Fitaccen Jarumin Fim a Najeriya Ya Bayyana Ana tsaka da Jita Jitar Ya Mutu

Fitaccen Jarumin Fim a Najeriya Ya Bayyana Ana tsaka da Jita Jitar Ya Mutu

  • Kungiyar masu gabatar da shirin fim a Najeriya, ANTP ta yi karin haske da ake yada cewa daya daga cikin mambobinta ya bar duniya
  • ANTP ta karyata jita-jitar cewa fitaccen jarumin Nollywood, Lere Paimo (Eda Onile Ola) ya rasu, inda ta tabbatar cewa yana nan raye
  • Kungiyar ta ce ta tabbatar da lafiyar jarumin ne ta bakin matarsa, tana kira ga jama’a su guji yada ƙarya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Kungiyar masu shirya fina-finai (ANTP) ta bayyana gaskiya game da jita-jitar cewa jaruminta ya riga mu gidan gaskiya.

Kungiyar ta karyata jita-jitar da ake yadawa cewa fitaccen jarumin Nollywood, Lere Paimo, wanda aka fi sani da Eda Onile Ola, ya rasu.

An karyata mutuwar jarumin fim a Najeriya
Daya daga cikin fitattun jarumai, Lere Paimo. Hoto: @lerepaimo.
Source: Instagram

An karyata mutuwar jarumin Nollywood

A wata sanarwa da mai magana da yawunta na ƙasa, Prince Adejonwo Oluwafemi ya fitar wanda Tribune ta samu ya ce labarin mutuwar jarumin karya ne.

Kara karanta wannan

Ngige: Ministan Buhari ya fadawa Obi yadda 'yan ta'adda suka bude masa wuta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Femson ya ce rahotanni a kafafen yada labarai da aka wallafa ba gaskiya ba ne, domin har yanzu yana raye kuma cikin koshin lafiya.

Har ila yau, kungiyar ta ce ta tattauna da iyalan marigayin musamman matarsa wacce ta tabbatar da cewa dattijon na cikin koshin lafiya.

Kungiyar ta ce:

“Muna son sanar da jama’a cewa bayanan da ake yadawa a Facebook game da rasuwar Cif Olalere Osun Paimo (MFR) karya ce.
"Mun tabbatar da hakan daga matarsa cewa yana raye cikin ƙoshin lafiya babu wata damuwa tattare da shi.”
Iyalan jarumin fim sun musanta labarin mutuwarsa
Dattijon jarumin fim, Lere Paimo da aka yada ya yaru. Hoto: @lerepaimo.
Source: Instagram

An bukaci al'umma sun hankalta kan yada karya

ANTP ta kuma ja hankalin jama’a da su yi watsi da waɗannan labaran ƙarya, tana mai cewa wasu bata-gari ne kawai ke yada irin wadannan bayanan domin rikita jama’a.

Kungiyar ta kara da cewa Cif Olalere Osun Paimo (MFR), wanda shi ne shugaban kwamitin amintattu na kungiyar, yana raye.

Kara karanta wannan

Ngige: An ji halin da ministan Buhari ke ciki bayan 'yan bindiga sun bude wa motarsa wuta

Ta kuma roƙi jama’a su tabbatar da sahihancin kowanne bayani kafin yadawa domin guje wa shiga rikici, cewar rahoton The Nation.

“Don Allah ku yi watsi da wadannan rahotannin karya, ku sani cewa wasu bata-gari ne suke yada su. Babban ɗan wasan Nollywood, Cif Olalere Osun Paimo (MFR), Shugaban Kwamitin Amintattu na ANTP, yana da rai kuma yana cikin koshin lafiya.
"Muna roƙon kowa da ya tabbatar da sahihancin kowace bayani kafin yada shi domin kauce wa yada ƙarya, mun gode."

- Cewar sanarwar

Jarumin Nollywood mai shekaru 86 wanda ya sha karramawa, ya fara harkar fim tun 1958, kuma ya fito a manyan fina-finai da dama irin su Saworoide, Oleku, Ogbori Elemonso da sauran fitattun kayatattun fina-finai na masana'antar Nollywood.

Jarumi ya musanta labarin mutuwarsa

Kun ji cewa a kwanakin baya, an yi ta yada jita-jitar cewa fitaccen jarumin Nollywood, Chiwetalu Agu ya mutu bayan fama da rashin lafiya.

Jarumi Agu ya saki faifan bidiyo a shafinsa na kafar sada zumunta, inda ya karyata labarin cewa ya rasu wanda ya tayarwa iyalansa hankali.

Kara karanta wannan

Malami: EFFC ta gayyaci ministan Buhari kwanaki bayan cewa zai yi takara a 2027

Ya bukaci yan uwa da masoyansa su yi watsi da wannan mummunan labari, yana mai cewa yana nan a raye kuma ba yanzu zai mutu ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.