Malami: Yadda Ta Kaya tsakanin Ministan Buhari da EFCC bayan Ya Amsa Gayyata

Malami: Yadda Ta Kaya tsakanin Ministan Buhari da EFCC bayan Ya Amsa Gayyata

  • Tsohon ministan shari'a a gwamnatin Muhmmadu Buhari, Abubakar Malami ya samu gayyata daga wajen hukumar EFCC
  • Abubakar Malami ya amsa gayyatar da EFCC ta yi masa kamar yadda ya yi alkawarin zuwa gaban hukuma tun da farko
  • Tsohon ministan ya ce sun tattauna da jami'an EFCC kuma zai sake komawa nan gaba domin dorawa daga inda aka tsaya

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon ministan shari'a a gwamnatin Muhammadu Buhari, Abubakar Malami, ya amsa gayyatar da hukumar EFCC ta yi masa.

Abubakar Malami ya bayyana cewa an sake shi bayan ya amsa gayyatar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta yi masa.

Abubakar Malami ya amsa gayyatar EFCC
Tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami Hoto: Abubakar Malami SAN
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da tsohon ministan ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ta kaya tsakanin Malami da EFCC?

Kara karanta wannan

Ngige: An ji halin da ministan Buhari ke ciki bayan 'yan bindiga sun bude wa motarsa wuta

Malami ya bayyana cewa ganawarsa da hukumar yaƙi da cin hancin ta kasance cikin nasara, inda ya kara da cewa an sa masa wani sabon lokaci domin ci gaba da tattaunawa da masu bincike.

Malami ya kara da cewa gaskiya game da “kirkirarrun zarge-zargen” da ake yi masa za ta ci gaba da bayyana.

“A bisa alkawarin da na yi wa ‘yan Najeriya na ci gaba da sanar da su game da gayyatar EFCC, ina gode wa Allah bisa taimakonsa."
"Tattaunawar ta tafi yadda ya kamata, kuma daga karshe an sake ni tare da sanya mini wani lokaci na ci gaba da tattaunawa yayin da gaskiya game da zarge-zargen da aka kirkira a kaina ke ci gaba da bayyana.”

- Abubakar Malami

Malami ya samu gayyata daga EFCC

Wannan bayanin ya biyo bayan wata sanarwa da ya gabatar a baya inda ya tabbatar da cewa ya samu gayyatar EFCC.

A wancan lokacin, ya ce zai amsa gayyatar ne a matsayin ɗan kasa mai bin doka da oda da tabbatar da gaskiya.

Bayan samun gayyatar, babban lauyan wanda ya yi ministan shari'a a karkashin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari daga 2015 zuwa 2023, ya tabbatar wa jama’a cewa yana da cikakkiyar niyyar bada hadin kai ga hukumar.

Kara karanta wannan

Malami: EFFC ta gayyaci ministan Buhari kwanaki bayan cewa zai yi takara a 2027

Malami ya gana da hukumar EFCC
Abubakar Malami na jawabi a wajen taro Hoto: Abubakar Malami SAN
Source: Facebook

Ya ce bada haɗin kai ga EFCC ya yi daidai da ka’idodin da ya rika karewa a lokacin da yake rike da mukamin gwamnati.

“Ina sanar da iyalina da abokaina cewa EFCC ta gayyace ni domin in bayyana wasu abubuwa. A matsayina na ɗan ƙasa mai bin doka da kuma masoyin ƙasa, zan amsa wannan kira ba tare da wata jinkiri ba."
"Na yi amanna da muhimmancin gaskiya, rikon amana da ɗaukar alhakin abin da mutum ke yi a shugabanci. Waɗannan su ne ƙa’idojin da na daɗe ina tsayawa a kai a tsawon shekarun da na shafe a aikin gwamnati.”

- Abubakar Malami

Timpre Sylva zai kai kansa ga EFCC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Timpre Sylva ya shirya kai kansa ga hukumar EFCC.

Timpre Sylva ya aika da wasika ga EFCC yana rokon a saka masa ranar da zai bayyana gaban hukumar domin amsa tambayoyi game da zarge-zargen da aka yi masa.

Kara karanta wannan

"Mun san su": Sanata Maidoki ya ba gwamnati zabi 2 kan kawo karshen 'yan bindiga

Tsohon gwamnan ya rubuta wasikar ne bayan da hukumar EFCC ta ayyana shi wanda ake nema bisa zargin almundahanar $14.8m.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng