Bayan Birne Shi a Masallaci, Sheikh Abdullahi Pakistan Ya Yi Magana kan Dahiru Bauchi

Bayan Birne Shi a Masallaci, Sheikh Abdullahi Pakistan Ya Yi Magana kan Dahiru Bauchi

  • Shugaban hukumar NAHCON, Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan ya bayyana jimaminsa kan rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
  • Ya ce marigayin jagora ne da ya taimaka wajen gyaran tsarin Hajji a Najeriya, kuma ya na taimaka wa alhazai da ilimin addini
  • Pakistan ya ce shawarwarin shehin sun taimaka wajen kula da alhazai cikin natsuwa, ya mika ta'aziyya ga iyalai da mabiyansa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON), Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan, ya yi alhinin rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci kuma jagoran Darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Sheikh Pakistan, wanda shi ne shugaban kungiyar Izala na jihar Kano ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin, tare da bayyana gudummuwar da ya bada ga alhazan Najeriya.

Sheikh Abdullahi Pakistan.
Shugaban hukumar alhazai ta kasa (NAHCON), Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan Hoto: Prof. Abdullahi Saleh Pakistan
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mataimakinsa na Musamman kan Harkokin Yada Labarai, Ahmad Muazu, ya fitar a ranar Asabar, kamar yadda Punch ta kawo.

Kara karanta wannan

Allahu Akhbar: An yi jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi, an birne gawarsa a masallaci

Shugaban NAHCON ya mika ta’aziyyarsa ga iyalin marigayi Dahiru Bauchi, almajirai, mabiyansa, da gaba ɗayan al’ummar Musulmi.

Farfesa Abdullahi Pakistan ya ce rasuwar malamin ta zama babban rashi ga Musulmai a Najeriya da ma wajen ta.

Taimakon da Dahiru Bauchi ya yi wa NAHCON

Pakistan ya bayyana cewa marigayin ya kasance mutum mai kaunar walwalar alhazai kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen gyara tsarin Hajji da gyare-gyaren da aka samu cikin shekaru.

Shugaban NAHCON ya kara da cewa shawarwarin Dahiru Bauchi sun taimaka matuƙa wajen tabbatar da alhazai sun yi abin da addini ya umarta yayin aikin hajji.

“Duk lokacin da hukumar NAHCON ta bukaci karin haske ko mafita a kan al’amuran addini masu sarkakiya, kofar Sheikh Dahiru Bauchi a bude take,” inji shi.

Shugaban NAHCON ya tuna alheran marigayi

Abdullahi Saleh Pakistan ya kara da cewa hikimar marigayin ta samar da ingantattun mafita da ake amfani da su wajen kula da alhazai a yau.

Kara karanta wannan

Malamai da manyan ƴan siyasa da suka yi ta'aziyyar Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi

Shugaban NAHCON ya kara bayyana marigayin da cewa:

“Babban malami ne kuma jagora. Ya tsaya tsayin daka wajen ilmantarwa da kyawawan halaye. Yana tunasar da mu cewa dole a kula da kowane ɗan Najeriya cikin martaba yayin gudanar da aikin Hajji.”

Addu’o’i ga malamin da iyalansa

Sheikh Pakistan ya yi addu’ar Allah ya ji kan sa, Ya azurta shi da Aljannatul Firdaus, Ya kuma ba iyalansa, mabiyansa da al’umma haƙuri da juriya a wannan babban rashi.

Ya kuma bayyana cewa rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi ta bar gibin da zai wahala a iya cikewa, cewar The Nation.

Pakistan da Dahiru Bauchi.
Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan da Sheikh Dahiru Usman Bauchi Hoto: Prof. Abdullahi Saleh Pakistan
Source: Facebook

Yadda aka yi jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi

A baya, mun kawo muku yadda aka yi jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi tare da birne shi a wani bangare a masallacinsa kamar yadda ya yi wasiyya.

Sheikh Shariff Saleh Al-Hussaini ne ya jagoranci yi wa marigayin Sallah, inda dubun dubatar musulmi daga ciki da wajen Najeriya suka halarta.

Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, da gwamnonin Kano, Bauchi da Neja na cikin manyan da suka halarci jana'izar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262