Shettima da Wasu Manyan 'Yan Najeriya Sun Halarci Jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi

Shettima da Wasu Manyan 'Yan Najeriya Sun Halarci Jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi

  • Kashim Shettima ya sauka a Bauchi domin wakiltar Shugaba Bola Tinubu a jana’izar marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi
  • Manyan jami’an gwamnati da daruruwan mabiya sun isa Bauchi domin jana’izar jagoran Tijjaniyya, da ya rasu ranar Alhamis
  • Tsofaffin shugabanni da gwamnoni sun halarci jana'izar malamin, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen ba da ilimin Musulunci

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bauchi - Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya isa Bauchi domin wakiltar Shugaba Bola Tinubu a jana’izar Sheikh Dahiru Bauchi.

Jirginsa ya sauka Bauchi da misalin karfe 1:300 na rana, inda ya samu tarba daga manyan jami’an gwamnati da suka hada da Gwamna Bala Mohammed.

Wasu fitattun 'yan Najeriya sun halarci jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi ciki har da Kashim Shettima
Gwamna Bala Mohammed da wasu jami'an gwamnatin Bauchi sun tarbi Sanata Kashim Shettima. Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Twitter

Hakanan, kamfanin dillanci labarai na kasa, NAN, ya rahoto cewa mataimakin gwamnan jihar ya kasance cikin tawagar tarbar Shettima da tawagarsa mai karfi.

Kara karanta wannan

Allahu Akhbar: An yi jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi, an birne gawarsa a masallaci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tabbatar da cewa ya zo ne domin nuna girmamawar gwamnatin tarayya ga fitaccen malamin, wanda ya rasu a safiyar ranar Alhamis a Bauchi.

Ministoci da jami’an gwamnati sun raka Shettima

Tawagar Shettima ta kunshi manyan jami’an gwamnati daga Abuja cikin su har da mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu.

Hakanan ministan labarai, Idris Mohammed, ministan lafiya Ali Pate da ministan harkokin waje Yusuf Tuggar suma sun yi wa Shettima rakiya.

Haka kuma, wasu sanatoci da tsofaffin gwamnoni sun halarci taron, inda aka ga Sanata Abdul’aziz Yari da Sanata Shehu Buba cikin tawagar.

An kuma rahoto cewa shi ma tsohon gwamnan Bauchi Ahmed Mu’azu ya shiga jihar domin jana'iza da mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan Sheikh Dahiru Bauchi.

Tsofaffin shugabanni da gwamnoni sun isa Bauchi

Kafin zuwan Shettima, wasu manyan shugabanni sun riga sun isa garin Bauchi, ciki har da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, in ji rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Yadda jikin Shehu Dahiru Bauchi ya yi tsanani, aka tafi da shi asibiti ya rasu

Hakanan Gwamnan Kano Abba Yusuf ya isa tare da Gwamnan Neja Mohammed Bago yayin da aka ga wasu tsofaffin ministoci da hafsoshin tsaro a taron.

A cewar rahotanni, tsohon babban hafsan sojin sama Sadique Abubakar ya halarta, haka nan tsohon sakataren gwamnatin tarayya Yayale Ahmed, Bala Wunti na NNPC duk sun isa wurin jana’izar malamin.

Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya rasu a ranar Alhamis, 27 ga Nuwamba, 2025.
Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya halarci taron Mauludi da aka gudanar a Bauchi. Hoto: Fityanul Islam.
Source: Facebook

Dahiru Bauchi ya rasu yana da shekaru 98

Marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya rasu ne a ranar Alhamis a asibitin koyarwa na jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

Malamin ya rasu ne yana da shekaru 98 bayan dogon lokaci yana jagorantar darikar Tijjaniyya, kamar yadda muka ruwaito.

Sheikh Dahiru Bauchi ya yi fice wajen koyar da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin Musulmi, kuma an ce ya shafe rayuwarsa wajen ilimantar da al'umma Al-Qur'ani.

Dalilin jinkirta lokacin jana'izar Dahiru Bauchi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, daya daga cikin 'ya'yan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya bayyana makasudin jinkirta jana'izar mahaifinsu.

A ranar Alhamis, 27 ga watan Nuwamba, 2025 ne Allah ya karbi rayuwar Sheikh Dahiru, amma iyalansa suka ce za a jinkirta jana'izar zuwa Juma'a.

Kara karanta wannan

Dahiru Bauchi: Gwamna Bala ya ayyana ranar hutu a jihar Bauchi

Da yake bayani, Naziru Dahiru Usman Bauchi ya bayyana cewa sun yanke shawarar jinkirta jana'izar Shehun ne saboda bai wa wadanda ke nesa damar halarta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com