Daga Karshe, An Ji Dalilin Da Ya Sa Aka Jinkirta Jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi

Daga Karshe, An Ji Dalilin Da Ya Sa Aka Jinkirta Jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi

  • A yau Juma'a aka gudanar da jana'izar Marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda Allah ya yi wa rasuwa jiya Alhamis
  • 'Daya daga cikin 'ya'yansa, Nasiru Dahiru Bauchi ya yi bayani kan abin da ya jawo jinkirin jana'izar zuwa yau Juma'a
  • Babban malamin addinin musulunci, wanda jagora ne a darikar Tijjaniyya ya rasu ne a wani asibiti a cikin garin Bauchi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi, Nigeria - A jiya Alhamis, 27 ga watan Nuwamba, 2025 ne Allah ya karbi ran babban malamin darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi a wani asibiti.

Bayan tabbatar da rasuwarsa da asubahi, iyalan Shehun Malamin sun sanar da cewa za a yi masa sutura kamar yadda addinin musulunci ya tanada yau Juma'a.

Sheikh Dahiru Bauchi.
Marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi Hoto: Nazir Dahiru Usman Bauchi
Source: Twitter

BBC Hausa ta tattauna da daya daga cikin 'ya'yan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya bayyana makasudin jinkirta jana'izar mahaifinsu zuwa yau Juma'a, 28 ga Nuwamba, 2025.

Kara karanta wannan

Allahu Akhbar: An yi jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi, an birne gawarsa a masallaci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda jagora ne na darikar Tijjaniyya ta Afirka gaba daya, ya rasu yana da shekaru 98 a kalandar miladiyya, amma a kalandar Musulunci kuma ya kai shekara 101 da ƴan watanni.

Me yasa aka jinkirta jana'izar Dahiru Bauchi?

Da yake bayani, Naziru Dahiru Usman Bauchi ya bayyana cewa sun yanke shawarar jinkirta jana'izar Shehun ne saboda bai wa wadanda ke nesa damar halarta.

Ya ce daga cikin wadanda aka duba aka jinkirta jana'izar domin su halarta akwai Sheikh Shariff Ibrahim Saleh, wanda marigayin ya yi wasiyyar cewa shi yake so ya masa sallah.

Naziru Sheikh Dahiru Bauchi ya ce:

"Dama (mahaifinmu) ya bar wasiyyar cewa amininsa, Sheikh Shariff Ibrahim Saleh, yake so ya yi masa sallah, idan kuma ba ya gari Sheikh Isma'il Khalifa ya jagoranci yi masa sallah
"Amma shi Sheikh Isma'il Khalifa ya riga ya rasu. Don haka Sheikh Shariff Saleh ne zai masa sallah."

Kara karanta wannan

Tuna baya: Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya fadi yadda ya rungumi Sufanci

Wadanda ake tunanin za su halarci jana'iza

'Dan marigayin ya kara da cewa akwai 'yan uwa na nesa, dalibai da mabiyan Sheikh Dahiru Bauchi da za su halarci jana'izarsa daga kasashen Canada, Amurka, Masar da kuma Saudiyya.

Mahalarta jana'iza.
Yadda mutane suka mamaye harabar masallacin Dahiru Usman Bauchi Hoto: Darika TV
Source: Facebook

A cewar Naziru, mutane da dama sun kira tare da tabbatar da cewa za su taso daga kasashen da ke makwaftaka da Najeriya kamar Sudan, Ghana, Benin, Chadi da Kamaru domin zuwa wurin jana'izar Sheikh Dahiru.

Ya ce wadannan da ma wasu da za su zo daga jihohin Najeriya ya sa aka jinkirta jana'izar zuwa yau Juma'a.

Yadda Dahiru Bauchi ya fadi lolacin mutuwarsa

A baya, mun kawo muku cewa fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya taba bayyana adadin shekarun da zai kwashe a raye.

A wata hira da ya yi da manema labarai a yayin da ake shirye-shiryen birne mamacin, Malam Al-Azahari ya ce Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya shaida masa cewa ba zai wuce shekaru 102 a duniya ba.

Kara karanta wannan

Malamai da manyan ƴan siyasa da suka yi ta'aziyyar Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi

Ya ce daga baya ya fahimci ba shi kadai ya san da maganar ba, kuma malamin ya rasu a wadannan shekaru da ya bayyana masu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262