Kano Ta Dauki Zafi, Ganduje Ya Yi Magana bayan Gwamnatin Abba Ta Nemi a Kama Shi
- Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya soki Gwamna Abba Kabir Yusuf bayan gwamnatinsa ta nemi jami'an tsaro su kama shi
- Gwamnatin Kano ta nemi a kama Ganduje ne kan wasu kalamai da take zargin za su iya tayar da tarzoma da dagula harkar tsaro
- Tsohon gwamnan ya bukaci Gwamnatin Abba ta maida hankali kan hakkin mutane da kansa, domin ya ce alamu sun nuna ya gaza
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na kasa kuma tsohon Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya yi martani kan kiran da aka yi ga jami'an tsaro su kama shi.
A jiya Jumu'a ne gwamnatin Kano ta nemi a kama Ganduje bisa wasu kalamai da ya yi, wadanda take ganin barazana ce ga kokarin tabbatar da tsaro a jihar.

Kara karanta wannan
Shugaban hukuma a Kano ya caccaki Ganduje, ya goyi bayan Abba a kama tsohon gwamna

Source: Facebook
Daily Trust ta ce a wata sanarwa da Edwin Olofu, Mai magana da yawun Ganduje ya fitar, tsohon gwamnan ya bayyana kiran kama shi a matsayin rashin kwarewa da neman mafaka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Martanin Ganduje ga gwamnatin Kano
Ya yi fatali da kiran da Gwamnatin Kano ta yi na cewa a kama shi bisa zargin kalaman da ka iya dagula tsaro, yana mai cewa wannan batu marar tushe ne, kuma alamar rashin kwarewa ce.
Ganduje ya yi zargin cewa gwamnatin Kano ta yi wannan kiran ne domin ta kauda hankalin jama’a daga gazawarta, yana mai cewa:
“Maimakon ya magance karuwar rashin tsaro a jihar, Gwamna Abba yana bin inuwa yana laluben wanda zai jingina wa gazawarsa.”
Ya ce mutanen da ke fama da hare-hare a kananan hukumomi irin su, Bagwai, Shanono, da Tsanyawa, ba su taɓa ganin gwamnan ya ziyarce su ko ya nuna tausayawa ba.
Ganduje ya nesanta kansa da matsalar tsaro

Kara karanta wannan
Martanin Barau da gwamnatin Kano ta nemi a cafke shi saboda zargin ingiza rashin tsaro
Sanarwar ta kara jaddada cewa Ganduje ba ya da alaka da kungiyoyin tada kayar baya kuma bai taɓa aikata wani abu da zai lalata zaman lafiya a Kano ba.
Ta kuma ce a mulkinsa na shekaru takwas, jihar Kano ta kasance mafi kwanciyar hankali, kuma ta samu yabo a matakin ƙasa saboda tsare rayuka da dukiyoyin al'umma.
Ganduje ya bayyana hakan a matsayin banbancin da ke tsakanin shi da gwamnatin yau wadda ya zarga da rashin tsari da rashin iya jagoranci, cewar Leadership.

Source: Facebook
Shawarar da Ganduje ya ba Abba Gida-Gida
Tsohon gwamnan ya yi kira ga Gwamna Abba da ya maida hankali kan aikin da kundin tsarin mulki ya dora masa, ya daina “wasan siyasa” da yin zarge-zarge marasa tushe.
Ganduje ya ce:
"Jagoranci aiki ne na hangen nesa, nauyi da tausayi, ba na taron manema labarai ko fitar da bayanan da ba su da amfani ba.”
Sanata Barau ya soki gwamnatin Kano
A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya zargi Gwamna Abba Kabir Yusuf da yunkurin siyasantar da batun tsaro a Kano.
Ya ce a halin da ake ciki, kamata ya yi gwamnati ta mayar da hankali a kan warware matsalolin da ke addabar Kano, musamman dangane da abubuwan da suka shafi tsaro.
Sanata Barau ya yi mamakin zargin da gwamnatin jiha ta yi cewa maganganunsa na iya kawo cikas ga kokarin da ake yi na inganta tsaro.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
