Lokaci Ya Yi: Tsohon Gwamna Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Najeriya, An Yi Jana'iza

Lokaci Ya Yi: Tsohon Gwamna Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Najeriya, An Yi Jana'iza

  • An birne tsohon kwamandan sojoji a Najeriya kuma tsohon gwamnan yankin Kudu maso Gabas da cikakken girmamawar soja a jihar Delta
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa Manjo Janar Paul Ufuoma Omu (mai ritaya) ya mutu yana da shekaru 84 da haihuwa
  • Manyan jami’an rundunar sojojin Najeriya, ’yan siyasa da sarakunan gargajiya sun halarci jana'izan domin karrama marigayin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Delta, Nigera - A kwanakin baya aka tabbatar da rasuwar tsohon gwamnan mulkin soji na Jhar Kudu maso Gabas (wacce yanzu ta kasu zuwa jihohin Kuros Riba da Akwa Ibom), Manjo Janar Paul Ufuoma Omu (mai ritaya).

Rahoto ya nuna cewa a yau Asabar, 29 ga watan Nuwamba, 2025 aka yi jana'izar tsohon gwamnan a mahaifarsa Igbide, cikin Karamar Hukumar Isoko ta Kudu, Jihar Delta.

Paul Ufuoma Omu
Sojoji dauke da gawar marigayi Manjo Janar Paul Ufuoma Omu (mai ritaya) Hoto: Chief Feguson Onwo
Source: Facebook

An birne tsohon gwamna a Delta

Kara karanta wannan

Obasanjo ya fadi matsayarsa kan tattaunawa da 'yan bindiga, ya ba gwamnati shawara

Jaridar The Nation ta tattaro cewa an yi bikin jana'iza da birne mamacin cikin girmamawa ta musamman ta rundunar sojojin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayin, wanda ya rasu yana da shekaru 84, ya kasance dattijo mai hikima kuma tsohon shugaban kungiyar ci gaban Isoko (IDU),

Haka zalika ana ganin Manjo Janar Omu na ɗaya daga cikin fitattun kwamandojin sojoji da suka yi fice a tarihin Najeriya.

Jana’izar ta samu halartar manyan baki daga rundunar sojin Najeriya, shugabannin siyasa da sarakunan gargajiya, wadanda suka bayyana shi a matsayin abin koyi wajen kishin ƙasa, ladabi da jagoranci na gari.

Yadda aka yi addu'o'i a cocin Delta

An gudanar da hidimar jana’izar a Cocin St. Andrew’s Anglican, Igbide, inda aka yi waƙoƙin bege, addu’o’i, da karatun Littafi Mai Tsarki daga Yohanna 11:25–26.

Babban limamin Cocin Anglican na Bendel Province, Rabaran Cyril Odutemu, ya yaba wa marigayin bisa yadda yake da kishin kasa, da jajircewa wajen hidimar jama’a.

Ya bayyana shi a matsayin, “daya daga cikin klilan din ’yan Najeriya da suka yi imanin cewa ƙasar nan ta cancanci a sadaukar da rai domin ita.”

Kara karanta wannan

Babbar magana: Gwamnatin Kano ta bukaci a kama tsohon shugaban APC, Ganduje

Tawagar gwamnatin Delta da ta halarci jana'izar

Tawagar gwamnatin jihar Delta da ta halarci jana'izar ta haɗa da Gwamna Sheriff Oborevwori da matarsa Tobore, Tsohon Gwamna James Ibori, tsohon Gwamna, Ifeanyi Okowa da matarsa Edith.

Sauran sun hada da Tsohon Mataimakin Gwamna Benjamin Elue, Sanata Joel-Onowakpo Thomas, Rear Admiral Mike Onah, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Delta, Rt. Hon. Emomotimi Guwor da Sakataren Gwamnati, Dr. Kingsley Emu.

Gwamnan Delta a wurin jana'iza.
Gwamnan jihar Delta tare da manyan baki a wurin jana'izar Paul Ufuoma Omu a coci Hoto: Chief Ferguson Onwo
Source: Facebook

Gwamna Ododo ya yi ta'aziyyar Sarki

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Ahmed Ododo ya yi alhinin rasuwar Sarkin Bassa Nge da ke jihar Kogi, Alhaji Abu Ali, wanda ya rasu yana shekaru 82.

Ya bayyana cewa ya samu labarin rasuwar Mai Martaba Etsu Bassa Nge da matukar bakin ciki, yana mai cewa Najeriya ta yi babban rashi.

Gwamna Ododo ya tuno da hidima, ladabi, da jajircewa wajen kula jin dadin jama’arsa da Alhaji Abu Ali ya yi a tsawon rayuwarsa, inda ya ce marigayin uba ne ga kowa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262