‘Tausayinsa na Ke Ji’: Malami Ya Yi Magana bayan Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
- Malamin Musulunci da aka dakatar a Jihar Niger ya magantu kan rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi ya ce dukkan malamai daya suke wajen kuskure
- A bidiyon da aka ya wallafa, malamin ya jaddada cewa ba murna suke yi ba, sai dai tausayi da rokon Allah ya tsare su daga akidar dagutu
- Ya ce duk dukiyar Sheikh Dahiru Bauchi ba ta hana shi shiga kabari shi kaɗai ba, yana kira ga jama’a su ji tsoron Allah su guji bin dagutu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Minna, Niger - Matashin malamin Musulunci da aka dakatar a jihar Niger ya yi magana bayan rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi.
Malam Musammad Sani Muhammad ya ce ko kadan ba murnar mutuwa ya ke yi ba amma tausayinsa yake ji saboda yana goyon bayan dimukradiyya.

Source: Facebook
Matashin malamin ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo da Hon Nuhu Sada ya wallafa a shafin X a yau Juma'a 28 ga watan Nuwambar 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malami ya fadi yadda yake ganin Dahiru Bauchi
A bidiyon, malamin ya ce da mutuwar dan izalah da darika da salaf da sauran malamai duk daya ne saboda ba su bin tafarki mai kyau.
A cewarsa:
"Ana cewa aikin banza murnar mutuwa, idan na wandannan yan dimokuraɗiyya sun mutu saboda mu da malamin darika da izalah da shi'a da kala kato duk daya kuke.
"Mu ba murna muke yi ba, tausayinsa muje yi, muna rokon Allah ya dauke mu a wannan akida ta kafurcewa dagutu.
"Kuma wallahi kowa ya duba ya gani, wannan bawan Allah da ya rasu, Sheikh Dahiru Bauchi, kai kasan idan dai duniya ce ya tara."

Source: Facebook
Malamin ya shawarci malamai su ji tsoron Allah
Matashin ya bayyana cewa abin tsoro ne yadda malamin ya bar duniya duk da yawan dukiya, mata da dalibansa da sauran masoya.
Ya kara da cewa:
"Duk yawan dukiyarsa da yayansa da matansa da dalibansa shi kadai aka birne shi, shi kadai zai zauna a kabari har tashin kiyama."
Malamin ya shawarci al'umma da su kafurce wa dagutu, su ji tsoron Allah domin samun tsira a gobe kiyama.
Ya bayyana cewa wanda ya mutu a kan tafarkin da ba na su ba ya mutu asararre saboda addini ba maganar yabo ba ne kawai zagi ba.
Ya ce duk malaman nan sun san a kan bata suke saboda suna bin dimokuraɗiyya ya kamata su tuna su bi tafarkin Allah.
An dakatar da malamin Musulunci a Niger
Mun ba ku labarin cewa Gwamnatin jihar Niger ta dakatar da dukkanin ayyukan wani malamin addinin Musulunci da ake zargin da yada akidar Boko Haram.
Shugaban hukumar kula da harkokin addinai ta jihar, Umar Faruk, ya sanar da cewa an mika rahoton malamin ga jami'an tsaro wanda ake ganin ya zama barazana.

Kara karanta wannan
'102 zai yi,' Yadda Dahiru Bauchi ya bayyana shekarun da zai shafe a duniya tun tuni
Sheikh Faruk ya ce wani kwamiti da aka kafa ya gano cewa Muhammad Sani Muhammad ba shi da ilimin addini kuma yana barazana ga tsaron jihar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

