Matakin Tinubu Ya Rikita Ƴan Siyasa, Sun Bazama Neman Masu Gadinsu Ta Kowane Hali

Matakin Tinubu Ya Rikita Ƴan Siyasa, Sun Bazama Neman Masu Gadinsu Ta Kowane Hali

  • Bayan umarnin shugaban kasa na janye jami’an ’yan sanda daga manyan mutane, an fara samun matsala game da tsaron yan siyasa
  • Fitattun mutane sun fara neman jami'an tsaro daga jami'an hukumar NSCDC, gandurobobi da kamfanoni masu zaman kansu
  • Rahotanni sun nuna cewa buƙatar ma’aikatan NSCDC ta karu ƙwarai, yayin da jihohi kamar Ondo ke ƙara ɗaukar Amotekun domin ƙarfafa tsaro

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya umarci janye jami’an ’yan sanda daga manyan mutane a Najeriya domin tsaurara tsaro.

Yan siyasa sun fara buƙatar kamfanoni tsaro masu zaman kansu da NSCDC domin tsaron lafiyarsu.

Tinubu ya umarci janye yan sanda daga tsaron yan siyasa
Shugaba Bola Tinubu yayin ganawa da Sufeta-janar na yan sanda, Kayode Egbetokun. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Rahoton Punch ya ce Tinubu ya ba da wannan umarni domin ƙarfafa tsaro a al’umma, musamman inda ake fuskantar barazanar rashin tsaro.

Kara karanta wannan

Ndume zai barowa Sanatoci aiki, ya nemi Tinubu ya janye 'yan sanda a majalisa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan sanda sun janye masu gadin manya

Sufeta-janar na yan sanda, Kayode Egbetokun ya bayyana cewa an riga an janye jami’an tsaron da suka kai 11,566 daga manyan domin mayar da su kan ayyukan tsaron jama’a.

Binciken manema labarai ya nuna cewa yan siyasa da dama sun fara neman karin jami’an NSCDC domin kiyaye gidajensu, iyalansu, da jigilar su.

NSCDC mai ma’aikata kusan 60,000 na kare rayuka, tsare kadarorin gwamnati, da taimakawa hukumomin farar hula.

A Abuja, an ce jami’an NSCDC na samun kira da saƙonni daga manyan mutane masu neman sababbin masu tsaro, duk da ƙarancin ma’aikata a halin yanzu.

Jihohi kamar Ondo sun fara ɗaukar matakan tallafawa tsaro, inda Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya amince da ɗaukar ma’aikatan Amotekun 500 domin ƙarfafa kariya.

A taron gwamnonin Kudu, an jaddada cewa babu makawa sai an kafa ’yan sandan jihohi idan ana son magance matsalar ’yan bindiga yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Abu ya gagara: Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta baci kan matsalar tsaron Najeriya

An fara cika umarnin Tinubu na janye yan sanda da ke gadin manya
Sufeta-janar na yan sanda, Kayode Egbetokun. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Facebook

Yadda yan siyasa ke neman jami'an kariya

Wasu kamfanonin tsaro masu zaman kansu ma sun ce sun kasa biyan bukatar manya saboda ƙarancin ma’aikata da ƙaruwar buƙatar tsaro a lokaci guda.

Wasu ’yan siyasa sun killace kansu a gidajensu har sai sun samu sababbin tsare-tsare, suna ganin matakin ya dace da halin tsaro na yanzu, cewar The Nation.

Sanata Ali Ndume ya yaba da umarnin, yana mai cewa ya kamata a rage yawan ’yan sandan da ke aiki da ’yan majalisa domin mayar da su ga jama’a.

Ya ce abin kunya ne yadda manya ke amfani da jami’an tsaro da yawa, har ma a kan matansu da ’ya’yansu, yayin da talakawa ke rasa kariya.

Janye 'yan sanda: An fara cika umarnin Tinubu

Mun ba ku labarin cewa Rundunar 'yan sandan Najeriya ta fara cika umarnin da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayar a kan jami'anta.

Shugaba Tinubu ya yi umarnin a janye dukkanin jami'an 'yan sanda da ke tsaron manyan mutane a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan

Yadda 'Yan sanda suka saba alkawarin janye jami'ai daga gadin manya amma ba a cikawa

Bola Tinubu ya bayar da umarnin bayan an samu karuwar hare-hare, musamman a makarantun da ke karkara a kasar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.