Ngige: An Ji Halin da Ministan Buhari ke Ciki bayan 'Yan Bindiga Sun Bude Wa Motarsa Wuta
- 'Yan bindiga sanye da kayan sojoji sun bude wuta kan ayarin tsohon Ministan Kwadago, Chris Ngige a hanyar Nkpor–Nnobi
- Tsohon ministan ya ce ba yunkurin kisa ba ne, matsalar tsaro ce kawai da ke ci gaba da ta’azzara ta rutsa da motarsa a Anambra
- Bayanai sun nuna cewa dan sandan da ke gadinsa ya samu raunun harbin bindiga amma likitoci sun yi masa aiki a asibiti
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Anambra, Nigeria - Tsohon gwamnan Anambra kuma tsohon Ministan Kwadago, Sanata Chris Ngige, ya fito ya bayyana halin da yake ciki bayan 'yan bindiga sun farmaki ayarinsa.
An fara rade-radin halin da tsohon ministan ke ciki ne bayan wasu 'yan bindiga sun bude wa motarsa wuta a hanyar Nkpor–Nnobi, karamar hukumar Idemili ta Arewa a jihar Anambra.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta biya kudin fansa kafin ceto 'daliban Kebbi? Majalisa ta yi bayani

Source: Facebook
Wane Chris Ngige yake ciki?
Vanguard ta tattaro cewa Ngige, wanda ya yi wa’adi biyu a majalisar zartarwa ta gwamnatin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, ya tabbatar da cewa yana nan a raye.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon ministan ya kuma musanta jita-jitar da wasu ke yadawa cewa harin wani yunkuri ne da aka shirya domin hallaka shi.
Ya jaddada cewa mutanen yankin sun san motar ayarinsa da direban da harin ya rutsa da su, wanda ya shafe shekaru 22 yana aiki tare da shi tun lokacin da yake gwamna.
An yi yunkurin kashe tsohon Minista?
A cewar Ngige, wasu na iya alakanta harin da yunkurin kisa, amma dukkan bayanan farko sun tabbatar cewa lamarin ya faru ne sakamakon rashin tsaro da ke addabar yankin.
Rahotanni sun nuna cewa ’yan bindigan sun kai hari a wani gari da ke kusa awa guda kafin su ci karo da ayarin tsohon gwamnan.
Direban, wanda ya je gyaran mota, ya tsinci kansa a tarkon 'yan bindigar da suka kawo harin ne lokacin da ya dawo daga wurin mai gyara.
Ngige ya shaida wa manema labarai cewa:
“Ina nan a raye, ina lafiya, babu abin da ya same ni. Wannan ba yunkurin kashe ni ba ne, matsalar tsaro ce kawai.”
Yan bindiga sun harbi dogarin Ngige
Bincike ya nuna cewa tun kafin su farmaki motar Ngige, yan bindigan sun kai hari kan motar sintirin ’yan sanda a Ezi-Owelle, inda suka kona motar suka kwashi makamai.
Bayan wannan ne suka yi karo da motar Ngige, amma ana zargin burinsu shi ne samun kayan aikin jami’an tsaro, ba kai hari ga fararen hula kai tsaye ba.

Source: Facebook
A lokacin harin, dogarin tsohon ministan mai matsayin Insufetan ’Yan Sandan a Anambra, yana cikin motar kuma an harbe shi a ƙafa.
Rahoto ya nuna cewa an garzaya da shi asibiti kuma likitoci sun yi masa tiyata domin ceto rayuwarsa.
'Yan bindiga sun kashe jami'an NIS
A wani labarin, kun ji cewa 'yan bindiga da ake zargin mayakan Lakurawa ne sun farmaki jami'an hukumar NIS a jihar Kebbi.
Wasu majiyoyi sun shaida cewa ’yan bindigan sun isa wurin ba zato ba tsammani, suka tarwatsa mutane kana suka bude wuta kan jami’an da ke bakin aiki.
An tabbatar da cewa jami'an NIS uku da ke bakin aiki sun rasa rayukansu a harin wanda ya auku da tsakar dare a yankin karamar hukumar Bagudu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

