar da mutuwar Okogwu ne a daren Lahadi 23 ga watan Nuwambar 2025.

Kara karanta wannan

Daga cacar baki, matasa sun caccaka wa babban dan sanda wuka, ya sheka lahira

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An samu gawar tsohuwar alkalin Delta

An ce an samu gawarta a gidanta da ke bayan ofishin jaridar The Pointer abin da ya tayar da hankulan mazauna yankin.

Majiyoyi sun nuna an daure kafafunta da hannayenta, an kuma lalata ko’ina cikin gidan, alamar an kai harin ne da gangan.

Abin da ya kara rikitar da binciken shi ne bacewar mai gadin dare da aka tura gidan, wanda ya makale ba a gan shi ba tun bayan faruwar lamarin.

Wannan ya kara zargin cewa akwai hannun wasu da suka san gidan sosai inda aka bukaci daukar matakai masu tsauri.

Dan’uwan mamaciyar, Ogbueshi Godfrey Okogwu, ya bayyana cewa:

“An kashe babbar ’yar uwata a gidanta daren Lahadi. Mun samu labari ne da safiyar Litinin, don haka lamarin ya faru cikin dare.
“Abu mafi tayar da hankali shi ne bacewar mai gadin dare. Mai gadin safe ya ce ya zo ya tarar da kofar gida a bude. Ya ce ya zauna a can. Don yin me? Ban fahimta ba.”

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun harbe matar da ke daukarsu bidiyo yayin hari kan tsohon gwamna

An kama masu gadi kan zargin kisan tsohuwar alkali
Taswirar jihar Delta a Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

'Dan uwan marigayiyar ya yi magana

Okogwu ya bayyana cewa sun gabatar wa ’yan sanda cikakken bayani game da kamfanin tsaro da ya turo ma’aikatansa gidan, cewar Sahara Reporters.

Ya kara da cewa:

“’Yan sanda sun tsare mai gadin safe, sun kuma kira mai kamfanin tsaro zuwa ofis. Ba mu san ko ya bayyana ba.”
“Allah kadai ya san abin da ya faru. Ba za mu san cikakken bayani ba sai an kammala binciken ’yan sanda.”

Mai magana da yawun ’yan sandan Delta, DSP Bright Edafe, ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin Legit Hausa.

Edafe ya ce tabbas ana ci gaba da bincike bayan kama daya daga cikin masu gadin da ake zargin su da hannu a lamarin.

Ya ce:

“Wasu daga cikin masu gadin suna hannun ’yan sanda, yayin da ɗaya ya tsere.”

An tsinci gawar jarumin fim a otal

An ji cewa jarumin fina finan Najeriya kuma mai wasan barkwanci, Odira Nwobu ya mutu a Afirka ta Kudu yana da shekaru 43.

Kara karanta wannan

Sojar Amurka ta rasu bayan harin da dan bindiga ya kai musu, Trump ya fusata

An ce an tsinci gawarsa a cikin dakin otel din da ya sauka, bayan ya je Afrika ta Kudu daukar tallar wani kamfani.

An ga jarumin kwance a gado a wani bidiyo da ya yadu a kafar sadarwa, abin da ya jawo martani daga abokan sana'arsa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.