Tsohon Shugaban INEC Ya Samu Mukami da Tinubu Ya Nada Sababbin Jakadun Najeriya 32

Tsohon Shugaban INEC Ya Samu Mukami da Tinubu Ya Nada Sababbin Jakadun Najeriya 32

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya turo sunayen sababbin jakadu 32 ga Majalisar dattawan Najeriya domin tantancewa
  • Daga cikin wadanda aka ga sunansu akwai tsofaffin gwamnoni, tsohon shugaban INEC, matan tsofaffin gwamnoni da manyan jami’an gwamnati
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan Shugaba Tinubu ya tura sunayen mutum uku da yake son turawa kasashen waje a matsayin jakadu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Makonni bayan ya sauka daga shugabancin hukumar INEC ta kasa, Farfesa Mahmud Yakubu ya samu mukami a gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Hakan na zuwa ne bayan Shugaba Bola Tinubu ya nada sababbin jakadu 32, wadanda za su wakilci Najeriya a kasashe daban-daban a duniya.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Mai girma shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnati da ke Abuja Hoto: @DOlusegun
Source: Twitter

Fadar shugaban kasa ta bayyana sunayen wadanda aka nada a wata sanarwa da ta wallafa a shafin yanar gizo mai dauke da sa hannun kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga.

Kara karanta wannan

Trump: Tinubu ya zakulo 'yan Najeriya da za su yi aiki da Amurka kan tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya tura sunayen jakadu 32 majalisa

Tinubu ya aika wa Majalisar Dattawa sunayen sabbin jakadu 32 domin tantancewa da tabbatarwa, kwanaki kadan bayan ya aika jerin farko na mutane uku.

A cikin wasiku biyu daban-daban da ya turo wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, Tinubu ya nemi majalisar ta gaggauta tabbatar da sababun jakadun.

Wasikar farko na kunshe da sunayen sababbin jakadu 17 da ba su da gogewar aikin jakadanci, yayin da ta biyu ke dauke da cikakkun jakadu masu gogewa 15.

Rukunin farko na jakadu 17

Wadanda Tinubu ya nada da ba su da gogewar aikin jakadanci sun hada da:

1. Barista Ogbonnaya Kalu – daga Abia

2. Reno Omokri – tsohon hadimin shugaban kasa (Delta)

3. Farfesa Mahmud Yakubu – tsohon Shugaban INEC

4. Erelu Angela Adebayo – tsohuwar uwargidan gwamnan Ekiti

5. Ifeanyi Ugwuanyi – tsohon Gwamnan Enugu

6. Tasiu Musa Maigari – tsohon Kakakin Majalisar Katsina

Kara karanta wannan

Tinubu ya nada shugaban NIA da ya shiga badakalar $43m lokacin Buhari a matsayin Jakada

7. Yakubu N. Gambo – tsohon kwamishina a Filato

8. Farfesa Nora Ladi Daduut – tsohuwar Sanata (Filato)

9. Otunba Femi Pedro – tsohon mataimakin gwamnan Legas

10. Cif Femi Fani-Kayode – tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama

11. Bariata Nkechi Linda Ufochukwu – daga Anambra

12. Fatima Florence Ajimobi – tsohuwar Uwargidan Gwamnan Oyo

13. Lola Akande – tsohuwar Kwamishina a Legas

14. Grace Bent – tsohuwar Sanata daga Adamawa

15. Victor Okezie Ikpeazu – tsohon Gwamnan Abia

16. Sanata Jimoh Ibrahim – dan kasuwa kuma lauya daga Ondo

17. Paul Oga Adikwu – daga Benuwai.

Rukuni na 2 na sababbin jakadu 15

Sauran cikakken jakadu 15 da Tinubu ya nada a wasika ta biyu sune:

1. Enebechi Monica Okwuchukwu (Abia)

2. Yakubu Nyaku Danladi (Taraba)

3. Miamuna Ibrahim Besto (Adamawa)

4. Musa Musa Abubakar (Kebbi)

5. Syndoph Paebi Endoni (Bayelsa)

6. Chima Geoffrey Lioma David (Ebonyi)

7. Mopelola Adeola-Ibrahim (Ogun)

8. Abimbola Samuel Reuben (Ondo)

9. Yvonne Ehinosen Odumah (Edo)

Kara karanta wannan

Abin da muka sani game da Oke, Are da Dalhatu, sababbin jakadu da Tinubu ya nada

10. Hamza Mohammed Salau (Niger)

11. Amb. Shehu Barde (Katsina)

12. Amb. Ahmed Mohammed Monguno (Borno)

13. Amb. Muhammad Saidu Dahiru (Kaduna)

14. mb. Olatunji Ahmed Sulu Gambari (Kwara)

15. Amb. Wahab Adekola Akande (Osun).

Shugaban Majalisar Dattawa.
Shugaban Majalisar Dattawa ta 10 a Najeriya, Sanata Godswill Akpabio Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

Jakadu 3 da Tinubu ya fara nadawa

A baya, kun ji cewa Bola Tinubu ya fara nada mutum uku a matsayin jakadu da ya tura sunayensu zuwa Majalisar Dattawan Najeriya

Sunayen da shugaban kasa ya aika sun haɗa da Kayode Are daga Jihar Ogun, Aminu Dalhatu daga Jihar Jigawada kuma Ayodele Oke daga jihar Oyo.

Nadin na zuwa ne bayan ofisoshin jakadancin Najeriya da ke kasashen waje sun kasance babu jakadu har na tsawon fiye da shekara biyu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262