Ana Wata ga Wata: DSS Ta Gayyaci Datti Baba Ahmed, An Ji Dalilin Neman Shi
- Kalaman tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa a 2023, Datti Baba-Ahmed na neman sanya shi a cikin matsala
- Hukumar tsaro ta gayyaci Datti Baba-Ahmed domin ya yi mata bayani kan kalaman da ya rika yi a cikin 'yan kwanakin nan
- Majiyoyi sun bayyyana cewa babu batun siyasa a cikin gayyatar da hukumar DSS ta yi wa abokin takarar na Peter Obi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gayyaci tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben 2023, Yusuf Datti Baba-Ahmed.
Hukumar DSS ta gayyaci Datti Baba-Ahmed ne kan wasu kalamai da ya yi a cikin 'yan kwanakin nan.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa hukumar DSS ta gayyaci Datti Baba-Ahmed, wanda shi ne ya kafa jami’ar Baze, a daren ranar Juma’a, 28 ga watan Nuwamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa DSS ta gayyaci Datti Baba-Ahmed?
Hukumar DSS ta gayyace shi ne bisa zargin cewa yana ci gaba da bayyana ra’ayoyi da ake kallon suna tunzura jama'a kan gwamnatin Najeriya.
Wata majiyar tsaro ta ce DSS na bibiyar bayanan Datti Baba-Ahmed a kafafen yaɗa labarai a ’yan kwanakin nan, musamman maganganunsa game da abin da yake kira 'rikicin kundin tsarin mulki'.
“’Yan kwanaki da suka wuce, Datti Baba-Ahmed ya bayyana a gidan talabijin, inda ya zargi kotuna da rundunar sojoji da cewa sun bari an rantsar da Shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima.”
“Har ma ya yi maganar da za a iya ɗauka a matsayin tunzura rundunar sojoji, yana cewa rantsar da Tinubu ne ya ba su damar kallon fuskar mutane su kira su ‘sakarkarun banza’".
- Wata majiya
DSS ta damu kan kalaman Datti Baba-Ahmed
A cewar majiyar, hukumar DSS, ta bayyana cewa irin waɗannan maganganu na iya ƙara tada hankula, musamman a wannan lokaci da siyasar Najeriya ke da ɗimbin rashin tabbas.
Ta kara da cewa hukumar tsaro tana kallon lamarin da taka-tsantsan, kamar yadda rahoton jaridar The Punch ya nuna
Majiyar ta ce:
“Abu ne mai tayar da hankali ganin irin waɗannan maganganu suna kama da yadda matsalar kasashe kamar Guinea-Bissau da wasu ƙasashen yammacin Afrika ta samo asali.”
“Ba abin siyasa ba ne. Maganganun da ka iya yin barazana ga zaman lafiya da haɗin kan ƙasa ba za a yi watsi da su ba.”

Source: Facebook
Hakazalika, hukumar ta yi nuni da cewa kiran Baba-Ahmed na cewa ƙoƙarin gwamnati na inganta tsaro “tatsuniya ne kawai” na iya tayar da hankali da rage amincewar jama’a ga hukumomin gwamnati.

Kara karanta wannan
Guinea Bissau: Gwamnatin Tinubu ta faɗi halin da Jonathan ke ciki bayan ya maƙale
DSS dai ba ta fitar da sanarwa a hukumance ba har zuwa lokacin da aka kammala hada wannan rahoto.
DSS ta gurfanar da matashi a kotu
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta maka wani matashi daga jihar Rivers kara a gaban kotu.
Hukumar DSS ta gurfanar da shi ne bisa zargin yin kira ga juyin mulki da kuma ɓata suna ga gwamnati a kafar sada zumunta.
DSS ta ce matashin mai suna Chukwuemeka Onukwume ya wallafa sakonni a shafinsa na X da ke kira ga kifar da gwamnati a Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

