Obasanjo Ya Fadi Matsayarsa kan Tattaunawa da 'Yan Bindiga, Ya Ba Gwamnati Shawara

Obasanjo Ya Fadi Matsayarsa kan Tattaunawa da 'Yan Bindiga, Ya Ba Gwamnati Shawara

  • Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya nuna damuwa kan yadda rayukan 'yan Najeriya ke salwanta saboda matsalar rashin tsaro
  • Obasanjo ya kuma nuna cewa ba laifi ba ne don 'yan Najeriya sun nemi taimako daga waje kan rashin tsaro saboda gwamnati ta gaza
  • Tsohon shugaban kasar ya bukaci gwamnati ta yi amfani da kayan aiki na zamani domin murkushe tsagerun da ke kashe mutane

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya yi watsi da kiraye-kirayen da ake yi na tattaunawa da ’yan bindiga.

Obasanjo ya jaddada cewa dole Najeriya ta ɗauki mataki mai karfi tare da karɓar taimakon ƙasashen waje domin fuskantar matsalar rashin tsaro.

Obasanjo ya koka kan rashin tsaro
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo Hoto: Olusegun Obasanjo
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce Obasanjo ya bayyana hakan ne a wajen taro kan bikin Kirismeti da aka gudanar a Jos ranar Juma’a, 27 ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: ADC ta jefa zafafan tambayoyi ga gwamnatin Tinubu

Me ya ce kan sulhu da 'yan bindiga?

Obasanjo ya bukaci gwamnatin tarayya ta daina neman uzuri da kuma tattaunawa da ’yan ta’adda.

Wannan matsayar tasa na zuwa ne a tsakiyar yawaitar kashe-kashe, garkuwa da mutane, da hare-hare da dama da ke faruwa a sassan Arewacin Najeriya cikin kwanakin nan.

Yayin jawabin nasa a Jos, Obasanjo ya nuna takaici kan yadda tsaro ke tabarbarewa, yana mai cewa ’yan Najeriya suna da hakkin neman taimakon kasashen duniya idan gwamnati ta kasa kare su.

“Ko da a wane addini ka fito. Ko daga ina ka fito. Ko mece ce sana’arka, mu ’yan Najeriya ana kashe mu, gwamnati kuma kamar ta kasa kare mu."
“Mun kasance cikin al’ummar duniya. Idan gwamnati ba za ta iya ba, muna da hakkin kiran ƙasashen duniya su yi mana abin da gwamnati ta kasa yi mana.”

- Olusegun Obasanjo

Obasanjo ya bada shawara

Ya kara da cewa kafin ya bar mulki, ya san ana da karfi da kayan aiki da za su iya kamo duk wani mai laifi a ko’ina cikin ƙasar, rahoton ya zo a jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Abin da muka sani game da Oke, Are da Dalhatu, sababbin jakadu da Tinubu ya nada

Obasanjo ya bukaci gwamnati ta daina sulhu da 'yan bindiga
Olusegun Obasanjo yana jawabi a wajen wani taro Hoto: Olusegun Obasanjo
Source: Facebook
“Kafin na bar gwamnati mun riga mun samu damar gano duk wanda ya aikata laifi a Najeriya ko da a ina yake. Abin da ba mu da shi a lokacin shi ne, bayan gano shi, bazamu iya cafke shi ba sai mun yi tafiya ta kasa ko ta sama."
“Yanzu muna da wannan damar. Tare da amfani da jirage marasa matuka za ka iya bin sawunsu, ka gano su, ka kuma kawar da su. Me ya sa ba mu yin haka? Me ya sa muke neman afuwa? Me ya sa muke tattaunawa?”

- Olusegun Obasanjo

Fayose ya caccaki Obasanjo

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya ragargaji Olusegun Obasanjo.

Ayodele Fayose ya bayyana cewa maganganun Obasanjo a bikin zagayowar haihuwarsa na 65 sun fusata shi matuƙa, har ya ji kamar ya jefe shi.

Tsohon gwamnan na jihar Ekiti ya ce lamarin ya fusata shi har ya ji kamar ya kwace makirufo daga hannunsa ya buge shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng