Rahoto Ya Ce an Kashe Musulmai 4,700 a jihar Filato a Tsawon Shekaru
- An gudanar da addu’a a Jos don tunawa da Musulmi sama da 4,700 da suka rasa rayukansu a jerin tashe-tashen hankula
- An yi zaman addu’ar ne a babban masallacin Jos inda aka fara da karatun Alƙur’ani domin roƙon rahama ga waɗanda suka mutu
- Shugabanni sun bayyana yadda rikice-rikice daban-daban suka lakume dubban maza da mata, samari da tsofaffi a sassan jihar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jos, Filato – Al’ummar Musulmi a birnin Jos sun gudanar da addu’a karo na 17 domin tuna dubban rayukan da aka rasa a tashe-tashen hankulan da suka addabi jihar fiye da shekaru 20.
An gudanar da zaman addu’ar a ranar Juma’a, 28, Nuwamba, 2025 a babban masallacin Jos, inda aka fara taron da karatun Alƙur’ani domin roƙon rahamar Allah ga waɗanda suka mutu.

Source: Original
Daily Trust ta rahoto cewa al’ummar sun ce tun bayan rikicin kananan hukumomi na 2008 da sauran hare-hare da suka biyo baya, rayuka fiye da 4,700 ne suka salwanta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka kashe Musulmai a Filato
Shugaban ƙungiyar Jasawa Community Development Association (JCDA), Yawale Muhammad, ya bayyana cewa rikicin Filato abu ne da ya jawo kashe al’ummar Musulmi .
Domin a cewarsa, rikice-rikicen 2001, 2002, 2004, 2008, 2010 da wasu da suka gabata sun yi mummunan barna ga al'ummar Musulmi.
A cewarsa, a 2001 Musulmi fiye da 700 ne suka mutu, yayin da a 2002 aka kai hare-hare ga ɗaruruwa a yankin Eto Baba.

Source: Facebook
Ya ce rikicin Yelwa-Shendam na 2004 ya ƙara yawan adadin mutanen da aka kashe da akalla mutum 700.
Daily Nigerian ta rahoto ya kara da cewa a 2008 rikicin bayan zaben kananan hukumomi ya jawo hallaka Musulmi sama da 1,000.
Yawale ya kara da cewa rikice-rikicen wurare daban-daban a 2010 – ciki har da Dutse Uku, Gero da Kuru Jenta – sun lakume rayukan Musulmi fiye da 2,000.
Manyan hare-hare da aka kai bayan 2010
A taron addu'ar, an kuma tunatar da rikicin filin sallar Idi na Rukuba na 2011 wanda ya yi sanadin mutuwar masu ibada 20.
Haka zalika, a 2021, harin da aka kai wa Musulmi masu dawowa daga gaisuwa ga Sheikh Dahiru Bauchi ya yi sanadin mutuwar wasu matafiya a Rukuba.
Yawale Muhammad ya ce:
Daga alkaluman da muka tattara, an kashe mana mutum 4,700.”
Ya bayyana cewa sun yi rajistar waɗannan mutane bisa faruwar hare-haren da ba su gushewa ba tsawon shekaru.
Jagoran addu’ar, Malam Hamisu Umaru, ya bayyana cewa zaman addu’ar na da matuƙar amfani domin neman gafarar Allah ga waɗanda suka mutu tare da roƙon zaman lafiya ga jihar Filato.
Sojoji sun ziyarci masallaci da coci a Filato
A wani rahoton, kun ji cewa wasu dakarun sojojin Najeriya da suke aiki a jihar Filato sun ziyarci wuraren ibada.
Bayanan da Legit Hausa ta wallafa sun nuna cewa dakarun sun gudanar da ziyarar ne a karamar hukumar Barikin Ladi.
Yayin ziyarar, shugaban tawagar ya bayyana wa malaman addinin Kirista da Musulunci cewa ana bukatar hadin kansu wajen magance rashin tsaro.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


